ADABI LALE DA TASKAR ADABIN BAKA TASKAR TATSUNIYOYI NA DR. BUKAR USMAN DAGA: SANI MAIKATANGA DA IBRAHIM MUSA GIGINYU
Tabbas a wanan zamanin da’irar adana adabin baka na cikin wani hali na takaici da ban tausayi musamman idan aka dubi yadda marubuta na wannan zamanin suka karkata alkalumansu zuwa wata alkiblar da suke ganin anan lagwada ta yi zango. To amma kasan ba duk aka taru aka zama daya ba, domin da’rar adana adabin bakan ta samu wani bawan Allah wanda za’a iya cewa rabon da wannan da’irar ta yi irin wannan kamun tun zamanin su farfesa Ibrahim Yaro Yahaya da sauran su. Dakta Bukar Usman haifaffen garin Biu ne a can Jahar Borno Najeriya. Daktan da shekara sittin da bakwai a duniya (67) Ya shigo harkar rubutune saboda kishin alkinta adabin baka da yake da shi. Ganin cewa mafi kasarin yaran wannan zamanin sun kasance suna da karancin sani game da irin al’adun su sakamakon barin turbar adabin baka da ga tushe da aka yi. Daktan ya ce, “ada da zarar an ce almuru ya karato to sai ka tarad da duk inda yaro yake tunaninsa na gurin shin yau wacce tatsuniya Baba ko Kaka ko Goggo zata bayar. Sabanin yadda a yanzu kalle-kallen zamani suka fi tasiri a rayuwar yaran wannan zamanin. Wannan maganar haka take, domin a wannan lokacin wannan mahallli da yara ke zama don sauraron wannan tatsuniyar makaranta ce ta farko da ake koyon karatun ilimin zaman duniya. Kowa ya san ma’anar tatsuniya, wato labari ne wanda ke dauke da wasu halaye na gari da hanyoyin dabarun warware wasu matsaloli na rayuwa da kuma yin ishara game da wasu abubuwa da sukan faru ga, masu aikata munanan halaye. Hakan shi ke koyar da kwadayin son zama mutum na gari da kuma kyamar zama mutumin kawai idan an girma. Saboda muhimmancin wannan makarantar da kuma irin yadda wannan makarantar ta kasance zamani na neman kawad da ita kwatakwata, shi ya sa Dakta Bukar Usman ya ga ya dace da ya shigo wannan harkar don kawowa wannan fanning dauki. Kamar yadda Dakta Bukar Usman ya shaida mana a wata tattaunawa da muka yi da shi a Birnin Kano lokacin da ya bakunci birnin na Kano don halartar bikin kaddamar da wani littafi na farfesa Sa’idu Muhammad Gusau, Daktan ya ce, “Ya dade yana nazarin hanyar da zai bi don ganin cewa adabin baka bai subucewa yaran wannan zamani ba. Ganin yadda shi kansa ya sharbi romon adabin baka a lokacin yana dalibta daga rubuce-rubucen adabin baka da marubuta na baya suka samar. To amma sai ga shi irin wadannan rubuce-rubucen sun yi karanci a wannan zamanin. Dalilin da ya sa Dakta Bukar ya daura damarar samar da littattafai wadanda za su kasance sun taimaka wajen tattarawa da kuma alkinta adabin baka a wannan shiyyar ta Arewacin Kasar Najeriya da ma duniyar Hausawa. Daktan Bukar Usman wanda yayi karatun sa na Jami’a share fagen shiga a babbar makaranta nan dake can Jahar Ikkon Najeriya wato King’s College, wadda daga nan ne ya yi karatunsa na jami’a a Jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria, inda ya kamala digiri a fanning tafiyar da mulki da hulda da kasashen waje a shekara ta 1969. Dakta Bukar Usman ya yi aiki a Gwamnatin Tarayya ta Najeriya a inda hakurinsa da juriyarsa suka kaishi ga kaiwa matakin mukamin Babban Sakatare (Permanent Secretary) a Ofishin Shugaban Kasa, wato “Presidency”. Dakta Bukar Usman ya bar aikin Gwamnati a shekara ta 1999. Masu Magana na cewa “yaba kyauta tukuici”, saboda irin jajircewa da bin doka da ka’ida bisa aiki da kuma irin yadda ya tafiyar da ma’amulolinsa a lokacin da yake aikin gwamnati da kuma bayan ya bari, Gwamnatin Kasar Najeriya ta ga cewar ya dace da ta bawa shi Dakta Bukar Lambar Yabo ta Kasa’ta OON a shekarar 2000, wani yunkuri na cewa Dakta Bukar Usman mun gode da wannan aiki na alkhairi. Dakta Bukar Usman ya fara rubuce-rubucen sa ne da harshen Turanci kuma ya yi rubutu da harshen na Turanci da dama tun cikin 1992. Littattafan na Turancin sune:- Voices in a choir – issues in democratization and national stability in Nigeria. Hatching Hopes-Autobiography Bride Without Scars The Stick of Fortune Girls in Search of Husbands The Hyena and the Squirrel Press Policy and Responsibility Na rubuta littattafai guda goma sha hudu na Hausa a wannan fanning na adabin baka masu taken Taskar Tatsuniyoyi na daya zuwa shida a halin yanzu suna kasuwa tuntuni. Na bakwai zuwa na goma sha hudu da yardar Allah za su fito nan ba da dadewa ba, domin na riga na gama aikinsu tuni. Ta bakin Daktan kenan. Littattafan da dai suka riga suka fito kasuwa cikin jerin taskar tatsuniyoyi na Bukar Usman sune:- Marainiya (da wasu labarai) Jarumin Sarki (da wasu labarai) Yarima da Labbi (da wasu labarai) Tsurondi (da wasu labarai) SandarArziki (da wasu labarai) Dankutungayya (da wasu labarai) Marubucin wadda ya fara rubuce-rubucen Hausa a shekarar 2005, kusan a iya cewa ya fito da wani sabon tsari a yanayin littattafan nasa, da yadda duk karshen labari zaka ga an fidda irin.darussan da wannan labarin ke koyarwa. Haka zalika duk littattafan guda shida kamfanin Gidan Dabino Publishers ne suka buga su. Da muka tambayi marubucin ko me yasa hakkan sai ya ce da mu: “Nayi amana da Kwarewar wannan kamfani kan aikin talifi, kuma ga shi shugaban wannan kamfanin shahararsa a fannin rubuce-rubucen Hausa ba inda ba ta kai ba. Saboda irin kwadayin da nake dashi na yin aiki mai ingani shi ya sa naga ba inda ya dace ace anyi aikin tailfin littattafannan nawa illa Gidan Dabino Publishers.” Dadin dadawa, marubucin ya bayyana mana aniyarsa na samar da wani nau’in littattafai na adabin baka na Hausa na zana wato abin nan da ake kira da turanci “Cartoon”, wanda a ke ganin dan zane da kuma bayanin zanen don samun fahimta ingantacciya ga makaranci. Tabbas kowa ya ga irin aikin da Dakta Bukar Usman ya aiwatar, zai fuskanci cewa, ba wargi cikin al’amuransa. Haka zalika ya bfirowa da fannain adabi wato matashiya da zata zamewa wannan fannin kurangar kaiwa ga samun dorewar wanzuwar adabin haka a rayuwar al’ummar Hausawa. Ta yadda dabi’u na gari, wayon zaman duniya da sauran al’amuran da za su tabbatar da samun nagartacciyar al’umma, za’a koye su tun daga tushe. Kuma magana ta gaskiya ita ce, in son samu ne gwamnatocin jihohin Arewacin Najeriya su shigar da wadannan littattafai cikin mannajjar karatun firame karkashin shirin nan na samar da ilimi tun daga tushe wato “Universal Basic Education.” Ba anan Dakta Bukar Usman ya tsaya ba kawai, Daktan ya samar da wata cibiyar taimakawa mabukata wacce a ke kira da suna “Dr. Bukar Usman Foundation.” Ita wannan cibiyar ta taimakawa mabukata na da babban ofishinta ne adireshi kamar haka: “Plot 637, Kwame Nkrumah Crescent, Asokoro District, Zone A4, Abuja. Da yake Karin bayani wannan cibiyar ta taimakawa mabukata Dakta Bukar ya ce, “Lokaci ya yi da ya kamata a ce mun fuskanci cewa ba komai gwamnati za ta iya yi wa jama’a ba, dole ne mutane daidaiku da kungiyoyi su tashi haikan wajen ganin cewa an samar da wani nau’l na taimakon juna hakan ne ya sa naga ya dace muka kafa wannan cibiyar. Wannan cibiyar a yanzu haka tana da membobi guda saba’in (70) da kuma kwamitin amintattu mutum goma.” Da muka tambayi Dakta ko ya za’a iya samun taimakon daga wannan cibiyar? Sai yace: “Za’a rubuto mana ne ta adireshin ofishinmu da ke Abuja, mu kuma zamu binciki wannan maganar, daga nan in mun gamsu, cikin ikon Allah za’a samu wannan taimakon.” Kamar yadda Dakta Bukar Usman ya shaida mana, cibiyar tana samun kudaden da take aikace-aikacenta ne ta irin kudaden da shi kansa a matsayinsa na shugaban cibiyar da sauran membobi ke tarawa musamman don wannan aiki na taimakon mabukata. Abin da zamu ce anan shi ne Dakta, Allah ya kara bidu amin. Ga mai bukatar taimakon wannan cibiyar, sai a rubuto zuwa ga babban ofishin cibiyar wato “Plot 637, Kwame Nkrumah Crescent, Asokoro District, Zone A4, Abuja.” |