Raya Adabin Hausa: Balaguron Marubuci zuwa Burkina Faso Daga Dokta Bukar Usman
A cikin Afirilun bana, Gidan Adana Kayan Tarihi na kasar Burkina Faso tare da hadin gwiwar Kungiyar Makaranta sun karrama marubuci Dokta Bukar Usman da kambin girmamawa, bisa la’akari da gudunmowarsa wajen bunkasa Adabin Hausa da kuma jaddada zaman lafiya tsakanin al’ummar Hausa da duniya baki daya. Bayan ya dawo, ya rubuta wannan tsaraba ga masu karatu, kamar haka:
Ita dai Kungiyar Makaranta, kungiya ce mai zaman kanta, wacce ba ta gwamnati ba kuma al’ummar Hausawa mazauna kasar Burkina Faso ce ta kafa ta a 2006, da nufin bunkasa al’adu, ilimi, zamantakewa, tattalin arziki da kuma harshen Hausa a kasar. Domin tabbatar da wannan kuduri nata, sai kungiyar ta shirya gagarumin biki, wanda ya hada da kalankuwa, baje kolin kayan gargajiya, babban taron masana daga ko’ina a duniya da kuma karrama wasu muhimman ‘yan Afrika da suka taimaka wajen bunkasa al’ummar Hausawa. Ina daya daga cikin wadanda aka zaba, domin karramawa. Haka kuma, ba yan ni kaina, an kuma zabi Sanata (Injiniya) Rabi’u Musa Kwankwaso, tsohon Gwamnan Jihar Kano.
Sanata Kwankwaso da ni kaina, mun halarci bikin a Babban Birnin Burkina Faso, Ouagadougou (Wagadugu). Ma’anar sunan birnin nan shi ne ‘Wurin da ake karrama da girmama mutane’ – babu shakka birnin ya ci sunansa, domin kuwa hakika ana girmama baki da daraja su. An karrama ni da kambi tare da takardar shaida mai taken ‘Jakadan Adabin Hausa.’
Wannan taro na kasa-da-kasa, an yi masa lakabi da “Gudunmowar Al’adun Hausa Wajen Wayar Da Kan Al’ummar Afirka.” Kasar Hausa ta yi fice wajen saka da rini da kira da jimar fata da ginin tukwane da sauran ayyukan fasaha da zayyana, wadanda ake sayarwa har wajen kasar ta Hausa. Harshen Hausa na daya daga cikin manyan harsunan duniya. Adabin Hausa na ci gaba da bunkasa, musamman ana samun rubuce-rubuce a fannoni da dama na ci gaban al’umma, duk kuwa da cewa akwai bukatar a rika amfani da na’urorin zamani tare da tsarin dauri wajen taskance harshen da al’adunsa domin amfanin gida da ma al’ummar duniya baki daya. An nuna sha’awar sanin ainahin sunayen da ake amfani da su a kasar Hausa, kafin zuwan Musulunci, sannan kuma aka nuna takaici da yadda yara kan gaza yin magana da harshen iyayensu.
A yayin bikin nunin kayan al’adun gargajiya na Hausa, wanda Ministan Al’adu Da Shakatawa na Burkina Faso, Mista Tahirou Barry ya bude, an baje kolin kayayyaki daban-daban, har ma da abincin gargajiya. Kayan sun hada da zayyane-zayyane da aka yi na fata, duwatsu, tabarmi da mafutai, kayan aikin noma, kayan girki da na cin abinci, korai, sakakkun suturu da kuma tukwane iri daban-daban da aka yi wa zayyana masu kyau. Haka kuma akwai ingantattun magungunan gargajiya da sake-saki, nama iri-iri da kayan sha na gargajiya daban-daban.
An sha kallo kuma an nishadantu da kade-kade da wake-waken gargajiya na Hausa, ga wasanni, musamman na kokowa da aka gudanar. Wasan kokowa na daya daga cikin wasanni masu tashe a kasar Burkina Faso. Tawagar karfafa kuma gwanayen kokowa daga Jamhuriyyar Nijar ta halarci bikin. A yayin da aka gudanar da tarukan kara wa juna ilimi a ranakun 14-16 na watan Afrilu, an ci gaba da baje kolin kayayyakin gargajiya, wanda zai dore har zuwa tsakiyar Yunin bana.
