Yadda Na Gina Taskar Tatsuniyoyi

– Dakta Bukar Usman

Daga Ashafa Murnai Barkiya, a Abuja*

Daidai lokacin da al’ummar Hausawa ke }orafi dangane da wasu ba}in ]abi’u da yara }anana suka yi wa ri}on kamun-kazar-kuku, an samu wani mai kishin Hausa wanda ya tuna baya, ya tattaro wasu tatsuniyoyi da sauran labaran hikimomi ya rubuta su zuwa litattafai ]ai ]ai har guda shida. Bukar Usman dai za a iya cewa wata babbar kyauta ce ga Hausawa a wannan zamanin, domin ba asalin Bahaushe ba ne. Daga jin suna Bukar, mai karatu zai gane asali, tushe, yare da kuma }abilar marubucin wanda LEADERSHIP HAUSA ta ta~a yin cikakkar tattaunawa da shi a farkon 2009.

Litattafan Bukar Usman abokai ne da kuma }awayen hira ga yaranmu ta yadda za su jawo hankulansu daga barin kalle-kallen wasu gur~atattun ]abi’u daga wasu finafinan da ba su dace iyaye na barin ‘ya’yansu su na kallo ba. Sannan kuma marubucin ya gina wata taska a rubuce, inda ya adana tatsunniyoyi wa]anda a da sai a baki ka]ai ake jinsu, hasalima wasu an fara mantawa da su.

 

• Bayani A Kan Mawallafi

An haifi Dr. Bukar Usman ne a garin Biu na }asar Borno, Nijeriya a ranar 10 ga Disamba, shekarar 1942. Bayan ya yi makarantar Firamare a Biu, ya je Maiduguri inda ya yi karatun Sakandare kafin ya je King’s College da ke Lagos inda ya yi karatun share fagen shiga Jami’a. Daga nan ya shiga karatun neman digiri a Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya inda ya kammala da samun digiri a fannin tafiyar da mulki da hul]a da }asashen waje a shekarar 1969.

       Bayan Dakta Bukar Usman ya gama karatu, ya kama aiki a Gwamnatin Tarayya inda ya kai har mu}amin Babban Sakatare (Permanent Secretary) a Ofsihin Shugaban }asa, watau Presidency, kafin ya yi ritaya a shekarar 1999. Saboda yabawa da aikin da Dakta Bukar Usman ya yi da kuma kyaun halinsa, Gwamnatin Tarayya ta ba shi lambar yabo ta }asa ta OON a shekarar 2000.

Koda ya ke Dakta Bukar Usman ya rubuta wasu littattafai a lokacin da yake aiki, ya kama rubuce-rubucen littattafai gadan-gadan ne bayan ya yi ritaya. Wannan littafi ya na ]aya daga cikin wasu da ya wallafa a cikin harshen Hausa a Taskar Tatsuniyoyi.

Dakta Bukar Usman ya na da aure da ‘ya’ya, kuma ya na zaune a Abuja tare da iyalinsa.

Bayan Bukar Usman ya kammala litattafansa shida, a cikin kowane littafi ya yi jawabin godiya inda ya ke cewa:

Godiya ta tabbata ga Allah Ma]aukakin Sarki. Bayan haka, akwai mutane da yawa wa]anda suka taimaka mini wajen ha]a labaran da ke cikin wannan littafi. Duk sun cancanci in yi musu matu}ar godiya. Daga cikin wa]annan mutane akwai Mai Martaba Sarkin Biu, Mai Umar Mus]afa, wanda ya }arfafa mini gwiwa }warai wajen rubuta wannan littafi. Mai Martaba kuma ya taimaka wajen binciko wasu labaran da ke cikin wannan littafi. Sai Kasim Abubkar Imam da Alli Mohammed da Mukhtari Mohammed da Umar Mohammed Biu da Abdullahi Ibrahim da wasu mutanen Biu, tsofaffi da matasa da samari  da ‘yan mata. Cikinsu har da tsohon malamin makarantar firamaren nan da ya shahara wajen sanin tarihin }asar Biu, watau Malam Bemi Biu.

