LITTAFIN FALSAFAR BUKAR USMAN

 Littattafai

 Labarai  Rahoto
 Tatsuniyoyin  Takardar Girmamawa

Sharhi

 Ra’ayin Mutane

 

Dokta Bukar Usman

 
 

 Littattafan Taskar Tatsuniyoyin Hausa Sun Sami Tagomashi:

 Za a Juya Su Zuwa Ajami

A ranar Juma’a 28 ga watan Mayu na shekarar 2010 ne aka sanya hannu a kan yarjejeniyar juya wasu  labaran da ke cikin littattafan TASKAR TATSUNIYOYI na Dr. Bukar Usman OON, zuwa rubutun Ajami, a matsayin littafi, wanda za a hada Hausar Boko da kuma Ajami a waje daya, wato in an karanta rubutun Ajami sai kuma a karanta Hausar Boko a gefe da gefe. An yi wannan yarjejeniya bayan tattaunawa  a Tahir Guest Palace da ke unguwar Nasarawa GRA da ke jihar Kano Nijeriya da misalin karfe 4.00 zuwa 6.15 na yamma. An yi wannan yarjejinya ne tsakanin kamfanin Gidan Dabino International, da ke Nijeriya da kamfanin Editions Gashingo da kuma EIRENE Sahel da suke a Yamai ta kasar Nijar.

Mallam Abdou Bako shi ya sanya hannu a madadin kamfanin Gashingo. Sai kuma Mr. Thomas Buttner, Bajamuse, ya sa hannu a madadin kungiyar EIRENE Sahel. Ado Ahmad Gidan Dabino, shi ne wanda ya sanya hannu a madadin marubuci Dr. Bukar Usman da kuma kamfanin Gidan Dabino International. Labaran da aka zaba za a buga su ne kamar haka:

Littafi na daya wato Marainiya, an dauki labarai guda hudu, Marainiya da Wani Sarki Da Matansa da Mace Mai Ciki da kuma ‘Yan Mata Masu Kamun Kifi.

A cikin littafi na biyu kuwa wato Jarumin Sarki, an debi labarai guda uku ne, Jarumin Sarki da Kishiyoyi Biyu da kuma Wata Mata Mai Ya’ya Biyu.

A cikin littafi na uku kuwa wato Yarima Da Labbi, an tsamo labarai biyu ne, Yarima Da Labbi da kuma ‘Yar Sarkin Da Ta Saci Dinya.

 A littafi na hudu kuwa wato Tsurondi, an dauki labarai hudu ne,  Tsurondi da Binta ‘Yar Sarki da Wata Mayya Da Danta da kuma ‘Yan Bakwai Da Aljana.

 Sai kuma cikin littafi na biyar wato Sandar Arziki, inda aka kwashi labarai ukuMakauniya Da Danta da ‘Yar Mowa Da ‘Yar Bora da kuma Wata Mata Da Aljana.

A cikin littafin Dankutungayya wato littafi na shida kenan, an dauki labarai biyu ne, Nasiru Da Nisiru da kuma ‘Yan Mata Biyu.

Shi kuwa littafi na bakwai wato Gwaidayara, an tsamo labarai biyu ne,  Darajar Neman Sani da kuma Talume.

Littafi na takwas, Dan Agwai Da Kura ke nan, an zakulo labarai biyu, Samarin Barayi Uku da  kuma Cin Amanar Dan’uwa.

Tsohuwa Da ‘Yan Mata Uku shi ne littafi na tara, inda an lalibo labarai har guda biyar a cikin sa, Tsohuwa Da `Yan Mata Uku da Garin Da Ba Maza Sai Mata da `Yan Matan Fangama da Jika Da Kaka da kuma Dawi Mai Turmi.

A cikin littafi na goma sha daya wato Al’ajabi, an dauki labari daya ne kacalMugun Nufi.

A littafi na goma sha biyu, `Yargata, an debi labarai guda hudu,`Yargata da Auren Ya Da Kanwa da Mace Da `Ya’yanta Uku da kuma Sarki Mai Sha’awar Mata.