Zan iya tunawa, a lokacin da nake makarantar sakandare, a 1960, na samu labarin madaukakun Daulolin Mossi Dagomba da ke yankin Tsakiyar Afrika ta Yamma. A wannan zamani a yau, a Burkina Faso, irin wadannan dauloli da suka bunkasa, sun ci gaba da bunkasa har zuwa lokacin da Turawan mulkin mallaka na Faransa suka murkushe su a wajajen 1896. Wannan dalili ma na daga cikin dalilan da suka sanya na yi kwadayin ziyartar kasar, musamman domin in tantance wadannan kayatattun labarun da suka shafi kasa da al’ummomin Burkina Faso, kamar yadda aka gaya mana a can baya.
A sakamakon tsawon lokacin da na yi ina nazarin tsarin al’umma, na fahimta da cewa duk mai son ya fahimci tarihi da al’adun al’umma, zai iya samun ilimi mai yawa daga almara da tatsuniyoyinsu. Wannan ya sanya a lokacin da na sauka a birnin Wagadugu, tun ma kafin in sauka a masaukina na otel, sai na yi wa shagon sayar da littattafai tsinke, domin in samu littafin da ya yi bayani game da kasa da al’ummar Burkina Faso. Tabbas kuwa na ga littattafai da yawa da za su yi mani amfani, amma abin takaici, babu ko daya da aka rubuta da Ingilishi.
Na yi kokarin tambayar inda zan samu littattafan da nake nema, amma ban dace ba. Don haka sai na maida hankali ga intanet, inda na samu bayanai irin na kunne-ya-girmi-kaka. Na fahimta da cewa a kasar, manyan yarukan da ake amfani da su, su ne Moore da Djula da kuma Faransanci. Burkina Faso na da kabilu 63, cikinsu har da Fulani da Yarabawa da Ibo, tare da shugabanninsu.
Burkina Faso, wadda ke nufin ‘kasar mutane masu gaskiya’ tana da tarihi mai tsawo. Tarihinta ya faro ne tun 1896, lokacin da Faransa ta yi tunga a yankin a matsayin mallakinta. A 1904, Faransa ta mallaki kasar Upper Senegal da Yankin Nijar a Afrika ta Yamma, inda birnin Bamako ya kasance hedikwata. Daga bisani aka canja wa yankin suna zuwa French Upper Volta mai hedikwata a Wagadugu, a 1919. A shekarar 1932 aka rushe wannan tsari, aka karkasa kasashen zuwa Ivory Coast da Sudan da Nijar. An sake maida ta tsarin baya a 1947, inda aka dawo da yankin Upper Volta, aka mayar mata da iyakokinta. An ba ta mulkin kanta a 1958, sannan aka ba ta ‘yancin kai da sunan Jamhuriyyar Upper Volta a 1960.
Kamar dai yadda ta faru a Najeriya, sojoji sun tsoma hannunsu a mulkin Jamhuriyyar Upper Volta a 1966, inda gwamnatin ta soja ta kare a 1976. Sabuwar gwamnatin farar hula da ta gaji ta soja, an tunkude ta ita ma a 1980, inda sojan suka ci gaba da mulki zuwa 1983. Thomas Sankara da Blaise Campaore ne suka ci gaba da mulki a kakin soja kuma wannan gwamnatin ce ma ta canja wa kasar suna zuwa Burkina Faso a 1984. Bayan an yi wa Thomas Sankara kisan gilla a 1987, kasar ta samu natsuwar mulki a karkashin Shugaban Kasa Blaise Campaore na tsawon shekara 27. An matsa masa lamba, dole ya sauka daga mulki a 2014.
Tsohon sunan kasar na Upper Volta, an samo shi ne daga Koramar Volta, wacce ta hade har zuwa Kogin Atilantika, wanda ya ratsa har zuwa kasar Ghana a yanzu. Wani Baturen Fotugal ne ya rada mata sunan “Volta” domin ya yi la’akari da yadda ta yi ta kwana-kwana. Koramar tana da manyan bakuna uku, Farar Volta, Jar Volta da kuma Bakar Volta, wanda haka ke nuna launin kasar wuraren. Launin kasar Wagadugu ja ce kuma Jar Volta na Arewa Maso Yammacin Wagadugu.
Burkina Faso a yanzu haka tana da yawan mutane miliyan 20, inda Wagadugu ne Fadar Gwamnati, wanda ke kunshe da yawan mutane kimanin miliyan 2. Birnin Kasuwancin kasar, sunansa Bobo-Dioulasso, yawan al’ummarsa na kasa da miliyan daya ne kuma an yi kidayar jama’a ta karshe a 1982.