Bayan mutanen Biu, akwai mutane daga wasu sassan }asar nan da suka taya ni shirya wannan littafi. Mislai, akwai Duve Nakolisa mai Kamfanin buga littattafai na Klamidas Communications Ltd. da Alhaji Ado Ahmad Gidan Dabino na Kamfanin Gidan Dabino Publichsers da Salisu Na’inna [ambatta, wani ma’aikacin gwamnati a ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya da Malam Tukur Abdulrahman, Editan jaridar Gaskiya ta fi Kwabo. Bayan su akwai Farfesa [andatti Abdul}adir da Farfesa Bello Sa’id na Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, da Faresa [angambo Abdulkadir na Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, da Farfesa Sa’idu Ahmed Ba~ura, shi kuma na Sashen Koyar da Turanci, dukan su a Jami’ar Bayero, Kano. Sun duba littafin nan, suka yi gyare-gyare tare da ba da shawarwari masu amfani domin tabbatar da ingancinsa. Har wa  yau, akwai Malam Aminu Bin Ladan Abubakar (ALA) da Malam Umaru Labaran Dabo da Malam Aminu Adamu wa]anda suka yi wasu daga cikin zane-zane da ke cikin wannan littafi. Haka kuma ina gode wa Ogwu Godwin da Amos Joshua da Chinasa Ehiemere dukan su na kamfanin G.O.U Systems Limited wanda suka taya ni wajen jerin wannan littafi. Ina shaida wa kowannensu ba zan manta da ]imbin gudunmawar da suka bayar a kan wannan aiki da }ara mini ilimi ba. Na gode musu }warai da gaske. Ina ro}on Ubangiji ya saka musu, ya kuma ba mu lafiya, amin.

  • Kowa ya san ma’anar tatsuniya, watau labari ne ]auke da wasu halaye na gari da hanyoyin warware wasu matsaloli na rayuwa da kuma yin ishara game da wasu abubuwa da sukan faru ga masu aikata munanan halaye kamar mugunta da kwa]ayi da wula}anci ko zalunci ko kishi ko sata da cuta da sakarci da }arya; ko kuma ga masu aikata kyawawan halaye kamar aikata alheri da nuna mutunci da soyayya da ladabi da biyayya da ri}e amana da sada zumunci da nuna tausayi da girmama na gaba da sauransu.

A cikin wannan littafi mai suna Yarima Da Labbi wato littafi na uku, an yi amfani da mutane da wasu namun daji da doddani da macizai da tsuntsaye da bishoyoyi. Littafin kuma ya }unshi tatsuniyoyi goma ne, kowace da irin abin da take koyarwa.

[aya daga cikin wa]annan tatsuniyoyi ta }unshi labarin wani Bafulatani ne da yake kiwon shanunsa a daji, ya ga wata mata ya ri}a yi mata alheri har }auna ta shiga tsakaninsu ya aure ta, suka haifi ‘yan mace. Bai sani ba ashe matar nan macijiya ce. Da ‘yar ta girma sai uwatar ta tura ta wani gari. Duk da cewa yarinyar mummuna ce sai da ta dace ta samu wani ]an Sarki ya aure ta, amma fa bayan uwarta ta ha]iye ta, ta amayar da ita ta koma kyakkyawa. An ce: Alheri dan}o ne ba ya fa]uwa }asa banza.

  • A cikin littafi na hu]u suna Tsuronodi an yi amfani da mutane da wasu namun daji da aljanu da doddani da mayu da }wari da {adangare. Littafin kuma ya }unshi labarin wata mayya ne da ta sa ]anta a gaba sai ta cinye shi, to akwai dokin da yaron ya gada daga mahaifinsa sai kawai ya ]are dokin ya gudu. Da ma ana zaton ita ce ta cinye uban nasa. Da ta samu labarin ]anta ya gudu, sai ta bi sawunsa har cikin dokar daji, inda namun daji suka ba shi mafaka. Ta na zuwa idonta a rufe sai ]aya daga cikin namun dajin nan ya cafke ta ya cinye, ]anta kuma a ku~uta. Makusancinka na iya zama makashinka.
  • A cikin wannan littafi mai suna Sandar Arziki an yi amfani da mutane da wasu namun daji da aljanu da dodo da }wari da sanda. Littafin kuma ya }unshi tatsuniyoyi tara ne, kowace da irin abin da take koyarwa. Sandar Arziki shi ne littafi na biyar.

