Taskar Tatsuniyoyi
Ba Sai Bahaushe Ne Ka]ai Zai Yi Kishin Hausa Ba – Dakta Bukar Usman
Daga Ashafa Murnai Barkiya, a Abuja
Duniya mai abin mamaki. Yayin da ake zargin mashahuran manazartan Hausa da manyan malaman Hausa a jami’o’i da cewa sun yi watsi daga yin ingantattun rubuce-rubucen litattafai, sai ga shi tauraron wani babban marubucin litattafan Turanci ya hasko bigiren al’ummar Hausawa, inda marubucin DAKTA BUKAR USMAN wanda ]an }abilar Babur ta jihar Barno ne, ya fara rubuce-rubucen litattafan Hausa. Ba wannan ne ka]ai abin mamaki dangane da marubucin ba. Baya ga cewa Hausa ba yaren sa ba ne, Bukar Usman gogaggen ma’aikaci ne wanda ya manyanta a mu}amid a kuma shekaru, domin tun cikin 1999 wa’adin kammala aikin sa ya cika, inda ya yi ritaya bayan ya yi aiki na shekaru talatin cif }ar}ashin gwamnatin tarayya, in ya yi ritaya a matsayin…
Wani abin burgewa dangene da ]abi’ar Bukar Usman ita ce, mai karatu zai yi tunani cewa gogaggen ]an book kamar sa babu inda zai tsoma }afar sa bayan ritaya sai gonar siyasa. Amma a maimakon haka, sai ya yanke shawarar fara rubuce-rubuce, na Turanci da kuma na Hausa. Abin sha’awa shi ne yadda dattijo kamar Bukar ya ]auki layin rubuta labarai na tatsuniyoyin da can, wa]anda ya ce ya yanke shawarar tattara su ne saboda ya ga zamananci na }o]arin shafe su a doron duniyar Hausawa. “Yawa yawan ‘ya’yan mu da jokokin mu a yanzu ba su san tatsuniyoyin da mu ka ri}a ji daga kakanni da iyayen mu ba, saboda tatsuniyoyin sun gushe yara sun koma kallon talbijin dare da rana.” Inji Bukar Usman.
Daga cikin litattafan Turanci da ya wallafa, akwai wani dan}arere mai suna VOCIE IN A CHOIR: An Issue in Democratasation and National Stability in Nigeria. Littafi ne da wannan tsohon ma’aikaci ya yi nazarin siyasar Nijeriya mai ]auke da shafuka 350. Shi ne ya rubuta ‘Hatching Hopes’ da kuma ‘The Hyena and the Squirrel’. A ~angaren litattfan Hausa kuwa, Bukar ya rubuta guda shida wa]anda duk littattafi ne na tatsuniyoyi da ya rarraba daga littafi na ]aya zuwa na shida. Akwai: ittafi na ]aya mai suna Marainiya, Jarumin Sarki (Da wasu labarai,) wanda shi ne littafi na biyu, sai littafi na uku mai suna Yarima Da Labbi (da wasu labarai), akwai nah u]u mai suna Tsurondi (Da wasu labarai). Littafi na biyar shi ne Sandar Arziki (Da wasu labarai), sai na shida mai suna [an Kutungayya (Da wasu labarai).
Ba su ka]ai kenan ba, koda yake dai su ka]ai ne su ka fara fitowa. Ina sauran? Yaushe za su fito? Ku karanta tattaunawar sa da ASHAFA MURNAI BARKIYA ku ji komai:
Mene ne tarihin Dakta Bukar Usman?
A ta}aice sai a ce an haife ni a }asar Barno. Bayan na yi makarantar firamare a can, sai na tafi Maiduguri na yi sakandare. Na je Kings College ta Legas, inda daga can na koma Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Na yi aiki a makarantar gwamnatin tarayya FGC da ke Bakori, to daga can ban duba bayana ba, sai na yi ritaya a shekarar 1999.