 Duguli Dan Bajinta shi ne littafi na goma sha uku, wanda a ciki aka dauki labarai mafi yawa, wato labarai shida aka tsamo daga ciki, Duguli Dan Bajinta da Auren Sarki Da ‘Yar Maharbi da Makafin Barayi da Kishiyoyi Biyu da kuma  Kishiyoyi Biyu Da Dodanni.

Duka labaran da aka zaba suna yin magana ne a kan aure da zaman kishiya da kuma sauran harkokin da suka shafi rayuwar mata.

A yarjejeniyar an yarda za a dauki wasu labarai ne daga cikin littattafan Taskar Tatsuniyoyi guda goma sha hudu wadanda suka fito kasuwa; an zabe labarai guda talatin da bakwai wadanda suke da shafi 172, wato na rubutun Boko kenan, in da za a juye su da rubutun Ajami a hada su waje guda. Za a fara da rubutun Ajami sai kuma na Boko ya biyo baya, wato in an bude shafin Ajami daya sai a tarar da na Boko daya, da haka har a gama iyakacin adadin shafukan.

Sannan za a sake zanukan da ke cikin littafin na asali wato wanda aka yi a nan Nijeriya, su kuma daga can kasar Nijar za su sake wasu zanukan da za su dace da yanayin can kasar Nijar da kuma nan Nijeriya.

Wannan sabon littafi da za a fito da shi za a yi shi kashi biyu, wato littafi na daya da na biyu, wanda kowanne zai kai akalla shafuka dari biyu, gaba daya zai kai shafuka dari hudu kenan, na daya da na biyun.

Bayan haka kuma girman littafin wato fadi da tsayinsa zai wuce na Taskar Tatsuniyoyi na asali wato na Boko da aka fara bugawa a nan Nijeriya.

Kungiyar EIRENE Sahel ne za su dauki nauyin aikin juyar labaran zuwa rubutun Ajami da sake zanukan ciki da kuma buga su.

Littattafan za a bayar da su kyauta ne ga makarantun allo na jihar Maradi da ke kasar Nijar, amma a Nijeriya za  a sayar da su ne.

Bugan littattafan zai zama  mai ingancin gaske, wato wajen takardu da bangon da za a yi amfani da su za su kasance masu nagarta sosai.

 

Wadanda za su Gudanar da Aikin

GASHINGO: Kamfanin Gashingo, yana da ofis a Yamai babban birnin Kasar Nijar. An kafa shi ne a shekarar 2006 da nufin bunkasa harkar wallafe-wallafe da kuma sauran ayyukan ilmantarwa a kasar Nijar da afrika da kuma duniya baki daya. Kalmar ‘Gashingo’ tana nufin Hawainiya, wato suna iya rikidewa yau su shiga wannan sabga gobe su shiga wancan, kamar yau an gan su a harkar rubutun littattafai gobe kuma ana iya ganin su ta wata harkar kamar ta finafinai ko wata dai daban, suna gudanar da ayyukansu da hukumomi da kungiyoyi na kasashen duniya daban-daban, kamar UNESCO da OIF da EIRENE da dai sauransu.

EIRENE SAHEL: Kungiya ce mai zaman kanta wadda take gudanar da ayyukanta tsakanin kasashen duniya, amma tana da matsuguni a kasar Jamus tana kuma gudanar da ayyukan tallafi ga al’umma a Amurka ta Arewa da Amurka ta Kudu wato Latin Amurka da kasashen Asiya da Afrika da sauran kasashen duniya. Ma’anar kalmar EIRENE, an samo asalin ta ne daga kasar Girka. A Girkanci kalmar EIRENE tana nufin ‘Zaman Lafiya’.

An kirkiro wannan kungiya ne jim kadan bayan kammala yakin duniya na biyu, a lokacin da matsaloli suka addabi nahiyar Turai da kuma sassan duniya daban-daban.