[aya daga cikin wa]annan tatsuniyoyi ta }unshi labarin wa]ansu marayu ne su biyu, matashi da }anwarsa, wa]anda iyayensu suka bari tun su na }anana. Wan ne kan je farautar abincin da sukan ci. Sannu a hankali har ya saba da namun daji, su kuma sukan taimaka masa.

Da kura ta smau labari cewa ya na da }anwa a gida sai ta zare jiki ta je ta cinye ta. Da aka fa]a wa shugaban namun daji, watau zaki, sai ya tara su ya tambaye su, kowa ya ce ba  shi ne ya cinye ta ba. Sai kurege ya ba zaki shawarar ya umurci kowa ya amayar da abin da a ci a wannan ranar. Nan take, kowa ya yi amai, amma ban da kura, wai ita ba ta da lafiya. Sai da zaki ya yi kurarin zai cinye kura idan ba ta amayar da abin da ta ci ba, sannan ta yi amai, sai ga yarinya ta tashi.

A }arshe namun daji suka far wa kura suka yayyaga ta; macuci }arshensa kunya da halaka.

  • A cikin littafi na shida, mai suna [ankutungayya an yi amfani da mutane da namun daji da wasu dabbobin gida. Littafin kuma ya }unshi tatsuniyoyi goma sha ]aya ne, kowace da irin abin da take koyarwa.

[aya daga cikin wa]annan tatsuniyoyi ta }unshi labarin Ar]o ne da ya samu labarin matarsa ta na da wani kwarto da take kai wa abinci har gidansa su na ma-sha’a idan mijinta ya fita kiwo. Rannan sai ya bi ta har gidan kwarton ba tare da ta sani ba, ya la~e. Da yake ba ta tarar da kwarton ba sai ta ajiye abincin ta fito. Ar]o kuwa sai ya shige ya cinye abincin ya kuma cika akusan da kashi da fitsari, ya fita abinsa.

{warto ya zo shi da abokansa su kwashi girki sai shirgegen kashi suka tarar a cikin akusan, suka fa]a shi da zagi. Da haushi ya kama shi sai ya je ya shirya da wata karuwa don ya huce haushin abin da matar Ar]o ta yi masa. Kafin karuwar ta iso, matar Ar]o ta je ]aukar akusan sai ta tarar an cika su da kashi, sai ita ma ta fusata ta juye kashin da fitsarin akan gadon kwarto, ta fita abin ta.

Da karuwar ta zo ta tarar da gadon ca~a-ca~a da kashi da fitsari sai ta yi masa zagin cin mutunci, ta fice. Kwarto dai ya rasa abin yi sai ya kwashe kayan gadon da tufafinsa duka ya je ya wanke su ya shanya. Da dare ya yi kuma sai Ar]o ya je ya kwashe kayan gaba ]aya ya zuba su a kogi. Da gari ya waye kwarto ya je ]auko kayansa sai ya tarar ko bante babu. Sai kawai ya banka wa gidansa wuta, ya bar garin. An ce: Rama cuta ga macuci ibada.

 

• Gabatarwa

Nakan tuno a lokacin da nake }arami, a kullum da dare bayan ni da sauran yara mun ci abinci, mahaifiyata kan yi mana tatsuniya a cikin harshen Babur/Bura a can garinmu Biu, na }asar Borno.

Idan da rani ne, mukan zauna a tsakar gida, wanda aka kewaye da zana. Wani lokacin kuma ga farin wata ya haske gari garau, kamar mutum ya tinsci allura a }asa; sararin sama kuma cike da taurari birjik, manya da }anana. Idan kuma da damina ne, sai mu zauna a cikin duhu a tsakar gidan, ko kuma a cikin ]akin da aka hura wuta, musamman idan ana ruwa.

Tatsuniyoyin masu }ayatarwa ne }warai, kuma na ji da]insu a lokacin. Wa]ansu tatsuniyoyin na ban tsoro ne, wasu kuwa akwai ban mamaki. Sai dai dukkaninsu su na bu]e mana idanu da }ara mana ilimin zaman duniya da dabarun zama da mutane.

