Dakta Bukar Usman [anbaiwa  

Daga

Salisu Yakasai

Ko ka]an, shekarun da ya yi a matsayim ma’aikacin gwamnati ba su wadatar da himma da }wazon Dakta Bukar Usman ba cikin ayyukan adabi. Domin a wurin wannan tsohon babban sakatare mai ritaya, rubuce-rubuce ne yake bukata domin ilimantarwa da fa]akarwa da kuma nisha]antarwa. Saboda haka, daga fiye da littattafai ashirin da ya rubuta, a fili take cewa karansa ya kai tsaiko. A wani sabon salon rubutu kuma, marubucin adabin ya rubuta sabon littafinsa mai suna Rayuwa Da Ayyukan Dakta Bukar Usman Na Adabi.

A insaniya irin ta ]an’Adam, kowa da irin basirar da Allah ya ba shi daidai gwargwado, kuma wannan yanayi shi ke haifar da amfani da wannan basira ta hanyoyi mabambanta. Sai dai kuma daga cikin irin wa]annan mutane, sai kuma ka samu wasu da suka yi fice cikin sarrafa tasu basirar ta yadda al’umma gaba ]aya suna fa’idantuwa da gudummawarsu. Irin wa]annan mutane ba su cika yawa ba, kuma wannan shi ne ma dalilin da ya sa ake yi masu la}abi da ‘Yan-baiwa!

Shekarun gaba na rayuwar Bukar Usman sun tunasar da shi zamantakewar garin Biu. A halin yanzu da yake cikin shekarun girma, tsohon babban sakataren ya share fagen ]orewar ayyukansa na adabi cikin wannan sabon littafin nasa mai ban sha’awa. Wannan ]an-baiwa ya amsa kiran shiga ayyukan rubuce-rubucen adabi ne bayan ya yi ritaya daga aikin gwamnati. Sai dai kuma ya da]e da aza al}alaminsa cikin rubuta tarihinsa a littafin  Hatching Hopes  a shekara ta 1999. A shafukan farko na sabon littafin  Rayuwa da Ayyukan Dakta Bukar Usman na Adabi  yana cewa “Na shiga duniyar rubuce-rubuce cikin fagen nan da marubuci ke waiwayen zubi da tsarin rayuwa”.

Tun kafin fitowar wannan aiki na adabi a shekarar da ta gabata, tuni marubucin ya wallafa fiye da littattafai guda ashirin a cikin shekaru bakwai kawai. Ya fara aikin rubutu ne daga ‘yan rubuce-rubucen jawabai da suka shafi ayyukan ofis, kuma sune tushen samuwar littafinsa mai suna Voices in a Choir: Issues in Democratisation and National Stability in Nigeria. Sauran littafan day a rubuta sun ha]a da  Press Policy and Responsibility: The Interface of the Muse and Government Protocol  da kuma  Democracy, Human Right and National Stability. Irin wannan salon rubutu ya taimaka gaya wajen fito da hikimarsa ta rubuce-rubuce. Saboda haka, ko da ya rubuta tarihinsa, sai kuma wata dama ta samu ta bayyana }warewarsa a wannan fagen.

A cikin sabon littafinsa, ya bayyana wa masu karatu cewa “Daga rubuta littafina na farko, sai kuma salon rubutuna ya sauya cikin sabon salon isar da sa}o mai }ayatarwa. Wannan canji kuwa a fili yake musamman a rubuce-rubucena na cikin jaridu bayan shekarar 1999. Wato na bambanta rubutun jarida da na aikin ofis ta fuskar salo cikin sau}in fahimta da kuma adon harshe. Ga misali, yayin da na tanadi jawaban cikin littafin  Voices in a Choir  domin masu sauraro, su kuma littattafan Hatching Hopes  da rubutun jarida kai tsaye suke magana zuwa ga mutane. Sakamakon da ake samu daga wannan salo ya nuna cewa mutane sun fi son a yi magana da su kai tsaye”.

Saboda haka a maimakon za~in kasancewa mai rubutun }ir}ira, sai ya ]auki salon magana da mutane kai tsaye, wanda a ganinsa mutane sun fi fahimta. Daga cikin magabata masu irin wannan salo akwai Ngugi wa Thong O  wanda littafinsa mai suna  The River Between  ya yi tasiri }warai da gaske. A hain yanzu Dakta Bukar Usman, a matsayinsa na ]alibin rubuce-rubucen hikima ya maida hankali ga koyo daga  magabata. Tuni dai ya fahimci cewa amfani da salo mai armashi cikin za~in kalmomi da ginin jumloli masu sau}i shi ne ya haifar da kar~uwar ayyukan Ngugi. Haka kuma ya amincewa  Onwa Ikenna Ndaguba  (1935 – 2011), mutumin da yake ]auka tamkar Walter Cronkite a fagen magana kai tsaye. Wannan gwanin nasa kuwa, shi ne ya jagoranci bukin gabatar da littafinsa mai suna Voice in a Choir a shekara ta 1999, da kuma  Hatching Hopes (tare da wasu na }ananan labaru guda hu]u) a Abuja.

