Bayan Ya Kammala Gina Wa Hausa Taskoki 14

Dakta Bukar Usman Ya Fara Shirin Korar ‘Tom And Jerry’

A satin da ya gabata kun karanta ta}aitattun bayanan da littattafan nan Taskar Tatsuniyoyi su ka }unsa, wa]anda hazi}in mai kishin Hausa Dakta Bukar Usman ya rubuta. to litattafan nasa ba na [aya zuwa na Shida ba ne ka]ai. Dakta Bukar ashe ya }ara maleji inda a halin yanzu ya kammala sauran taskokin inda sun kai goma sha hu]u. Babu abin da ya rage ga Hausawa sai kawai su yi tururuwa su na shiga taskokin su ci albarkacin ]an }abilar Babur.

Bukar Usman ya shaida wa LEADERSHIP HAUSA cewa a yanzu haka aiki ya kankama inda za a maida wa]annan litattafai 14 a matsayin tatsuniyoyin da za a ri}a kallo a cikin talbijin ta hanyar warware su a fayafayen CD. A ta}aice dai wata hikima ce Dakta Bukar ya shigo da ita doin hana yaran Hasawa kallon Tom and Jerry. Lallai sau}i ya samu domin nan ba da da]ewa ba za mu ri}a ganin su Gizo da {o}i da sauran dodannin cikin tatsuniyoyi su na magana da Hausa. Ya rage ga Hausawa su tashi tsaye su kar~i wannan yin}uri da hannu bibbiyu.

Yanzu dai a jimlace litattafan Dakta Bukar Usman 14 na tsakar Tatsuniyoyi su ne:

Littafi Na [aya: Marainiya

Littafi Na Biyu: Jarumin Sarki

Littafi Na Uku: Yarima Da Labbi

Littafi Na Hu]u: Tsurondi

Littafi Na Biyar: Sandar Arziki

Littafi Na Shida: [ankutungayya

Littafi Na Bakwai: Gwaidayara

Littafi Na Takwas: [an Agwai Da Kura

Littafi Na Tara: Tsohuwa Da ‘Yan Mata Uku

Littafi Na Goma: [ankucaka

Littafi Na Sha [aya: Al’ajabi

Littafi Na Sha Biyu: ‘Yargata

Littafi Na Uku: Duguli [an Bajinta

Littafi Na Sha Hu]u: Muguwar Kishiya.

Ga ka]an daga cikin abubuwan da ke cikin littafi na 7 zuwa na 14:

A cikin wannan littafi mai suna Gwaidayara an yi amfani da mutane da wasu namun daji da }wari da tsuntsaye. Littafin kuma ya }unshi tatsuniyoyi tara ne, kowacce da irin abin da take koyarwa.

[aya daga cikin wa]annan tatsuniyoyi ta }unshi yadda ake so mutum ya zama mai kyautata wa jama’a da yi musu alheri da muhimmancin girmama bako, sannan an nuna muddin ka shuka alheri shi za ka girba a rayuwarka.

A cikin littafi na Takwas: A cikin wannan littafi mai suna [an Agwai an yi amfani da mutane da wasu namun daji da }wari da tsuntusaye. Littafin kuma ya }unshi tatsuniyoyi goma sha ]aya ne, kowacce da irin abin da take koyarwa.

[aya daga cikin wa]annan tatsuniyoyi tana nuna mana yadda ya kamata ]an’Adam ya ri}a tausayi da kuma jin}an mutane da kuma dabbobi a matsayinsu na halittun Allah, domin yin hakan ya kan kawo babban alheri ga rayuwar duk mai aikata hakan.

Littafi na Tara: A cikin wannan littafi mai suna Tsohuwa Da ‘Yan Mata Uku, an yi amfani da mutane da wasu namun daji. Littafin kuma ya }unshi tatsuniyoy goma sha uku ne, kowacce da irin abin da take koyarwa.

[aya daga cikin wa]annan tatsuniyoyi tana nuna mana yadda taimakon Allah yake riskar ]an’Adam ba zato ba tsammani, sannan kuma idan mutum ya yi maka mummunan abu a rayuwa, to kai ka yi masa mai kyau, yin hakan zai sa mutumin ya gane kurensa, har ya yi nadama da ga baya kuma ya sauya halinsa.

Littafi na Goma: A cikin wannan littafi mai suna [ankucaka an yi amfani da mutane da wasu namun daji da }wari da tsuntusaye. Littafin kuma ya }unshi tatsuniyoyi goma sha biyu ne, kowacce da irin abin da take koyarwa.

[aya daga cikin wa]annan tatsuniyoyi ta nuna mana yadda illolin yin }arya suke a rayuwa, sannan kuma yaudara ba ta da amfani, haka zalika an nuna cewa kayan aro ba su rufe katara. Abu mafi kyau shi ne kowa ya tashi ya nemi abun kansa.

Littafi na Sha [aya: A cikin wannan littafi mai suna Al’ajabi an yi amfani da wasu namun daji da }wari da tsuntsaye. Litafin kuma ya }unshi tatsuniyoyi goma ne, kowace da irin abin da take koyarwa.

[aya daga cikin wa]annan tatsuniyoyi tana nuna mana yadda ake so mutum idan an gaya masa wata magana ya yi bincike kafin ya yarda da ita ko kuma zartar da hukunci a kan abin da ya ji, domin ]aukar kowacce irin magana ba tare da bincikawa ba, kan jawo da-na-sani. Wannan kuma ya dace da kalaman masu iya magana da ke cewa: “In mafa]in magana wawa ne, to majiyinta kada ya zama wawa.”

Littafi na Sha Biyu: A cikin wannan littafi mai suna ‘Yargata an yi amfani da mutane da wasu namun daji da }wari da tsuntsaye. Littafin kuma ya }unshi tatsuniyoyi goma ne, kowacce da irin abin da take koyarwa.

[aya daga cikin wa]annan tatsuniyoyi tana nuna mana yadda ake so mutum ya zama mai }as}antar da kai ban da yin ]agawa da nuna ka fi kowa, kowane irin matsayi ko ilimi kake da shi, domin duk iliminka ko matsayinka akwai wanda ya fi ka, cikinsu kuwa har da mahaifa da malamanka ko wa]anda suka raine ka a fannin da ka yi fice.

Littafi na Sha Uku: A cikin wannan littafi mai suna Duguli [an Bajinta an yi amfani da mutane da wasu namun daji da dabbobin gida da }wari da dodanni da wasu hanyoyi na siddabaru. Littafin kuma ya }unshi tatsuniyoyi goma ne, kowacce da irin abin da take koyarwa.

[aya daga cikin wa]annan tatsuniyoyi ta }unshi labarin wani maharbi ne mai wata ‘ya kyakkyawa. Saboda tsananin kyanta ba ya bari kowa ya ganta. Wata rana sanda