Bayan haka, a lokacin da na fara karatun boko a wajen shekarar 1852, na karanta wasu littattafan Hausa kamar su Ka Koyi Karatu da Ruwan Bagaja da Magana Jari Ce da sauransu masu yawa, musamman wa]anda shaharraren mawallafin nan Alhaji Abubakar Imam ya rubuta. Kai bayan ma na yi murabus daga aikin Gwamantin Tarayya a shekarar 1999, na ci gaba da karanta wasu littattafai da yawa da aka wallafa da Turanci kamar na uwar gidan Janar Domkat Bali, watau Esther Bali, wanda ya }unshi tatsuniyoyin mutanen Tarok da suke zaune a jihar Pilatu, da kuma wa]anda wasu ‘yan Nijeriya irin su Shaihn Malamin Jami’a Chinua Ahcebe da Chief Cyprian Ekwansi da Elechi Amadi suka wallafa. Bugu da }ari, na karanta littattafai da yawa na shahararrun Turawa mawallafa kamar su Chaucer da Shakespeare da Jane Austin da Coleridge da Yeats. Duk wa]annan littattafi sun sa na yi dogon Tunani }warai kan cewa ya kamata ni ma in rubuta littafin tatsunioyyi da wasu labarai daga }asar Biu, watau mahaifata.

A wannan zamani, mutane da yawa sun san wasu littattafi da Turawa suka wallafa domin yaransu, kamar Tom and Jerry da Chalk Zone da Jimmy Newton da Mew Mew Poer wa]anda har yaranmu ma sukan karanta su a namu makarantun, ko kuma su ri}a kallonsu a talabijin ko ta faya fayan bidiyo. Wannan ya nuna cewa akwai wajibci da bu]ata ga ‘yan }asa su tashi tsaye su rubuta littattafai wa]anda suka }unshi labarai irin namu, domin }ara wa yaranmu ilimin da ya dace da }asarsu da yanayinta da ]abi’un mutanenta, watau da misalan irin abubuwan da ke kewaye da mazauninsu.

Wani abin lura shi ne, ko labaran na ‘yan adam ne ko na aljanu ko na dabbobi ko ma dai na wace irin halitta ne, su na nuni ne da halayya ta gari ko mummuna. Bugu da }ari, akan ba da irin wa]annan labarai ne domin a ]ebe kewa, kuma a koyar da darusan rayuwa masu amfani, kamar dai yadda na bayyana tun da farko. Don haka irin wa]annan labarai su na da gindin zama a cikin adabi.

A cikin ‘yan shekarun da suka shige ne na waiwayi wa]annan tatsuniyoyi. Na je Biu musamman na yi bincike domin in samo mutanen da suka san irin wa]annan tatsuniyoyi na da. Na yi haka ne domin ganin yadda yawancin yaran yanzu kan fara karatun boko tun su na ‘yan shekara uku a duniya, kuma idan sun koma gidajensu, sai wasu su shiga kallon finafinan bidiyo da talabijin, ko su sa wa}o}kin Makosa na mutanen }asar Kwango.

To, ina fata wa]annan tatsuniyoyi za su rage haka, domin tun tuni gajerun labarai da tatsuniyoyi kan hana yara fita yawon banza, kuma su zaunar da dattijai a gida cikin iyali.

A lokacin da nake bincike a kan tatsuniyoyin nan, na tuntu~i mutane da dama a }asar Biu, ciki har da wnai da ya yi karatun boko har ya gama jami’a, amma ya ce bai ta~a jin ko ]aya daga cikinsu ba. Wannan abu ya ba ni mamaki da }arfin gwiwar tattara tatsuniyoyin nan a cikin littafi, da fatan yara da manya za su amfana da su.

Wani abin lura kuma shi ne, manyanmu, watau tsofaffi, wa]anda suka iya ba da wa]annan tatsuniyoyi ba su da yawa kamar da, kuma sai raguwa suke ta yi. Sai na lura idan ba an rubuta wa]annan tatsuniyoyi na adabin baka ba, ba shakka za su ~ace nan da ‘yan shekaru ka]an masu zuwa. Allah ya kiyaye faruwar haka, amin.

