TAFIYA MABUDIN ILIMI:

Ziyara A Kasar Afurka Ta Kudu

Daga Bukar Usman

 

 
 

Zancen da ake na cewa karfin tattalin arzikin kasashen Nijeriya da kasar Afurka ta Kudu ya zarta na kowace kasa a Afurka, zance ne da ke ci gaba da kai kawo a tsakanin masana tattalin arziki. A wani lokaci da ya wuce, an bayyana cewa karfin tattalin arzikin Nijeriya ya zarta na kasar Afurka ta Kudu, bayan da masana tattalin arziki suka yi kididdiga tare da fitar da alkaluma kan karfin tattalin arzikin kasashen. To, sai dai a halin yanzu zancen da ake shi ne, tattalin arzikin kasar Afurka ta Kudu tuni ya yi wa na Nijeriya fintinkau.

Bayan bulaguron da na yi har sau biyu zuwa kasar Afurka ta Kudu, na fahimci cewa idan dai har mutum yana son ya fahimci ainihin matsayin tattalin arzikin kasashen na zahiri, to tilas ya ajiye wadancan alkaluman da masana tattalin arziki suka dogara akan su, sa’ilin nan ya dubi abubuwa na zahiri da ke a cikin wadannan kasashen. Abin da za a mayar da hankali a nan shi ne abubuwan da ake gani a zahiri, don ta haka ne kadai za a iya kwatanta kasashen biyu.

Idan muka fara da birnin Abuja, babbar hedikwatar Nijeriya, to gari ne mai kyau da ya kai duk matsayin da ake bukata. An kafa birnin ne bayan wadanda suka tsara shi sun ziyarci manyan biranen kasashen duniya domin karin samun haske kan yadda za a gina birnin. Biranen Pretoria a Afurka ta Kudu da Canberra a kasar Austiraliya da Islamabad a kasar Pakistan da Brasilia a kasar Burazil na daga cikin kasashe da suka ziyarta. Duk da alamun lalacewar wasu abubuwa a baya bayan nan Abuja ta ci gaba da zama wani birni abin alfahari ga kasar nan. Filin saukar jiragen sama na Dakta Nnamdi Azikiwe, wanda aka sanyawa sunan Shugaban kasa na farko a Nijeriya na daga cikin wurare masu kayatarwa a birnin. A halin yanzu ana kan gyara da fadada filin jirgin. In dai ba an cire ginshikan da aka kafa ba aka kuma kammala gyaran filin jirgin, to zai zamo riga malam masallaci a kwatanta shi da filin saukar jiragen sama na kasa da kasa na Oliver Reginald Tambo na birnin Johannesburg, garin zinare na kasar Afurka ta Kudu. Shi ma wannan filin jirgin an sanya masa sunan daya daga cikin fitattun ‘yan kasar ta Afurka ta Kudu, an kuma kafa shi a shekarar 1952, amma an yi ta yin gyare-gyare da sauya masa suna. Muhimmin gyaran da aka yi masa shi ne a tsakanin shekarar 2009 da 2010 a lokacin da kasar ke shirye-shiryen karbar bakuncin gasar kwallon kafa ta duniya. Wannan filin jirgin tuni ya shiga cikin jerin manyan filayen jirgin na kasashen duniya.

Tafiya ta jirgin sama daga Nijeriya zuwa Afurka ta Kudu na tsawon sa’o’i shida kan iya ba mutum damar kwatanta yadda tsarin birane yake a tsakanin kasashen biyu. Idan mutum ya kalli kasashen biyu daga mahangar wanda ke a cikin jirgin sama, to zai fahimci cewa dukkanin kasashen suna da yanayin shimfidar kasa mai kyau, amma da zaran mutum ya sunkuyo zuwa sauka a filin saukar jiragen sama na Oliver R. Tambo, yanayin garin zai kara burge ka. Irin wannan yanayin ma na Abuja na da kyau da matukar burgewa, amma bai kai kamar na Pretoria ba, babban birnin Afurka ta Kudu, wanda tafiyar rabin sa’a ne akan titi daga birnin Johannesburg.

Tazarar dake tsakanin biranen biyu na Afurka ta Kudu wato birnin Johannesburg da Pretoria za a iya cewa ta ma kusa ta hade, wanda hakan ya mayar da tsakanin wani wajen dake da cunkoson abubuwan hawa akan tituna hudu daga kowane gefe, kamar dai tsakiyar birnin Abuja zuwa Zuba.

