Sharhi da Tsakure daga Littafin Kundin Hirarrakin Bukar Usman (1)

Daga

Bashir Yahuza Malumfashi

 

Sunan Littafi: Kundin Hirarrakin Bukar Usman

Sunan Marubuci: Khalid Imam

Kamfanin Wallafa: Whetstone Arts, Kano

Shekarar Wallafa: 2018

Yawan Shafuka: 366

 

 
   

Tarihin abin da ya faru a jiya, shi ke wanzar da abin da ke faruwa a yau, kamar kuma yadda yake daidaita ko saita abin da ka iya faruwa gobe. Bisa mizanin wannan magana da ta gabata na xora qunshiyar wannan littafi da nake wa nazari a yau, mai taken ‘Kundin Hirarrakin Bukar Usman’ littafin da ke qunshe da ingantattun hirarraki masu yawa da kafofin watsa labarai daban-daban suka gudanar da fitaccen marubuci, shahararren ma’aikacin gwamnati, masanin harkokin tsaro, Dokta Bukar Usman OON. Hirarrakin da suka qunshi al’amura da dama na rayuwar al’ummar Najeriya ta wata fuskar da kuma rayuwar al’ummar duniya ma gaba xaya a wata fuskar. Hirarrakin da suka qunshi al’amuran ilimi, tsaro, adabi da sauransu. Hirarraki ne da suka wanzu na tsawon shekaru 20 da xoriya.

     An kasa qunshiyar littafin nan zuwa gida uku, baya ga shafukan gabatarwa (daga shafi na 5 zuwa na 26) da suka qunshi Sadaukarwa, Tarihin Marubuci Khalid Imam, Taqaitaccen Tarihin Dokta Bukar Usman, Godiya, Muqaddima, Gabatarwa da kuma Ta’aliqi.

     Kashi na xaya na littafin (daga shafi na 27 zuwa na 155), ya qunshi hirarraki guda 15 da wasu jaridu da mujallu na Hausa da na Ingilishi da suka haxa da Daily Trust, Aminiya, New Nigerian, The Guardian, The Sun, ThisDay, The Punch, Daily Independent, Blueprint, Platform, Muryar Arewa, Leadership Hausa, Fim, Nigerian Pilot da kuma Nigerian Tribune.

     Kashi na biyu na littafin (daga shafi na 157 zuwa na 325) ya qunshi hirarraki ne daban-daban da wasu gidajen rediyo da talabijin, na gida Najeriya da na qasashen waje suka gudanar da shi Dokta Bukar Usman a lokuta daban-daban. Waxannan kuwa sun haxa da Gidan Rediyon BBC Hausa, Gidan Rediyon Faransa (RFI), Gidan Rediyon Najeriya (FRCN), Gidan Rediyon Kano, Gidan Rediyo da Talabijin na Borno (BRTV), Gidan rediyo Altenative na Jamhuriyar Nijar, Gidan Rediyon Freedom Kano da kuma Gidan Rediyon RayPower na Kano.

Sharhi:

 
   >>> Littattafai