Mossi ita ce kabila mai mafi yawan mutane a kasar kuma suna da karin harshe kala biyu, Kompela da Tenkodogo. Mutanensu sun yi suna wajen hakuri da juriya, don haka Turawan Faransa suka rika daukar mazansu aikin soja, kuma aka rika ba su aikin gina hanyoyin jirgin kasa da na mota. Haka ma matansu, ba su da son jiki, suna da kokarin neman abinci. Ba su jin nauyi, domin za ka gan su suna tuka babur da motocin haya a babban birnin kasar. Suna yin noma, ban ruwa a fadamu, aikin buga bulo ko yin aikin siminti. An taba haramta auren mace fiye da daya a zamanin mulkin Sankara amma daga baya gwamnatin da ta gaje shi ta dawo da shi. Wannan ya sanya mutane da suke daraja al’ada suka rika auren mata da yawa. Duk macen da mijinta ya mutu, ba ta fita daga gidan aurenta, sai dai kawai ta zabi namiji daya daga dangin mijinta, ta sake aure.
Noma, shi ne babbar sana’ar mutanen kasar. Suna noma jar dawa da gyada, haka ma suna noma acca. Kamar Masar da Sudan, su ma Burkina Faso suna noma auduga mai yawa da suke sayarwa kasashen waje. Suna da ma’aidinan zinari da azurfa da sauransu, wadanda kasashen Australia da Afrika ta Kudu da Faransa da Japan da Ghana da sauransu ke amfana sosai ta hanyar hako su. Kasar tana dogaro da agajin kasashen waje ta bangaren tattalin arziki. Otel din Laico, wanda kuma ake kira da Hotel Libya shi ne kusan otel mafi inganci a Wagadugu. Marigayi Muamar Gaddafi ne ya gina shi kuma yana daya daga cikin abin alherin da ‘yan kasar ke tuna marigayin shi da shi. Wasu daga ciki wuraren bude ido a Wagadugu sun hada har da ‘Zauren Shahidai’ wanda yake kan hanyar Muamar Gaddafi. An gina shi ne domin tunawa da mutanen da aka rasa a hautsinin da ya faru a 2014.
Masu masaukina a kasar Burkina Faso, sun kasance tsatson Hausawa. Kakanninsu sun yo hijira ne daga Najeriya, musamman daga Kano, Sakkwato, Katsina, Kebbi da sauran biranen Arewa. Sun ce sun sauka a Upper Volta ne a matsayin ‘yan kasuwa, masaka, masunta, tun kafin zuwan Turawan Mulkin Mallaka na Faransa. Sun ce su ne ma tun farko suka fara kai sana’ar rini da sakar tufafi a kasar. Har zuwa yau kuwa, irin suturunsu ne ake alfahari da su a kasar.
Akwai al’ummar Hausawa da dama a biranen kasar Burkina Faso, suna zaune ne a unguwanninsu da ake wa lakabi ba Zango, sunan da aka samo a sanadiyyar kasuwancin da ya gudana shekaru masu yawa da suka shude, inda ‘yan kasuwa kan keta sahara daga wannan kasa zuwa waccan a kan rakuma. Wuraren da suke yada zango ne ake lakaba wa sunan unguwar ta Hausawa. A birnin Wagadugu, an canza wa Zango na ainahi matsuguni har sau biyu, domin kuwa ayyukan raya birnin ya shafe shi. Zango na farko yana kusa da tashar jirgin kasa, shi kuwa Zango na biyu, inda nan Hausawan suka zauna tsawon shekara 85, yana cikin kawyar birnin, nisan kilomita biyu daga Fadar Masarautar Moogo Naaba, Sarkin Gargajiyar Mossi; wanda suke da kyakkyawar mu’amala da shi. A 2001, Gwamnatin Blaise Campaore ce ta canza wa Zangon wuri zuwa inda yake yanzu, kusa da Fadar Shugaban Kasa.
Kalilan daga cikin Hausawa da suka yi karatun Boko, sun rike manyan mukamai a Ma’aikatun Gwamnatin Burkina Faso da sauran wurare har ma da wajen kasar. Daga bisani ne suka farga da muhimmancin ilimin zamani, inda suka kafa Kungiyar Makaranta, wacce ke taimakawa wajen fadakar da al’ummarsu, muhimmancin da ke tattare da ilimin na zamani.
Akwai abubuwa da yawa da mutum zai nazarta kuma ya karu a kasar Burkina Faso, duk kuwa da cewa karamar kasa ce da ba ta da yawan albarkatun kasa kamar wasu. Suna tafiyar da al’amuransu a kan tsari, ga su da bin doka da oda.
