Nazari Da Tsakure Daga Littafin Xankutungayya (Da Wasu Labarai) Daga Bashir Yahuza Malumfashi Sunan Littafi: Xankutungayya (Da Wasu Labarai) Marubuci: Bukar Usman Mawallafa: Gidan Dabino Publishers, Kano Shekarar Wallafa: 2005 Yawan Shafuka: 70 Farashi: Ba a faxa ba |
||
Littafin Xankutungayya (Da Wasu Labarai), kamar sauran guda biyar da muka yi wa sharhi a makonnin da suka gabata, shi ma yana xauke ne da tatsuniyoyi masu nishaxantarwa, ilimantarwa da kaifafa tunani. Haka kuma, littafin, xaya ne daga cikin jerin littattafai guda shida irinsa da marubucin ya rubuta a tsarin littattafan Taskar Tatsuniyoyi. Kafin mu tsakuro xaya daga cikin tatsuniyoyi goma sha biyu da ke cikin littafin nan, ya zama wajibi mu xan kawo bayani kaxan game da marucin littafin, domin kuwa Hausawa ma sun ce, a san mutum a san cinikinsa, ko kasuwa a san dillali… An haifi Dokta Bukar Usman ne a garin Biu na Jihar Borno, a ranar 10 ga watan Disamba na shekarar 1942. Bayan ya yi makarantar firamare a Biu, ya je Maiduguri inda ya yi karatun sakandare, kafin ya je King’s College da ke Legas, inda ya yi karatun share fagen shiga jami’a. Daga nan ya shiga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda ya samu digiri a fannin Dubarun Al’amuran Mulki Da Hulxa Da Qasashen Waje a shekarar 1969. Bayan Dokta Bukar Usman ya kammala karatun jami’a, sai ya kama aiki da Gwamnatin Tarayya, inda har ya kai muqamin Babban Sakatare a Ofishin Shugaban Qasa. Ya yi ritaya daga aikin gwamnati a shekarar 1999, inda saboda gamsuwa da aikinsa har Gwamnatin Tarayya ta ba shi lambar yabo ta qasa ta OON a shekarar 2000. Dokta Bukar Usman dai ya yi rubuce-rubuce da dama, mafi yawansu ma a cikin harshen Turanci, amma bayan ya yi ritaya ne ya tsunduma sosai cikin harkar rubuce-rubuce, inda har ya yi bincike ya rubuta waxannan littattafai guda shida na Taskar Tatsuniyoyi. Magidanci ne shi da ke zaune tare da iyalinsa a birnin Abuja. Dayake za mu yi tsakure ne daga cikin littafin nan, za mu xauki fitattar tatsuniyar nan ce ta Xankutungayya, wacce da ita ne aka yi amfani wajen sanya wa littafin suna. Tatsuniyar dai ta fito ne a cikin littafin daga shafi na 5 zuwa na 14. Idan mun shirya, ga tatsuniyar Xankutungayya: Ga ta nan, ga ta nanku: Akwai wani mutum da ke zaune a wani gari mai suna Raqumawa tare da matarsa da ‘ya’yansu su goma sha xaya. Rannan sai matarsa ta haifi xa namiji, ya zama na goma sha biyu. Da haihuwar yaro kuwa sai ya yi magana, ya ce wa uwarsa: “Kada ma a yi wahalar raxa mini suna, domin sunana Xankutungayya.” Ya qara da cewa, ragon sunansa ma kada a yanka, a bar masa ya rinqa hawa. Iyayen suka yi haka, jama’ar gari suna ta mamakin wannan yaro da abubuwan da ya yi. Ana nan, ana nan, sai wata rana yayyen Xankutungayya suka shirya za su gidan wata mata da suka saba zuwa gidanta hira da ‘ya’yanta su goma sha biyu. Sai Xankutungayya ya ce zai bi su