Ra’ayin Mutane

 

 “Allah ya kaimu makon goben,to amma su ma  manoman kansu sunada damuwa. Lokacin da muna  yara akwai burtalai (hanyan da dabbobi kan bi) da dama  amma yanzu babu ko daya. Saboda haka in ana son magance wannan bala’i a samu burtali.”- Umar Buni“Assalamu alaikum, Malam, Allah Ya kyauta!” – Prof. Ismaila A. Tsiga

“Thanks Alangubro for the posts. They are all good and enlightening.” – Prof. Isa Mshelgaru

“Allah ya biya, Ya kara basira.” – Muhammad Abubakar Zabi

“Barka da rana Sir.  Na karanta wannan bincike kuma ya amfanar da ni sosai. Na gode. A huta lafiya.” – Khalid lmam

“Malam Usman, Salam. Na gode da aiko min da wannan takarda. Na yarda da cewa samun wurin makiyaya na musamman zai taimaka mana a wajen kauda wadannan matsaloli. Allaah ya bamu sa’a.” – Malam Aminu Dorayi

“Alanguburo Dr. Again Barka da Sallah. Allah Shi kaimu Sallah na badi lafiya da saa da nasara da alkhairai. Above is interesting and awakening. Waiting for the continuation.

Thank you very much. Greetings to the family.” – Musa Kachalla Biu Alhaji

“Salam alykm. Ranka ya Dade barka  da safiya da fatan an yi sallah lafia. Ina godia kwarai da gaske da irin gudummuwar da kake ba da wa wajen ci gaban harshe da al’adun Hausawa. Ubangiji Allah ya saka da alkhairi, amin. Muna godia matuka.” – Dalibarku Zaliat Ammani

________________________

“Assalamu alaikum Baba. Da fatan kun tashi lafiya, Allah yasa haka Ameen ya Rabbi. Baba nine Aliyu Abba Mohammed Tafida, na samu sako wajen Usman, sun turo mani N75,000 na gode. Allah ya saka da Alheri. Allah ya kara bude, Allah ya kara lafiya da wadata. Baba a gaskiya tunda Babana Allah yayi mar rasuwa babu wanda ya kula dani don yanzu ba ni da wani Baba da ya wuce kai. Baba Allah ya ja nisan kwana ya kara lafiya nagode, nagode, nagode. Abinda ka yi mani Allah ya biya ka. Taimakon da kake yi wa marayu Allah kadai ya san irin ladan da zai baka abinda ka sa a gaba. Allah ya amsa adu’armu Ameen ya Rabbi. Ka huta lafiya Baba. Bissalam jazzakhallahu khairan.”  – Aliyu Abba Mohammed Tafida

“As salama alaikum Dokta! A cikin farin ciki da murna nake rubutu muku wannan wasika, don kuma in gaya muku da yanzu abokin aikina Salisu Hamisu ya yi mini albishir da alkhairin dubu 50 na naira da kuka turo mini. Nagode. Nagode. Nagode! Allah ya biya ku da alkhairinsa.

“Dama, jiya da nake sauraren shirinmu, sai na ji wani bangare da ku ke kira ga duk wani da yake wani aiki, da ya kokarta ya rubutu wani abu a kai don na gaba kafin ya bar duniya. Sai nake ce ma wani abokin aiki wannan shi ne dalilina na rubutu littafi a kan aikin jarida. Yanzu haka yana Gidan Dabino don bugawa, kuma tabbas wannan kyauta taku ta shiga ciki, sunnanku zai bayyana karara, bisa kan shawarar da ku ka bayar har ni samu kuzarin shiga bincike da rubutu littafin (jagoran aikin jarida). Ina godiya matuka, don hausata kasassa ce, ban san wace kalma ce ma fi daidaita, wadda zan amfani da ita in gode muku ba. Allah ya jikan mahaifanku, ya kuma kara muku arziki da koshin lafiya da tsawon kwanaki. Amin summah amin.” – Sule Maje Rejeto

“Assalamu alaikum! Ina wuni Sir? Naji labarin foundation naka da kuke taimaka wa mutane. Sir, nima ina so a taimaka dan Allah. Ka taimaka min da jarin sana’a duk wanda, Allah yasa ka bani ni mai godiya. Ni ‘yar Biu ce amma ina zama a Kaduna. Mamata ‘yar Biu ce tana da zama a wace Prison kusa da gidan Alh. Modu Chos mai rasuwa (Allah ya jikan rai amen). Ni marainiya ce kuma na rabu da mijina sakamakon wulakantani da yayi. Na sha wahala sosai a rayuwata Sir. Na haifu yara biyu amma dayan ya rasu dayar kuma ni nake dawainiya da ita kuma ga nawa dawainiya. Ba mai taimaka min sai Allah. Wataran harda yunwa nake kwana. Nata neman aiki amma Allah bai sa na samu ba sai na ji labarin foundation naka kana da taimakon mutane. Shi ne nake neman taimako dan Allah ka taimakeni don ‘yata ta samu ta yi karatu, nima in dinka biyama kaina matsalolina harma in future in taimaka wa wasu. Wallahi Sir, kudin haya da nake cikin karshen watannan zan biya, ga rashin abin da zamuci, ga ‘yata ba lafiya, ga mijina ya cutar dani. Shi ya sa na nemi gidan haya (one bed room flat) na zauna ni da ‘yata. Daman a Kaduna na yi aure. Ina shan wuya sosai dan Allah ka rufa min asiri kamar yadda Allah ya rufa maka. Na yi karatu ba mai nisa ba. Ina da NCE. Naso inyi karatun degree amma ba mai taimako. Daga gareni Hauwa zuwa ga Dr. Bukar Usman Foundation. Nagode.” – Hauwa Bello Gora

Malama Hauwa.

Ina fata kina lafiya. Kamar yadda muka yi magana, ina shaida miki cewa gidauniyar Dakta Bukar Usman za ta duba kukan da kika yi saboda ta taimaka miki gwargwadon abinda akwai. Kuma lallai yakamata ki kimtsa sosai wajen rayuwa kuma ki lura da baiwar da Allah ya yi miki. Karatun da kika yi har zuwa ga samun takardar shaida ta NCE ba karamar nasara ba kuma bai hanaki kokarin samun hanyar rayuwa ta yin wata sana’a ba. Allah ya kiyaye miki hanya tafiyar komawa Kaduna daga Biu – Dakta Bukar Usman