Lokacin da ka yi ritaya daga wane matakin mu}ami ne ka ke ri}e da shi a lokacin?
Na yi ritaya a matsayin Babban Sakatare (Permanent Secretary).
A wace ma’aikata?
Offishin Babban Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF)
Yanzu kusan ka na da shekara nawa kenan?
An haife ni a cikin 1942, kamar shekaru 66 kenan.
A jihar Barno kenan tun ta na ha]e da jihar Yobe. Mun san jihar ta na da }abilu fiye da ]aya, to kai ]an wace }abila ce daga cikin su?
Ni }abilar Babur ne.
Mutane za su yi mamaki, na farko kai ba Bahaushe ba, kuma ba Bafilatani ba, bare a ce Hausa/Fulani a ha]e, amma ga shi Allah ya ba ka fasaha ta rubutun Hausa. Shin dama can ka yi Hausar ne tun a farkon karatunka na firamare ko kuwa, ya abin yake?
Kamar yadda ka ce Allah ne ya ba ni fasahar yin Hausa ko in yi rubutu da Hausa, kuma na gaya maka nib a Bahaushe ba ne, amma na soma karatun boko da Hausa, irin litattafan su Alhaji Abubakar Imam, Mu {ara Karatu, irin su Runwan Bagaja da sauran su duk a lokacin ina karanta su. To daga lokacin abin ya ]aukar man hankali har na fara tunanin litattafan Hausa, saboda irin wa]annan takardun ana }arancin su da yawa, shi ya san a ce ni ma bari in duba ko na iya rubuta wani abu da Hausar Babur, amma zan ba mutane wa]anda za su iya su duba su ga dai ba irin Hausar da kamar shi Sardauna ya gaya wa Alhaji Ibrahim Kakaki da aka ba shi minister, sai ya ce “Ranka ya da]e Alhaji ya sa ka gaji ubanka.” Ka ga wannan Hausar ba ]aya ba ce, sai ya ce “a’a ga shi na baka mu}ami kuma ka na zagi na (raha) ta haka ya sa na }ara tunanin rubuta wani abu in ba mutane wa]anda su ke jin Hausa domin sun san Hausar zamani, wanda zai sa irin kurakuran da Kakaki ya yi gaban Sardauna wasu masu zuwa ba za su yi irin sa ba.
Akwai fannoni da yawa na rubuce-rubuce, kama daga na al’ada, na zamani, na tattalin arziki, da kuma rubuce-rubuce a kafafen ya]a labarai. To mutane za su yi mamaki babban mutum kamar ka ga shi ka dawo kusan }asa za’a ce ka zauna a cikin ajin }anana yara na firamare, ka na auna }wakwalwar ka ta wancan lokacin tare da us, to me ya sa ka za~i rubutu akan }anana yara da kuma tatsunniya?
A’a ka san dai na yi rubutu a cikin harshen Turanci, wannan ta fannin aikin gwamnati kenan, bayan na gama na tsaya na duba na ga mene ne zan iya yi ko ya kamata in yi, sai na ga abin da ya kamace ni, in yi rubutu saboda yawancin mu duk sun manta sai naga idan ba’a samu aka rubuta wasu ba, za’a wayi gari tatsunoyyin sai sun ~ata. Domin akwai lokacin da na tambayi wani ]alibin jami’a game da wata tatsunniya, amma ya kasa ba ni ita saboda bai santa ba. Don haka ni ke ]an bakin }o}arin na duk wasu tatsunoyoyi da na sani nike }o}arin rubuta su.
Kenan akwai tatsunoyoyin yarenku (Babur) da ka birkita su zuwa Hausa?
E, }warai akwai yawanci.
Kafin wannan ko ka san wasu tatsinniyoyin na Hausa?
E, sai dai wanda na karanta kamar wa]anda ke cikin littattafai irin su Ruwan Bagaja da sauran irinsu.