A wajen garuruwan Johannesburg, birnin Cape Town da Durban da sauran wasu muhimman wurare an bayyana cewa, cike suke da yanayi mai matukar ban sha’awa da kuma bayyana irin yanayi da tsarin gine-gine da muhalli mai kayatarwa da suka mayar da kasar ta Afurka ta Kudu a matsayin kyakkyawar kasa. Ina sa ran wata rana in ziyarci wadannan wurare domin in ga wadannan kyawawan birane a kasar, amma kafin nan na amince da abin da wani sanannen dan wasan fina-finai na Nijeriya, Bobby Michael ya fada inda ya ce “Abu na farko da ya kayatar da ni a lokacin da na isa a birnin Johannesburg shi ne, duk da cewa kasar Afurka ta Kudu kasa ce a nahiyar Afurka, an gina kasar ne a tsari irin na kasashen Turawa. In dai har ba ka taba ziyartar Afurka ta Kudu ba, to duk wani abu da za ka gani a talbijin game da kasar, to ba ainihin yadda kasar take ba ne. Suna da hanyoyin mota masu kyau idan an kwatanta da wadanda muke da su a Nijeriya, yanayin iska ma za ka ji shi tatacce. kasar dai ta fi kama da kasashen Turai.” (Jaridar Punch, 21 ga Agusta, 2016, shafi na 28).

Ga wanda ke ziyartar wannan kasa daga Nijeriya wadannan abubuwa ne masu ban sha’awa game da kasar Afurka ta Kudu da sun fi gaban a watsar. Amma duk da wadannan abubuwan kyalkyali, akwai wasu abubuwa na zahiri game da zamantakewa ta rayuwa, abin da za a iya kamantawa da karin maganar nan ta Hausawa dake cewa, mutum duk dan tara ne bai cika goma ba. Matsaloli na zamantakewar rayuwa a wannan kasa na da alaka da dadadden tarihin da take da shi na nuna wariya da bambanci a fannonin ci gaban rayuwa. Wadannan manufofin sun ingiza mafi yawan bakaken fata wadanda su suka fi yawa a kasar tare da mayar da su a matsugunai da muhallai marasa kyau, a bangare daya kuma fararen fata marasa rinjaye suka mamaye muhallai masu kyau da samun ingantattar rayuwa. Nuna wariyar launin fata, ya karkasa al’ummar Afurka ta Kudu zuwa wadansu matakai, inda fararen fata suke a matsayi na sama, ya yin da Indiyawa da Malay da sauran fararen fata da suka samo asali daga wadansu kabilu ke bi masu sai kuma bakaken fata a mataki na kasa.

Duk wannan a yanzu ya zama tarihi. Nuna wariyar launin fata an haramta shi a kasar tun bayan da Nelson Mandela ya zamo shugaban kasa na farko a kasar a shekarar 1994. Manufofin wariyar launin fata sun bar wani babban mikin da gwamnatocin da suka biyo bayanta ke ta kokarin ganin magance. Duk da haka akwai burbushin abin da ya gudana a wancan lokaci a wasu matsugunai kamar a garuruwan Mamelodi da Shoshanguve a Pretoria wacce aka fi sani da Soweton Johannesburg. Wadannan wuraren za a iya kwatantasu da Ajegunle a Legas da Nyanya a Abuja, Nijeriya. Wurare da aka yi watsi da su kuma suke neman kulawa musamman a fannin gidaje da sauran abubuwan more rayuwa na zamani.

Wani abu da ya kamata a sani game da kasar ta Afurka ta Kudu shi ne, tsarin da take da shi a halin yanzu, wato daftarin samar da ci gaba nan da shekarar 2030. Wannan daftarin ya fitar tare da shata manufofi da tsare-tsare da za su ciyar da kasar gaba da fitar da ita daga cikin halin da take ciki a yanzu. Manufar da suke son cimma a wannan tsarin shi ne, kawar da talauci da nuna bambanci, domin samar da al’ummar da za ta bayar da dama ga kowa ba tare da la’akari da asali ba, sai dai don kwarewa ko ilimi da kuma aiki tukuru.