Duk da cewa akasarin tatsuniyoyin wa]anda na ji ne a }asar Biu, na kawo su ne a cikin harshen Hausa saboda mutane da yawa su samu damar karanta su, kuma su kwatanta su da wa]anda suka sani. Kowa ya san cewa yanzu Hausa ta zama harshen mutane daban-daban a Nijeriya, har ma a }asashen waje. Shi ya sa ma na fara kowace tatsuniya da, “Ga ta nan, ga ta nanku”, maimakon in fara da, “suk suku”, watau yadda ake fara tatsuniya da harshen Babur/Bura, inda masu saurare kan amsa da “sunta”, watau an gayyace ka ka ba da labarin , kamar dai, “Ta zo, mu ji ta” a cikin harshen Hausa.

Ina fata jama’a za su samu }aruwa da wannan gudunmawa tawa.

 

*Leadership Hausa 25 Ga Faburari, – 4 Ga Maris, 2010

Gidauniyar Dokta Bukar Usman ta fito da sabuwar gasa

Wata gidauniya mai tallafa wa al’umma, wacce ke karkashin shugabancin fitaccen marubuci, Dokta Bukar Usman (Dr. Bukar Usman Foundation), ta yanke kudurin samar da sabuwar gasa ga marubutan Hausa.

Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin tsohon Shugaban Kungiyar Marubuta ta Najeriya, Dokta Wale Okediran, a taron Kungiyar Marubuta ta Najeriya da aka gudanar a Minna, Jihar Neja. Kamar yadda  shugaban ya ce, za a fara gudanar da gasar ne daga shekara mai zuwa (2010), inda aka gayyataci marubuta kirkirrun labarai, wasan kwaikwayo da marubuta wakokin hikima da su shigar da littattafansu.

Da yake karin bayani ga wakilinmu, shugaban gidauniyar, marubuci Dokta Bukar Usman, ya ce ya yanke kudurin fito da gasar ne domin tallafa wa marubutan Hausa, domin su fito da hazakar wajen wayar da kan al’umma. Ya ce, ta hanyar irin wannan gasa, za a kara habaka da inganta Adabi Hausa, sannan kuma a samar da ingantattun litattafan Hausa da za su wayar da kan al’umma.

Kamar yadda yace, nan ba da dadewa ba kwamitin gudanar da gasar zai fitar da tsare-tsaren yadda gasar za ta gudana, da kuma yawan kudin da za a ci, da kuma inda za a yi bikin kaddamar da ita.

Dr_Bukar-Usman.gif

ADABI

LALE DA TASKAR ADABIN BAKA TASKAR TATSUNIYOYI NA DR. BUKAR

USMAN

DAGA: SANI MAIKATANGA DA IBRAHIM MUSA GIGINYU

 

Tabbas a wanan zamanin da’irar adana adabin baka na cikin wani hali na takaici da ban tausayi musamman idan aka dubi yadda marubuta na wannan zamanin suka karkata alkalumansu zuwa wata alkiblar da suke ganin anan lagwada ta yi zango.

To amma kasan ba duk aka taru aka zama daya ba, domin da’rar adana adabin bakan ta samu wani bawan Allah wanda za’a iya cewa rabon da wannan da’irar ta yi irin wannan kamun tun zamanin su farfesa Ibrahim Yaro Yahaya da sauran su. Dakta Bukar Usman haifaffen garin Biu ne a can Jahar Borno Najeriya. Daktan da shekara sittin da bakwai a duniya (67) Ya shigo harkar rubutune saboda kishin alkinta adabin baka da yake da shi. Ganin cewa mafi kasarin yaran wannan zamanin sun kasance suna da karancin sani game da irin al’adun su sakamakon barin turbar adabin baka da ga tushe da aka yi. Daktan ya ce, “ada da zarar an ce almuru ya karato to sai ka tarad da duk inda yaro yake tunaninsa na gurin shin yau wacce tatsuniya Baba ko Kaka ko Goggo zata bayar. Sabanin yadda a yanzu kalle-kallen zamani suka fi tasiri a rayuwar yaran wannan zamanin. Wannan maganar haka take, domin a wannan lokacin wannan mahallli da yara ke zama don sauraron wannan tatsuniyar makaranta ce ta farko da ake koyon karatun ilimin zaman duniya. Kowa ya san ma’anar tatsuniya, wato labari ne wanda ke dauke da wasu halaye na gari da hanyoyin dabarun warware wasu matsaloli na rayuwa da kuma yin ishara game da wasu abubuwa da sukan faru ga, masu aikata munanan halaye. Hakan shi ke koyar da kwadayin son zama mutum na gari da kuma kyamar zama mutumin kawai idan an girma.