To wajen batun jirkita wani abu ya zuwa Hausa fa?
Kamar.
Kamar idan wani dodo ne ya na da sunansa, wajen juya shi sa zuwa Hausa ba ka sha wahala ba?
A’a ban sha wahala sosai ba, saboda na san wasu, amma wa]anda ban sani ba wa]anda su ka duba mani littafin don gyarawa su ke gyara mani. Ka san sashen Hausa na jami’ar Bayero ‘BUK’ ya taimaka mani }warai.
Idan ka duba zamani, za ka ga wa]annan tatsunoyoyi sun wuce, amma idan ka duba yadda ku ke }o}ari da }arfi aljihunku da tsawon lokaci da ku ka ~ata, ga shi kun a ta }o}arin ha~aka wannan al’ada. Shin abu na farko, ko me za ka ce game da danganta janyewar wa]annan tatsunoyoyi a cikin al’ummar Hausa, da kuma yadda yaran mu su ka raja’a game da kallon finafinan Hausa, da kuma abubuwa na zamani na kalle-kalle da kuma nisha]antarwa? Me za ka ce game da haka?
Ni dai na yi }o}arin na ce in na rubuta, don in ba ka rubuta ba, mutane ba su ga wani ba da za su iya fahimtar sa ba. Yawanci za ka ga litattafan da a ke kawowa duk na }asashen waje ne, don haka na ce bari in ]abba}a rubutun nawa, tun da su Abubakar Imam babu su yanzu, kuma ban ga wa]anda su ka rungumi hanyar su ba tarubu don har yanzu ban ga irin rubuce-rubucen da ina yaro ba. Shi ya sa na ce bari in yi irin nawa }o}arin tattaro abubuwan da na sani, kuma in mutane sun gani, wata}ila ka samu wani abu daga ciki da ka karanta ko? Ka ga in babu littafin ba za ka karanta komai ba. Kamar in ba a buga jarida ba, babu abin da mutun zai iya karantawa, saboda haka in na yi }o}ari na rubuta ina tsammani mutane za su samu abin karantawa.
To akwai wata magana da ake ta yi a yanzu cewa ]aya daga cikin matsalar da Bahaushe ke fama da ita, shi ne yadda ba ya girmama ko inganta abubuwan sa, kamar yadda aka wayi gari Turawa sun shigo sun a kwaikwayon tatsunnuyoyin mu su na fina-fina irin su Tom and Jerry da irin su atsabibin yaron nan na fina-finan Ingila wato Harry Potter. To idan ka kalla za ka ga su na da ala}a da tatsunonyoyin Hausa. Don haka wasu ke ganin don me a cikin mu Hausawa ba za’a samu wasu za}a}urai da za su ri}a shirya fim na tatsunniya da ta shafi gizo da }o}i?
E, bayan na rubuta ni zan yi }o}arin in ga masu zane-zane da wa]anda su ke wa]annan fina-finan wa}o}i da tatsunnuyoyi, wata}ila za su ]auka su yi. Amma gaskiya sa kai ne, in mutanen mu sun sa kansu, mu na da duk irin wa]annan da mutane su ke so. Lallai ka ce Turawa sun a zuwa sun a sace mana dabara, ka san cewa Ado Ahmad Gidan Dabino har Jamus ya je? Me ya sa shi zuwa, ka ga su ne suka kira shi domin neman irin abun da mu ke magana akai. Maimakon mu mu kira su, zo ka ga su ne suke kiranmu, Bahaushe fa yake zuwa can Jami’ar Jamus su kar~i irin wa]annan.
Kafin wa]annan littattafi na tatsuniyoyi da ka wallafa wanda kusan sun rabu zuwa gida shida, kafinsu ko akwai wasu littattafi da ka ta~a walafawa?