Duk da yake kasar Afurka ta Kudu na da yawan mutane da yawansu bai fi kashi daya bisa uku na yawan al’ummar Nijeriya ba, kasar na da fadin kasa fiye da Nijeriya. Kashi 60 daga cikin al’ummar kasar na zaune ne a birane, mafi yawanci a Kudu maso Gabascin kasar a garuruwa Durban da Natal da yankin Kudu maso Arewa a garuruwan Cape Town da Johannesburg da Pretoria (Thuasne) da Limpopo. A yayin da Nijeriya ke da jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya, kasar Afurka ta Kudu na da larduna guda tara.

Daftarin samar da ci gaba na kasar Afurka ta Kudu ya hakikance cewa, akwai karancin ruwan sha a kasar, inda (daftarin) ya bayyana cewa, kasar na a matsayin ta 148 a cikin jerin kasashe 180 kan abin da ya shafi samar da wadatattun ruwan sha. Wannan ya nuna bukatar da ake da ita na tsaftatattun ruwa da kuma ruwa domin aikin noma. Amma duk da wannan kasar ta Afurka ta Kudu ta yi kokari matuka kuma tana kan yin kokari kan abin da ya shafi noma da samar da abubuwan more rayuwa, abubuwan da suka zamo karfen kafa a Nijeriya.

Ta fannin abin da ya shafi makamashi da samar da lantarki ga al’umma, Afurka ta Kudu ta kai matsayin samar da tsayayyar wutar lantarki. Wani abin mamaki a nan shi ne, Afurka ta Kudu ta dogara kacokan ga makamashin Kwal a matsayin hanyar samar da wutar lantarki duk da cewa daftarin samar da ci gaba na kasar ya bayyana cewa, akwai bukatar kasar ta rage dogaro da take da wannan makamashi na Kwal, saboda kokarinta na ganin an magance gurbatar yanayi a duniya. Ganin irin rawar da makamashin Kwal ke takawa wajen samar da wutar lantarki a kasar Afurka ta Kudu zai sa mutum ya yi mamakin dalilan da suka hana masu tsara yadda ake samar da lantarki a Nijeriya yin amfani da Kwal din da ake da shi Okaba da Enugu domin samar da wutar lantarki.

Dogara da iskar gas wajen samar da lantarki a Nijeriya wanda shi ya haddasa matsalolin da ake fama da su na rashin wutar lantarki, ya nuna sakaci da rashin kyakkyawan tsarin samar da makamashin lantarki.

A fannin ciniki da kasuwanci, duk wanda ya ziyarci kasar Afurka ta Kudu daga Nijeriya zai fahimci cewa, tattalin arzikin Afurka ta Kudu da na Nijeriya suna da alaka. Manyan alluna wadanda aka haska fitilu masu fitar da hasken wuta launi-launi ga su nan birjik a ko’ina suna shelanta kasancewar wasu sanannun kamfanoni a Nijeriya. Daga cikin wadannan kamfanoni akwai Bankuna da kamfanonin sadarwa da sufuri da dai sauransu. Amma ta fannin yadda kasashen biyu ke gudanar da kasuwanci, a Afurka ta Kudu akwai kyakkyawan tsari a fannin gudanar da kasuwanci. Ba kamar a Nijeriya ba da manyan shaguna ko cibiyoyin kasuwanci ke warwatse a wurare daban-daban, a Afurka ta Kudu ire-iren wadannan cibiyoyin kasuwanci suna hade a wuri daya mai fadin gaske wanda aka tsara tare da samar da wuraren ajiye abubuwan hawa da kofofin shiga da ficewa wadatattu wadanda na’urori irin na zamani ke kula da su don tantance karbar kudade ba tare da cunkoso ko matsi ba.