EIRENE tana gudanar da ayyuka a kan jinkai, musamman domin jaddada zaman lafiya tsakanin al’ummomin duniya gaba daya da kuma ayyuka daban-daban, wadanda  suka hada da samar da fahimtar juna da jaddada zaman lafiya tsakanin al’ummar duniya. Misali, a Nijar tana  gudanar da yekuwar neman sulhu tsakanin al’umma, kamar makiyaya da manoma ta hanyar amfani da tattaunawa ba tare da amfani da makami ba. Kuma suna buga littattafai cikin harsuna daban-daban musamman harsunan gida da kuma na rubutun Ajami da tallafa wa makarantun allo a kasar Nijar.

GIDAN DABINO INTERNATIONAL: Kamfanin Gidan Dabino an kafa shi ne a shekarar 1990 da sunan Gidan Dabino Publishers Enterprises. Bayan shekara goma wato a shekarar 2000 aka sake yi masa wata rijastar da sunan Gidan Dabino International Nigeria Limited, wanda yake da sassa uku, wato Gidan Dabino Publishers da suke buga littattafai da Gidan Dabino Bookshop masu tallata littattafai da kuma Gidan Dabino Video Production da suke shirya finafinai. Kamfanin yana gudanar da ayyukansa a kan buga littattafai da shirya finafinai da kuma sauran harkokin ilmantarwa a Nijeriya da kuma yin huldar aiki da wasu kungiyoyi da hukumomi na kasashen duniya, kamar UNESCO da OIF masu shalkwata a kasar Faransa da British Council da DFID da suke kasar Ingila da Rediyon Muryar Jama’ar Jamus da ke Bonn kasar Jamus da SJG da SFH da suke Nijeriya da kuma Edition Gashingo da ke kasar Nijar.

Dokta Bukar Usman, OON: Marubucin wadannan littattafai guda goma sha hudu na Taskar Tatsuniyoyi, ya yi aiki a Gwamnatin Tarayya har na tsawon shekaru talatin, inda har sai da  ya kai mukamin Babban Sakatare (Permanent Secretary) a Ofishin Shugaban kasa, wato Presidency, kafin ya yi ritaya a shekarar 1999.

Har ila yau kuma ya rubuta littattafai na Turanci guda shida:

  1. Voices In A Choir: Issues in Democratisation and National Stability

          In Nigeria.

  1. Hatching Hopes (Tarihin Rayuwarsa).

  2. The Stick of Fortune and Other Stories.

  3. Girls In Search of Husbands and Other Stories.

  4. The Bride Without Scars and Other Stories.

  5. The Hyena and the Squirrel.

Saboda sha’awarsa wajen taimaka wa ilmi da kuma al’umma ya sanya Dr. Bukar ya kafa gidauniya mai suna Dr. Bukar Usman Foundation, domin tallafa wa harkar ilmi da sauran al’amuran al’umma marasa karfi a rayuwa.

Bayan littattafan labarai na tatsuniyoyi, yana kuma kan aikin wadannan littattafai don mayar da su cikin littafin zane, wato cartoon. Bayan haka kuma za a mayar da su cikin fim din zane-zane (cartoon) irin na Tom and Jerry.

Saboda kasancewar Dr. Bukar Usman mutum mai son yada ilmi ba don ya sami abin duniya ba, shi ya sa ya shiga rubuce-rubucen littattafai ka’in-da-na’in, sannan kuma da ya buga littattafansa na Turanci guda shida da kuma na Hausa wato Taskar Tasuniyoyi guda goma sha hudu, sai ya rage farashin su, wato farashin da ake sayar wa jama’a bai kai farashin da aka biya aka buga littattafan ba. Haka kuma da aka tuntube shi game da juyar wadannan labarai da ke cikin littattafansa, nan take ya ji dadi kuma ya yi na’am da wannan shiri da hannu biyu-biyu, ya kuma sauta wajen bayar da izinin yin wannan aiki, da kuma ba da kwarin gwiwa wajen yin hadin gwiwar aiki da aka shirya tsakanin Gidan Dabino na Nijeriya da Gashingo na kasar Nijar da kuma EIRENE ta kasar Jamus.