Sai dai kuma kash sai wannan manufa ta samu cikas, amma nan da nan ya fahimci cewa ai ya ma fi sau}i a isar da sa}o kai tsaye fiye da rubutu zube. A shafi na goma (p.10) na sabon littafinsa yana cewa “Daga lokacin da mutum ya yi rubutun farko, to akwai kalmomi da sassan jumlolin da ka iya kawo matsala. Haka ba ya faruwa a yanayin magana kai tsaye”. Baya ga batun rubutu cikin salo da harshe mai sau}i, ya kuma gano muhimmancin yin adalci a cikin rubutu. Ba shakka ya fuskanci }alubale wajen yin adalci ga ‘yan wasan da suka fito a ayyukansa da suka gabata.

Ga misali, a littafinsa na The Bride Without Soars and Other Stories  da aka wallafa a shekara ta 2005, gudummawar  Edward Muir  ta }arfafa batun tantance }arfi da kuma raunin kowane ]an wasa. Sai dai kuma matsalar muhallin da za a gabatar da wa]annan bayanai ma abin lura ne. A matsayinsa na marubucin }ananan labaru, ya gano cewa ba shi da filin da zai zuba dukkan wa]annan bayanai. Watakila yana iya bayani na ]an wasa ]aya ko biyu amma ba duka ba. Haka kuma an samar da wasu ayyukansa guda biyu bayan na labaru, to sai dai ba kamar na farkon ba mai labaru goma, guda biyun (wato The Stick of Fortune and Girls in Search of Husbands) suna }unshe da labarai takwas-takwas ne kowannensu.

A ta bakin marubucin “Kowane labarina yana da tsawo fiye da na gargajiya cikin zubi da tsari da ‘yan wasa da kuma maganganu, to amma kuma ban canja yanayin ingancin ‘yan wasan ba. Ta wannan haujin, na yi amanna da al’adu da yadda ake aiwatar da su”. Littafan Dakta Bukar Usman cikin Hausa rukuni biyu ne. Na farko ya }unshi littattafai guda shida da aka wallafa a shekara ta 2005: Marainiya da Wasu Labaran Jarumin Sarki  da  Yarima da Labbi da Tsurundi  da Sandar Arzi}i  da kuma [ankutungayya.  Rukuni na biyu kuwa da aka wallafa a shekara ta 2009 yana }unshe ne da littattafai guda takwas: Gwaidayara  da [an Agwai  da Tsohuwa da ‘Yan Mata Uku  da [ankucaka  da Al’ajabi  da  ‘Yargata  da  Daguli [an Bajinta  da  Muguwar Kishiya. Su wa]annan littattafan na Hausa (ba kamar na Ingilishi da kamfanin Klamides ya buga) kamfanin Gidan Dabino ne ya wallafa su.

Daga nan kuma sai yabo dangane da wa]annan ]imbin ayyuka daga sassa daban-daban. Wata }ungiya mai zaman kanta IRENE  ta }asar Jamus ta nemi izininsa domin sarrafa wa]annan ayyuka daga Hausa zuwa Ajami da kuma Boko, kuma tuni ya amince. {ungiyar na kuma son amfani da wa]annan ayyuka domin ilimantar da ‘yan mata da ke karatun allo a Nijar. A Kano ma, makarantar furanare ta Capital ta fara amfani da littattafan a cikin manhajar karatunta daga aji ]aya zuwa biyar. Domin bayyana gamsuwa da kuma godiya, Dakta Bukar a shafi na goma sha tara na sabon littafinsa yana cewa “A yau ina alfahari da nasarorin da na samu wajen wallafa littattafan labaru guda hu]u cikin Ingilishi da kuma wasu goma sha biyar cikin Hausa ]auke da labaru na hikimomin rayuwa. Na goma sha biyar kandami ne ]auke da wa]annan littattafai sha hu]u da kamfanin Gidan Dabino ya wallafa”.