Ba kamar Nijeriya ba, manyan garuruwan kasar Afurka ta Kudu ba su da kwamacalar mutane masu sayar da abubuwa a kan tituna, sannan abu mai wuya ne ka ga wani na bara ko sayar da wani abu akan tituna, wannan ya taimaka ta fannin tsaftar birane a kasar Afurka ta Kudu.

kasar Afurka ta Kudu ta bayar da muhimmaci sosai ga fannin ilimi. Jami’ar Afurka ta Kudu da Jami’ar Pretoria da sauran makarantu a kasar na da gine-gine masu kyau da kayan aikin na karantarwa da dakunan karatu da aka shake da littafai. Ko bayan wannan akwai dakunan karatu da dama a ko’ina fadin kasar. Kawai ka tambayi ko wane littafi ka ke nema, idan ma babu shi, to nan take mai kula da dakin karatun zai yi odar wannan littafi ba tare da an caji mai neman littafin ko sisin kwabo ba. Wannan ya sha bam-ban da Nijeriya, inda wasu masu buga littafai ke kokawa da cewa, duk da cewa suna da kusanci da wasu jami’o’i ko makarantun ilimi amma ba su taba sayen littafi daga wajensu ba.

Afurka ta Kudu ta shahara da sanannun gandayen namun daji, kamar dai yadda a Nijeriya muke da gandun daji na Yankari a jihar Bauchi, da na Borgu a jihar Neja da kuma Gumti a jihar Taraba. Sai dai ire-iren wadannan gandayen daji a Afurka ta Kudu ana kula da su sosai kuma suna samun masu ziyara masu dimbin yawa daga cikin kasar da kuma sauran kasashen duniya.

Garuruwa a kasar Afurka ta kudu na da wurare da suka zamo wuraren yawon bude ido ga masu ziyarar kasar. Sanannu kuma daya daga cikin ire-iren wadannan wuraren sun hada da ginin Union (Union Buildings) a birnin Pretoria wanda aka gina a shekarar 1913, an gina shi akan wani tsauni, kuma shi ne mazaunin fadar Shugaban kasa. Wani abu da aka yi daga bayan nan a gaban ginin shi ne, mutum-mutumin Nelson Mandela. Kamar dai mutum-mutumin Liberty a birnin Newyork na kasar Amurka ko na Christ the Redeemer a birnin Rio de Janero a kasar Burazil, shi ma wannan mutum-mutumi na Mandela an gina shi ne mai tsawon mita shida kuma yana a tsaye a cikin wata gadina da aka kawata, ya tayar da hannayensa kuma yana duban birnin Pretoria.

Idan ka gangara a cikin garin Pretoria, akwai gini mai tsayin gaske na gilashi. Kamar dai ginin Babban Bankin Nijeriya, wannan ginin na Pretoria nan ne mazaunin Babban Bankin kasar Afurka ta Kudu. A zagaye da Babban Bankin na Afurka ta Kudu sauran gine-gine ne dake dauke da ma’aikatu da sauran cibiyoyin gwamnati. Idan kai mai yawon bude ido ne, to kar ka sake ba ka ziyarci wata unguwa ba gabascin birnin Pretoria. Mafi yawan wadanda ke a wurin bakake ne, an lakabawa wannan wurin suna da Lagus (daga suna Legas) saboda yawan ‘yan Nijeriya dake a wurin da suke gudanar da harkokin kasuwanci.

Duk da akwai cunkoson abubuwan hawa a titunan manyan biranen kasar Afurka ta Kudu, masu amfani da titunan na tuki cikin tsari da kuma kiyaye dokokin hanya. Dukkanin ababen hawa da kake gani a manyan titunan Afurka ta Kudu sheki suke tamkar wadanda yanzu aka fito da su daga kamfani. Kowa na kiyayewa da kuma jiran umurnin fitilun dake ba da hannu a kan tituna, taka doka kuma zai sa a hukunta ka. Motocin safa masu daukar mutane daga 16 zuwa 18 sune aka fi amfani da su wajen jigilar mutane tare da kai koma daga ciki zuwa wajen birane.

A siyasance, Afurka ta Kudu kamar Nijeriya tana fadi tashin ganin dimokuradiyya ta zauna dindindin a siyasar kasar. Ba kamar Nijeriya ba da ta samu ‘yancin kai a shekarar 1960, kasar Afurka ta Kudu ta samu tabbataccen ‘yanci ne a shekarar 1994, lokacin da Nelson Mandela ya zama Shugaban kasa bayan an gudanar da zaben gama gari. Kafin wannan lokacin kasar na karkashin mulkin wariyar launin fata, wacce Turawa fararen fata ke jagoranta. Tun daga wancan lokacin zuwa yau an gudanar da zabuka da dama a kasar.