Moogo Naaba (Sarkin Duniya), shi ne lakanin Sarkin Gargajiya na Mossi da ke Wagadugu. Ana ba shi girma da daraja sosai. Kasancewar fadarsa na a babban birnin kasar, yana da martaba ta musamman, duk kuwa da cewa shi ne na hudu a tsarin martabar sarakuna a Daular Mossi ta Burkina Faso.
Tarihi ya nuna cewa Daular Mossi a Burkina Faso ta samo asali ne tun a Karni na 7. Kamar yadda tarihin ya tabbatar, Sarkin Gambaga na kabilar Dagomba a Arewacin Ghana, diya mace kawai ya haifa. Bayan ta yi aure, wata rana sai ta fita kilisa a doki, ta shiga daji kuma ta yi makuwa. Wani maharbi dan kasar Mali ya tsince ta kuma suka yi aure, suka haifi da namiji. Kasancewar a kan doki aka samu mahaifiyar jaririn, sai aka rada masa suna Ouedraogo (sunan namijin doki ke nan a Daular Mossi).
Shi Ouedraogo ne ya zama Sarki na farko a Daular Mossi kuma shi ne ya kafa Masarautar Tenkodogo. Sarkin Mossi na yanzu a Wagadugu, Naaba Booggo, shekararsa 34 ke nan a kan karaga. Shi ne sarki na 147 a jerin sarakunan daular. Masarautar tana daraja al’ada sosai, musamman akwai wata al’ada da har yanzu take wanzuwa. Kamar yadda sauran sarakunan kasar suka rika yi, duk Jumu’a, Naaba Booggo kan shiga sulke, ya hau doki da nufin tafiya yaki da wasu al’umma da ke Mali. Haka za a yi ta lallashinsa, ana ba shi hakuri, sannan ya sauko. Wannan shauki na yaki ya zama jiki a masarautar, duk Jumu’a.
Mai martaba Naaba Booggo ya amshi bakuncin mu mahalarta wannan muhimmin taro. Kafin mu kai ga ganawa da shi, sai da aka yi ta kai-komo wajen bin ka’idoji daban-daban amma duk da haka kwalliya ta biya kudin sabulu. Mutanen Burkina sun yi suna wajen hakuri, don haka sun dauka bakinsu ma haka ne. Sarkin na zaune a bisa karaga, tsakiyar butumbutumin zakoki biyu, hakoransu a bude, gwanin ban tsoro. Da yarensu ya yi mana jawabi, tafinta ya rika fassara mana. Ya yi mana jawabi ne game da rainon yara, inda ya nuna cewa zamani ya canja, don haka akwai bukatar dattawa su maida hankali wajen kyautata rainon yara, domin su tashi da da’a da biyayya, a matsayin ‘yan kasa nagari. Na fahimta da cewa, irin wannan sakon ne yake isarwa ga dukkan tawagar da ta ziyarci fadar tasa.
Domin kare martabar al’adun Masarautar Mossi, an haramta wa kowane mutum daukar hoton wani abu a fadar masarautar ba tare da izini ba. Sarkin dai ya karrama mu, inda ya amince muka dauki hoto da shi a wajen fadar. Akwai wani azancin magana da aka rubuta baro-baro a wata hasumiyar masarautar da harsuna uku na Moore da Djula da Fulatanci, kamar haka: “Duk inda ka ga dattijo, da wuya a aikata ba daidai ba a wurin.”
Naaba Booggo, dan kwallo ne. Babu mamaki, watakila shi ya sanya ma aka gina babban filin wasa na kasa kusa da fadar masarautarsa. Na samu bayanin cewa, shahararren dan kwallon nan na kasar Kamaru, Samuel Eto ne ya gina shingayen karfe da suka kewaye kofar fadar sarkin saboda nuna gamsuwa da yadda sarkin ke sha’awar wasan kwallon kafa.
Mun karu da wasu karin azancin magana a fadar Sarkin Hausawa a Zango. Kakakin Fadar ya ambata cewa: “Abu ne mai sauki ka ga makiyayi yana sarrafa garken shanu da sanda guda, a yayin da abu ne mai matukar wahala ka mulki jama’a kamar haka.” Wannan yana yi mana ishara da yadda mulki ke da wahala.
Taron kara wa juna sani da kuma bikin, kasancewarsu na kasa-da-kasa, an gayyaci mahalarta daga kasashen Benin, Kamaro, Afrika Ta Tsakiya, Chadi, Ghana, Nijar, Najeriya, Togo da kuma Sudan kuma dukkan wadannan kasashe, akwai al’ummar Hausawa da yawa. Taron ya samu halartar baki sosai, sai son barka, domin kuwa sarakunan gargajiya har uku suka zo daga kasar Togo kadai. Ba domin matsalolin sufuri da ke addabar nahiyar Afrika ba, da an samu mahalarta taron fiye da kima. Amma duk da haka, taron ya samu yabo daga mahalarta, a yayin da kasashen Togo da Senegal suka dauki alkawarin shirya irinsa a nan gaba.