Saboda muhimmancin wannan makarantar da kuma irin yadda wannan makarantar ta kasance zamani na neman kawad da ita kwatakwata, shi ya sa Dakta Bukar Usman ya ga ya dace da ya shigo wannan harkar don kawowa wannan fanning dauki. Kamar yadda Dakta Bukar Usman ya shaida mana a wata tattaunawa da muka yi da shi a Birnin Kano lokacin da ya bakunci birnin na Kano don halartar bikin kaddamar da wani littafi na farfesa Sa’idu Muhammad Gusau, Daktan ya ce, “Ya dade yana nazarin hanyar da zai bi don ganin cewa adabin baka bai subucewa yaran wannan zamani ba. Ganin yadda shi kansa ya sharbi romon adabin baka a lokacin yana dalibta daga rubuce-rubucen adabin baka da marubuta na baya suka samar. To amma sai ga shi irin wadannan rubuce-rubucen sun yi karanci a wannan zamanin. Dalilin  da ya sa Dakta Bukar ya daura damarar samar da littattafai wadanda za su kasance sun taimaka wajen tattarawa da kuma alkinta adabin baka a wannan shiyyar ta Arewacin Kasar Najeriya da ma duniyar Hausawa.

Daktan Bukar Usman wanda yayi karatun sa na Jami’a share fagen shiga a babbar makaranta nan dake can Jahar Ikkon Najeriya wato King’s College, wadda daga nan ne ya yi karatunsa na jami’a a Jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria, inda ya kamala digiri a fanning tafiyar da mulki da hulda da kasashen waje a shekara ta 1969. Dakta Bukar Usman ya yi aiki a Gwamnatin Tarayya ta Najeriya a inda hakurinsa da juriyarsa suka kaishi ga kaiwa matakin mukamin Babban Sakatare (Permanent Secretary) a Ofishin Shugaban Kasa, wato “Presidency”. Dakta Bukar Usman ya bar aikin Gwamnati a shekara ta 1999.

Masu Magana na cewa “yaba kyauta tukuici”, saboda irin jajircewa da bin doka da ka’ida bisa aiki da kuma irin yadda ya tafiyar da ma’amulolinsa a lokacin da yake aikin gwamnati da kuma bayan ya bari, Gwamnatin Kasar Najeriya ta ga cewar ya dace da ta bawa shi Dakta Bukar Lambar Yabo ta Kasa’ta OON a shekarar 2000, wani yunkuri na cewa Dakta Bukar Usman mun gode da wannan aiki na alkhairi. Dakta Bukar Usman ya fara rubuce-rubucen sa ne da harshen Turanci kuma ya yi rubutu da harshen na Turanci da dama tun cikin 1992.

Littattafan na Turancin sune:-

Voices in a choir – issues in democratization and national stability in Nigeria.

Hatching Hopes-Autobiography

Bride Without Scars

The Stick of Fortune     

Girls in Search of Husbands   

The Hyena and the Squirrel 

Press Policy and Responsibility

Na rubuta littattafai guda goma sha hudu na Hausa a wannan fanning na adabin baka masu taken Taskar Tatsuniyoyi na daya zuwa shida a halin yanzu suna kasuwa tuntuni. Na bakwai zuwa na goma sha hudu da yardar Allah za su fito nan ba da dadewa ba, domin na riga na gama aikinsu tuni. Ta bakin Daktan kenan. Littattafan da dai suka riga suka fito kasuwa cikin jerin taskar tatsuniyoyi na Bukar Usman sune:-

Marainiya (da wasu labarai)