Kamar zaben 2015 a Nijeriya, zaben da aka gudanar na kananan hukumomi a watan Agusta na wannan shekara ta 2016 a kasar Afurka ta Kudu yana da muhimmanci matuka, musamman idan aka yi la’akari da sakamakon zaben. Ga al’ummar kasar da kuma jam’iyyun siyasa zaben wani gagarumin ci gaba ne saboda wasu dalilai da dama. Na farko, jam’iyyun adawa musamman jam’iyyar Democratic Alliance (DA) da Economic Freedom Fighters (EFF) sun samu damar kutsawa a wuraren da jam’iyyar dake mulki wato Africa National Congress ke da karfi. Abu na biyu shi ne, sakamakon zabe daga Kudu maso Yammacin Café da sauran wurare, a karo na farko ya nuna yi wa al’ummar hidima shi aka sa a gaba ba kabilanci ko jam’iyya ba. Wannan ya fito fili saboda yawan kuri’un da jam’iyyar DA ta samu daga bakaken fata, jam’iyyar da a tarihince fararen fata suka mamaye ta. Abu na uku shi ne irin yadda aka gudanar da kuma bayyana sakamakon karshe na zaben a dakin taro a bainar jama’a. Taron ya samu halartar Shugaban kasar ta Afurka ta Kudu wato Jacob Zuma tare da mataimakinsa da babban mai shari’a na kasar da sauran manyan baki.

Abin ban sha’awa Shugaban kasar ya gudanar da jawabinsa cikin natsuwa duk da cewa a dakin taron akwai wasu matasan ‘yan mata dake dauke da allunan dake nuna rashin goyon bayansa. Sai bayan da aka kammala taron ne sannan jami’an tsaro suka tarwatsa masu zanga-zangar. Taron ya nuna karara tsarin tafiyar da dimokuradiyya ba tare da tsangwama ko tursasawa wani ba.

Ba kamar irin tsarin da ake da shi a Nijeriya ba, inda matakan gwamnati uku da muke da su wato sashen zartarwa da ‘yan majalisa da kuma sashen shari’a dukkaninsu ke zaune a Babban Birnin Tarayya, a kasar Afurka ta Kudu abin ba haka yake ba. Mazaunin matakan gwamnati a Afurka ta Kudu na rarrabe ne a tsakanin garuruwa uku. |angaren zartarwa da suka hada da Shugaban kasa da sauran mambobin majalisar zartarwa na zaune ne a birnin Pretoria, sai bangaren majalisar dokoki da ke da mazauni a birnin Café Town yayin da bangaren shari’a da babbar kotun kasar ke garin Bloomfontein. Saboda haka wasu ke cewa, kasar na da babban birnin tarayya har guda uku, tsarin da ke da manufar tafiya da kowa da kowa.

Akwai wani abu muhimmi da ya kamata a yi bayani kan kasar Afurka ta Kudu, wato yadda al’umma kasar ke tafiyar da rayuwarsa a bisa bin doka da oda. A tsakanin daidaiku da daukacin al’ummar kasar, akwai da’a da kiyaye bin ka’ida da doka, abin da za ka fara gani tun da sauka a filin saukar jiragen sama. Mutum kan zagaya a cikin filin jirgi ba tare da wata matsala ba, ga ma’aikata nan tsaye a cikin natsuwa da za su taimaka wa mutum wajen daukar kayansa. Ba wuraren bincike masu batawa mutum lokaci. Irin wannan yanayin na kwanciyar hankali da rashin tsangwama kusan shi ne za ka tarar a dukkan wuraren gudanar da al’amurran rayuwa na yau da kullum a kasar Afurka ta Kudu. Mafi yawan lokuta mutane kan zauna tare da mike kafafunsu a wuraren hutawa. Amma kuma wannan ba yana nufin mutane sun shantake ba ga yin zanga-zanga cikin lumana da kuma nuna rashin gamsuwar idan har an yi wani abu da ba su aminta da shi ba.

Dokokin da suka shafi mallakar filaye da harshe ko yare da ake amfani da shi sun ci gaba da kasancewa abubuwa masu muhimmanci a kasar. Ba kamar Nijeriya ba da mafi yawancin filaye suna a matsayin mallakar gwamnati, abin ba haka yake ba a Afurka ta Kudu. Tsarin amfani da filaye a kasar ya samo asali ne lokacin da Boear (Mutanen Dutch) da turawan Birtaniya suka zo a gabar yammacin Afurka a lokuta daban-daban da suka wuce a wani dadadden tarihi. Mutanen Dutch sun fara isa garin Café Town a farkon shekarun 1662 yayin da Birtaniya suka zo daga baya a garin Natal a shekarar 1848 da gabar ruwa ta Elizabeth a shekarar 1920.