Tafiya ta jirgin sama daga Abuja zuwa Wagadugu akwai wahala. An ba ni shawarar in shiga jirgi zuwa Kairo (Masar), ko kuma in bi ta wasu kasashen ma da ba na Afrika ba domin zuwa Wagadugu. Hanya mafi gajarta, ita ce ta Lome (Togo) ko Abdijan (Kwaddabuwa) kuma sai mutum ya kwana biyu a hanya. Matafiya daga Najeriya da suka biyo ta hanyar mota, sai da suka yi kwana uku, sun yada zango a Maradi da Yamai (Jamhuriyyar Nijar), sannan suka isa Wagadugu a rana ta ukun saboda jidalin bincike-binciken jami’an tsaro a iyakokin kasashen.
Kodayake duk da wannan jidalin, tafiya ta mota na tattare da nishadi, domin kuwa mutum zai karu sosai da sababbin abubuwa a hanya, na mutane iri-iri da kuma wurare. Ta fannin gane-gane a hanya kuwa, masu tafiya ta jirgi ma sun karu, domin kuwa mutum zai samu damar ganin falalen kasa, da itatuwa nan da can da hanyoyin kasa marasa kwalta da kuma gidaje warwatse, nan da can. Lallai akwai yalwar kasa, wacce ya kamata a aikata ta, domin ceto ta daga balbalcewa.
Na yi hira da wasu abokan tafiyata, wadanda suka bayyana abubuwan burgewa game da Najeriya. A jirgin da na shiga zuwa Abdijan zuwa Wagadugu, wani tsohon malamin Kwalejin Fourah Bay, Saliyo ya bayyana takaicinsa game da Najeriya. Ya bayyana yadda Allah Ya albarkaci Najeriya da albarkatun kasa amma saboda halin ko-in-kula na al’ummar kasar, an kasa amfana. Domin kawo gyara, ya ce ‘Najeriya na bukatar shugaba mai nuna karfa-karfa, amma ba mai zuciyar kisa ba.’
Haka kuma mun tattauna kan al’amuran da suka shafi ‘yancin dan Adam, musamman sakamakon yadda wasu mutum biyu suka rika cacar baki da juna. Daya daga cikinsu ma Bature ne. Wani mutum ne da ke zaune a bayan Baturen, yake ta magana a waya da karfi, shi ne Baturen ya kasa daurewa, ya shiga damuwa sosai, ya yi korafi. Shi kuma mai waya sai ya harzuka, ya maida masa martani mai kaushi, sai suka fara fada. Kafin ka ce kwabo, sai fadan ya girma har da zage-zagen juna, kowa na nuna cewa shi ke da gaskiya. Baturen ya roki ma’aikacin jirgin da ya sanya baki amma hakan ba ta samu ba. Haka suka ci gaba da cacar bakinsu, har suna cewa za su dambace, da zarar sun sauka daga jirgin.
Duk dai a cikin jirgin nan, wasu fasinjoji biyu, daya dattijo, daya kuma budurwa ce, su ma sun yi nasu wasan kwaikwayon. Dattijon ne yake ta buga kwamfutarsa (laptop) abinsa, sai ita kuma matar ta yi korafin cewa gwiwar hannunsa na tunkurinta. Shi kuma mutumin ya yi biris da ita. Haka abin ya ci gaba, ba a samu maslaha ba sai da matar ta canja wurin zama.
Babu shakka akwai darussa daga abubuwan nan da suka faru. Wani babban darasi daya a nan shi ne, a lokacin da mutum ke neman kare hakkinsa, yana da kyau ya yi la’akari da hakkin sauran mutane. Idan na kalli wadannan al’amura da suka faru a jirgi kuma na duba dalilin da ya sanya aka gayyace ni zuwa Burkina Faso domin a karrama ni, sai na fahimta da cewa a rayuwa muna bukatar mu kasance masu fahimtar juna, mu daraja ra’ayin juna a mu’amala, mu daraja al’adu da ra’ayoyin juna kuma mu yi iyaka kokarinmu wajen wanzar da zaman lafiya a tsakanin al’umma.
Dokta Bukar Usman, marubuci ne kuma tsohon Babban-Sakatare a Fadar Shugaban Kasa, yana zaune a Abuja.