Na tuno da wani kokari da Farfesa Abdalla Uba Adamu ya yi ta yi tun a cikin shekarar 1999, lokacin da ya gabatar da wata makala mai taken “Ajamization of Knowledge: Challenges and Prospects of an Educational Strategy” a matsayin Babban Bako mai jawabi a FCE Kano. Kai hasali ma dai a laccarsa ta jaddada farfesancin sa (wanda ya samu a 1997) ya gabatar da laccar mai suna “Sunset at Dawn, Darkness at Noon: Reconstructing the Mechanisms of Literacy in Indigenous Communities” wacce ya gabatar ranar 24 ga Afrilu, 2004 a Jamia’ar Bayero ta Kano.

Duk fafutukar da yake yi don a dinga yin rubuce-rubuce da za a bayar a makarantun allo na tsangaya ko kuma fassara wasu rubuce-rubucen daga Hausar boko zuwa Ajami, amma abin ya gagara.  Har yau shiru kake ji wai malam ya ci shirwa. Kuma duk wannan hobbasa day a yi ba ta yi tasiri ba a wajen manazarta da marubuta a Kano, inda wadansu fitattun marubutan ma suke ganin duk shirme ne, wai saboda ba tabbacin cewa Almajiran da Farfesa Abdalla ya damu mutane da su za su iya ma karanta Ajamin da yake damun mutane da shi.

Ya kamata a ce a jihar Kano hukumomin da aka kafa don kula da makarantun allo da tsangayu su amshi wannan shawara da hannu biyu amma ina, an yi shakwalatin bangaro da batun. Amma abin mamaki ga wasu kungiyoyi daga kasashen waje sun zo da burin yin wannan aiki. Abin dai da kunya.

Kuma ba zan manta ba, a cikin watan Satumba 29 zuwa 2 ga Oktoba 2009 na halarci  wani taro a Adis-Ababa ta kasar Itofiya, wanda UNESCO da UNESCO institution for Lifelong Learning ta kasar Jamus da kuma ISESCO suka shirya an gayyace ni, taron an yi masa take da, ‘Cross-regional Workshop on Capacity-building for LIFE in Asia, Sub-Saharan Africa and the Arab States: Adult (15+) Literacy in Multilingual Contexts, mu biyu muka je daga Nijeriya, ni daga  kamfani mai zaman kansa da ke Kano sai kuma wata mataimakiyar darakta a ma’aikatar ilmi ta tarayyar Nijeriya da ke Abuja, kuma na gabatar da takarda mai taken: ‘Languages and Literary Development in Multilingual Publishing in Northern Nigeria’ Kasashe goma sha hudu ne suka halarci taron, kuma ba a tashi daga taron ba sai da aka yi zancen buga littattafai cikin rubutn Ajami. Kai har littattafan da aka yi da Ajami sai da na saya na kai wa ita jami’ar shirya taron Farfesa Hassanatou Aliodou da ta zo daga kasar Jamus. Sannan kuma na tafi da littafan Taskar Tatsuniyoyi, na Dr. Bukar da littafin Bashr Tofa da sauran wasu littattafan da muka buga, duk  na rabar da su kyauta ga mahalarta taron da suka zo daga kasashe goma sha hudu. Kuma sai da na shirya wani fefen CD wanda aka dauki mata hudu da namiji daya suka karanta littattafan Hausa na labarai da tatsuniyoyi cikin hausar boko, sannan muka dauki na rubutun Ajami da kuma na Fulfulde wanda aka nuna wa mahalarta taron can kasar Itofiya.

Don haka lokaci ya yi da hukumominmu za su farka su gane abubuwan da ya kamata su sa hannunsu a ciki, ba su yi watsi da shi ba su bar wa baki kawai.