Bayan shekaru da dama na takaddama a tsakaninsu na wake da ikon mallakar wadannan wurare, daga karshe sun sasanta da dinke barakar dake tsakaninsu domin samarwa kansu mafita a yankin kudancin Afurka.

A wuraren shekarar 1910, sun hada kai ta kuma kaddamar da kungiya a Afurka ta Kudu wacce za ta yada al’adun mutanen Afurka. Ana amfani da Indiya da Malay wajen gudanar da ayyuka a kasar tun a wuraren shekarar 1860.

Bayanai sun nuna cewa an fito da tsarin wariya ne domin a zaunar da ‘yan kasa da Indiyawa da kuma Turawa a wurinsu daban, domin samar da cigaba a tsakaninsu dai-dai da tsarin rayuwa da al’ada da kuma addininsu.

An murkushe asalin ‘yan kasar ta hanyar amfani da karfin bindiga yayin da Turawa suka mallake gonaki da filayensu, wanda har yau din nan suke mallakar wadannan filaye da suka rarraba a tsakaninsu. Sun mallaki manyan ganduna da gonaki da suke kiwon dabbobi a ilahirin farfarjiyar gonakin. Abin da sam ba ka gani a Nijeriya.

Mallakar filaye a kasar na da alaka da arziki da kuma talauci, al’amarin dake bukatar taka-tsan-tsan. Kundin tsare-tsaren samar da ci gaba na kasar Afurka ta Kudu ya fahimci haka, shi ya sa aka fito da wani shiri da zai “magance dadadden mikin da wariya da kabilanci suka haddasa a karnuka da dama da suka wuce.”

Dukkanin kasashen biyu wato Nijeriya da Afurka ta Kudu sun fuskanci matsaloli kan wane yare ko harshen za a gudanar da harkokin gwamnati da shi. Ba kamar Nijeriya ba da gwamnati ta dauki yaren Ingilishi a matsayin yaren da aka aminta da shi wajen tafiyar al’amurran kasa, wanda hakan ya kawo koma baya ga harsunan asali na al’ummar kasa, a bangare daya kasar Afurka ta Kudu ta fifita yarukan Afurka akan sauran harsuna, kuma wannan ya kasance wani abin takaddama musamman a farfajiyar siyasar kasar. Bayan an dade ana kai ruwa rana tare da tayar da jijiyar wuya daga karshe kasar ta aminta da a rika koyarwa da harshen Ingilishi a makarantun kasar.

Bayan kaddamar da kungiyar hadin kai ta Afurka ta Kudu, an gudanar da zanga-zangar kin jinin fararen fata ta farko a shekarar 1952. Wannan gwagwarmayar ta ci gaba har zuwa shekarar 1994 lokacin da bakaken fata masu rinjaye suka karbi ragamar mulkin kasa lokacin Nelson Mandela ya zamo shugaban kasa. Kamar kundin tsarin mulkin Nijeriya, kundin tsarin mulki na Afurka ta Kudu na shekarar 1996 an samar da shi don hadin kai a tsakanin ‘yan kasa ba tare da nuna bambancin kabila, yare ko addini ba.

Kalubalen samar da tabbatar kasa mai hadin kai a tsakanin kabilu, wani abu ne da za ka iya samu a tsakanin kasashen biyu na Nijeriya da kasar Afurka ta Kudu. Abin tambaya a nan shi ne, a tsakanin kasashen biyu wace ce ke kokari tukuru na ganin ta samar da hadin kai a tsakanin al’ummarta, da samar da ababen more rayuwa da kuma habaka tattalin arziki? A ajiye kiddigar masana tattalin arziki a gefe, sannan a yi duba da idon basira a gano shin a tsakanin wadannan kasashen biyu masu karfin tattalin arziki wace ce ta fi? Wannan ita ce tambaya mai ma’ana da ya kamata a yi.

Bukar Usman, tsohon Babban Sakatare ne a Fadar Shugaban Kasa, a Abuja.