Jarumin Sarki (da wasu labarai)

Yarima da Labbi (da wasu labarai)

Tsurondi (da wasu labarai)

SandarArziki (da wasu labarai)

Dankutungayya (da wasu labarai)

 Marubucin wadda ya fara rubuce-rubucen Hausa a shekarar 2005, kusan a iya cewa ya fito da wani sabon tsari a yanayin littattafan nasa, da yadda duk karshen labari zaka ga an fidda irin.darussan da wannan labarin ke koyarwa. Haka zalika duk littattafan guda shida kamfanin Gidan Dabino Publishers ne suka buga su. Da muka tambayi marubucin ko me yasa hakkan sai ya ce da mu: “Nayi amana da Kwarewar wannan kamfani kan aikin talifi, kuma ga shi shugaban wannan kamfanin shahararsa a fannin rubuce-rubucen Hausa ba inda ba ta kai ba. Saboda irin kwadayin da nake dashi na yin aiki mai ingani shi ya sa naga ba inda ya dace ace anyi aikin tailfin littattafannan nawa illa Gidan Dabino Publishers.”

Dadin dadawa, marubucin ya bayyana mana aniyarsa na samar da wani nau’in littattafai na adabin baka na Hausa na zana wato abin nan da ake kira da turanci “Cartoon”, wanda a ke ganin dan zane da kuma bayanin zanen don samun fahimta ingantacciya ga makaranci.

Tabbas kowa ya ga irin aikin da Dakta Bukar Usman ya aiwatar, zai fuskanci cewa, ba wargi cikin al’amuransa. Haka zalika ya bfirowa da fannain adabi wato matashiya da zata zamewa wannan fannin kurangar kaiwa ga samun dorewar wanzuwar adabin haka a rayuwar al’ummar Hausawa. Ta yadda dabi’u na gari, wayon zaman duniya da sauran al’amuran da za su tabbatar da samun nagartacciyar al’umma, za’a koye su tun daga tushe. Kuma magana ta gaskiya ita ce, in son samu ne gwamnatocin jihohin Arewacin   Najeriya su shigar da wadannan littattafai cikin mannajjar karatun firame karkashin shirin nan na samar da ilimi tun daga tushe wato “Universal Basic Education.” Ba anan Dakta Bukar Usman ya tsaya ba kawai, Daktan ya samar da wata cibiyar taimakawa mabukata wacce a ke kira da suna “Dr. Bukar Usman Foundation.” Ita wannan cibiyar ta taimakawa mabukata na da babban ofishinta ne adireshi kamar haka:

“Plot 637, Kwame Nkrumah Crescent, Asokoro District, Zone A4, Abuja. Da yake Karin bayani wannan cibiyar ta taimakawa mabukata Dakta Bukar ya ce, “Lokaci ya yi da ya kamata a ce mun fuskanci cewa ba komai gwamnati za ta iya yi wa jama’a ba, dole ne mutane daidaiku da kungiyoyi su tashi haikan wajen ganin cewa an samar da wani nau’l na taimakon juna hakan ne ya sa naga ya dace muka kafa wannan cibiyar. Wannan cibiyar a yanzu haka tana da membobi guda saba’in (70) da kuma kwamitin amintattu mutum goma.” Da muka tambayi Dakta ko ya za’a iya samun taimakon daga wannan cibiyar? Sai yace: “Za’a rubuto mana ne ta adireshin ofishinmu da ke Abuja, mu kuma zamu binciki wannan maganar, daga nan in mun gamsu, cikin ikon Allah za’a samu wannan taimakon.”

Kamar yadda Dakta Bukar Usman ya shaida mana, cibiyar tana samun kudaden da take aikace-aikacenta ne ta irin kudaden da shi kansa a matsayinsa na shugaban cibiyar da sauran membobi ke tarawa musamman don wannan aiki na taimakon mabukata. Abin da zamu ce anan shi ne Dakta, Allah ya kara bidu amin. Ga mai bukatar taimakon wannan cibiyar, sai a rubuto zuwa ga babban ofishin cibiyar wato “Plot 637, Kwame Nkrumah Crescent, Asokoro District, Zone A4, Abuja.”