A’a, ban yi ba sai wa]annan guda shidda, amma akai-akai zan rubuta guda sha-hu]u duk na tatsunniya, wannan guda shida an buga a wannan sabuwar shekarar kafin nan da wata biyu ko uku guda takws za su fita.
Ka kan yi wata nawa, ko wane tsawon lokaci ne ka ke ]auka kafin ka }are littafi ]aya?
Na ]auka tun daga shekara 2005 za ka gani a cikin gabatarwa, ni ke rubuce-rubucen, amma wajen bugawa duk an buga su a lokaci guda. Shi ya sa ya zama kasha-kashi.
Kamar yadda ka yi magana duk ka fassara yawancin tatsuniyoyin daga yaren Babur, to ko a da mu mun san yawanci inda aka fi sauraren tatsunniya za ka ga gida ne inda yara su ke yawan shiga hira, a wajen tsoffi, iayaye ko sabbin amare, shin yallabai kai a gaban kakanninka ne ka tashi?
Ni na tashi a gaban uwaye na da kakanni na, musamman ma uwata, wadda yawancin wa]annan tatsunnoyyin daga wajenta na same su.
Mahaifiyar ka ita ce malamarka game da tatsunnuyoyi?
{warai kuwa, ita ce malama ta, kuma kamar yadda na fa]a a cikin littafin na tuntu~i mutane da yawa, na bi sawu na }ara.
To kamar ya za ka kwatanta irin wannan aikin na rubuta da kuma wanda ka yi n a gwamnati, ta wajen wahala da kuma ]auke hankali da sauransu?
Babu wahala don na yi ritaya a lokacin kuma da ni ke gwamnati ina rubuce-rubuce da yawa irin su taro in na zama sakatare dole in rubuta abin da aka tattauna, kusan ko wane mako sai na yi rubutu. Lokacin da na bar aikin gwamnati kawai na ci gaba da rubutuna, ina wasa }wa}alwa na ba na son kwanyata ta rufe.
Me ya hana ka shiga siyasa?
Ba ni da jininta, sam, na tashi da aikin gwamnati tun daga akawu (clerk) 1965. Amma ni ba na da sha’awar shiga siyasa a baya ko nan gaba sam ba ni da ra’ayi.
Yanzu na san sai da ka yi wani tunani, har ka yi tunanin za ka yi rubuce-rubuce akan tatsuniya wanda ka ke gani yara na wannan zamani sun a da }arancin ta. To banda wannan mene ne ka ke ganin karma matasa su ke da matsalar shi, musamman tafuskar ilimi, tun da ka na magana ne akan ilmi da sauransu?
Fannin ilimi yanzu idan so ne ina son mutane su koyi maganar Faransanci, don ma}wabtan mu da yawa duk renon Faranshi ne. Ka je Nija, ka je Ivory Coast, ka je Benin za ka ga ba a magana sai da Faransanci. Don haka ya kamata mutane su koyi harshen da kuma koyon kwanfuta, inji mai }wa}walwa.
To wannan rubutu ka yi shi ne don riba ko don taimaka wa yara ko kuma duka biyun?
Ti in riba ta zo mutum zai so, tunda na riga na yi ritaya, ammab a shi ne abin da ya sa ni yi ba, don a yanzu haka ma in mun sa farashi ba zai ishe mu ko ku]in biyan bugawa ba.
Ka yi tunanin za ka sake su ne a kasuwa ko ka na tunanin ha]a kanka da gwamnatocin jihhin Arewa don sa shi a cikin manhajar karatun su?
E, ya dangana ga kamfanin da ya wallafa shi ko bugawa, ni dai na rubuta, wanda ya buga kuma shi ne kamfanin Gidan Dabino a Kano, su ke da alhakin saida su, ni dai zan ji da]i in sun kai kasuwa.
Daga }arshe matan ka nawa, ‘ya’yan ka nawa?
Mata ta ]aya da ‘ya’ya uku.
To Allah ya taimaka.
Na gode sai an jima.
|