Idan wannan sabon littafi na Rayuwar Bukar Usman da Ayyukansa na Adabi ya }ayatar, to hakan ya faru ne saboda tsara shi cikin babi-babi hu]u. Kashi na farko bayani ne ga mai karatu dangane da yadda ya sami kansa cikin wannan aiki da kuma irin salon da yake amfani da shi.  A sauran sassan kuma, marubucin ya kwance bakin jaka ne cikin ayyukansa da ya gabatar amma fa wa]anda suke na labaru ba. Akwai kuma jawabai da sharhi kan al’amuran da suka shafi rayuwa daban-daban. Shi wannan littafi mai shafuka ]ari biyu da talatin da biyar ba  tsari ne na abubuwan da suka faru cikin lokaci guda ba. A maimakon haka sai aka karkasa littafin ta la’akari da jigo domin baiwa mai karatu hoton rayuwar marubucin. Daga nan kuma sai aka yi tsari mai armashi a babi na uku da na hu]u na littattafin. Tambayar a nan ita ce, shin ko rayuwar Biu ta ta~a sa Dakta Bukar Usman tunanin cewa wata rana zai zama marubuci? Idan haka ne, to ko ya samu damar isar da  sa}onninsa? Ba abin mamaki ba ne ganin yadda ya shahara a aikin gwamnati Sai dai kuma ya kasa jure bukatar rubuta }warewarsa a aikin gwamnati.

{warewarsa a harsunan Ingilishi da Hausa (duk da cewa ba nasa ba ne) sun taimaka masa wajen zama gwani a rubuce-rubucensa. Ga abin da yake cewa “Ban ta~a tunanin wata rana zan sarrafa su a rubuce-rubuce ba, musamman ma idan aka yi la’akari da cewa karatu da rubutu abu ne daban, kuma amfani da su domin rubuta labaru wani abu ne daban. Ta wannan haujin ne na fa’idantu da gudummawar editocina”. Daga littattafansa guda biyu, wato guda kan tarihin garinsu mai suna  A History of Biu  da kuma wani kan tasirin aikin gwamnati a Nijeriya, to a fili take cewa akwai wasu ayyuka na gwaninta da }ayatarwa a nan gaba.

A sanadiyar yabawa }o}arinsa ne na adana tatsuniyoyin al’ummarsa, aka na]a shi shugaban kwamitin farfa]o da }ungiyar nan ta  Nigerian Folklore Society,  kuma mamba a cikin dattawan }ungiyar da aka ]orawa alhakin adana da kuma inganta harshen Hausa da al’adun Hausawa. Ta haka ne, rayuwar wannan marubuci cikin mizanin auna mu’amala da zamantakewa suka sa ya zama ]an-baiwa!

_________________________________________

Dokta Bukar Usman Ya Zama Gwarzon Adabin Hausa

http://nnngtk.com/2017/03/09/dokta-bukar-usman-ya-zama-gwarzon-adabin-hausa/

Daga Zubair Abdullahi Sada

KUNGIYAR Alkalam ta marubuta Hausa mai dimbin mambobi mawallafa littattafai da take a birnin Kaduna garin Gwamna ta zabo fitaccen mawallafin nan kuma shugaban kungiyar Folklore Association of Nigeria (NSF), Dokta Bukar Usman domin ya karbe lambar karramawa da kwarewa kan ‘Adabin Hausa’ na marigayi Dokta Abubakar Imam.

Dokta Bukar Usman ya karbi wannan lambar ne ta adabin Hausa da aka yi wa lakabi da ‘Hikaya’ a wajen taron ranar marubuta ta duniya da aka gudanar a ranakun 3 da 4 ga wannan wata na Maris, 2017 a dakin taro na gidan Sardauna, wato ‘Arewa House’ da ke Kaduna garin Gwamna.

Da yake karin bayani kan lambar da za a bai wa Dokta Bukar Usman, Uban kungiyar ta Alkalam, Mahmoon Baba Ahmad ya ce, irin wannan lambar karramawa za a rika bayar da ita ne duk shekara ga bayin Allah irin su Dokta Bukar wadanda Allah ya yi masu baiwa kuma suna amfani da ita baiwar suna daukaka adabin na Hausa.

A nasa jawabin godiya ga wannan lambar karramawa ta adabin Hausa da aka ba shi, Dokta Bukar Usman ya ce, ba ya da wata kalma da zai iya nuna farin cikinsa dangane da wannan kyauta, sai dai ya ce, yana matukar godiya da wannan kyauta da ‘ya’yan wannan kungiya ta Alkalam suka yi masa. Allah kuma ya bar zumunci.

Idan ba a manta ba shi dai Dokta Bukar Usman mawallafin littattafan Hausa ne da dama da suka hada da ‘Taskar Tatsuniyoyi’ da ‘Tarihin Garin Biu’ da sauransu. Haka akwai aikace-aikacensa a mujallu da jaridu da kuma laccocin da yake gabatarwa a Jami’o’in cikin gida Najeriya da kuma kasashen ketare.

Dokta Bukar mutum ne mai neman ilimomi wanda yake bincikensa bayan ya nuna sha’awarsa a kan yanayi da tsirrai, kuma wannan ne ya sanya shi zama daya daga cikin manyan manoma a Najeriya.

* An buga wannan labari ne a mujallar GaskiyaTaFiKwabo, a ranar  9 ga watan Maris, 2017