amma babban wansu ya hana shi bin su. Amma ya bari sai da yayyen suka tafi, sai ya bi su a baya. Da isar su gidan, sai matar ta yi musu maraba; ta yi musu shimfixa, suka zauna; ta kawo musu abinci mai daxi suka ci, suka fara hira. Amma fa duk zuwan da suke yi gidan, ba su san cewa matar nan Dodanniya ce ba. Suka zauna suna ta hira kamar yadda suka saba kullum. Kuma duk sadda suka yi barci a gidan, Dodanniyar kan tashe su, su tafi gida. Ashe duk wannan dabara ce take yi don su saki jiki da ita, wata rana ta cinye su. Kuma tuni ta yi tanadin manyan tukwanen dafa su, ta sha romo. To, a daren da suka je tare da Xankutungayya ma, duk sauran sun yi barci in ban da shi. Can cikin dare sai ya ji ana wasa wuqa, sai ya ce a ransa: “A’a, lafiya kuwa?” Sai ya kwanta ya yi kamar yana barci. Da aka xan jima sai ya ga Dodanniya tana sanxa, har ta shiga wajen yara. Da ya ga lallai ta nufi yayyensa, sai ya yi tari da qarfi. Da ta ji tarinsa, sai ta koma da sauri. Da aka jima, sai ta sake dawowa; shi kuwa Xankutungayya ya qara yin tari, ta koma. A zuwanta na uku ne fa da ta ji tarin Xankutungayya, sai ta voye wuqa ta leqo ta ce: “Kai xan samari ba ka barci ne?” Sai ya ce: “Ai ni ba na barci in ba a kan rairayin qorama mai sanyi ba.” Da ta ji haka, sai ta xauki masaki ta tafi neman rairayin qorama. Kafin ta dawo sai Xankutungayya ya fito da wata ‘yar batta, ya buxe bakinta, ya zazzago wani magani, ya matsa kusa da wutar da ta hura, ya barbaxa maganin nan a cikin wutar, sai wani hayaqi ya tashi. Da ‘ya’yan Dodanniya da yayyensa suka shaqi wannan hayaqi, sai barcin da suke yi ya qara nauyi. Nan da nan Xankutungayya a cikin sauri irin na hatsabiban mutane ya bi ya tuve wa ‘ya’yan Dodanniya kayan jikinsu, ya sanya wa yayyensa. Kuma ya tuve wa yayyensa nasu kayan, ya sanya wa ‘ya’yan Dodanniya. Da ya gama wannan aiki sarai, sai ya kwanta, ya shiga jira. Can sai Dodanniya ta dawo, ta kawo rairayi ta ba Xankutungayya. Sai ya ce: “Yawwa Iya, na gode. Yanzu zan yi barci.” Da aka jima sai Dodanniya ta dawo da wata sharveviyar wuqarta a hannu, ta iske Xankutungayya ya yi barci. Nan da nan cikin gaggawa da qeta ta bi duk ‘ya’yanta ta yanke, tana zaton samarin da sukan je hira gidanta ne. Amma ba ta yanka Xankutungayya ba saboda ta ga shi qarami ne. Ta qyale shi, da nufin kiwata shi ya yi qiba. Da Dodanniya ta fita za ta fara shirin kwashe naman da take zato ta samu, sai Xankutungayya ya zaro battar nan tasa ya sake barbaxa garin maganin nasa a kan wuta. Kafin qifta ido, hayaqi ya murtuke xaki. Cikin gaggawa ya tashi yayyensa, ya gaya musu abin da ya faru, kuma ya ce su yi maza-maza su gudu gida. Ya ce shi zai bi su da gari ya waye, kada su jira shi. Take suka sulale, suka gudu. Da gari ya waye, sai Dodanniya ta zo za ta fara tattara waxanda ta yanka, a zatonta ‘yan uwan Xankutungayya ne. Yana ganin ta sai ya kaxa battarsa, sai ga ragonsa ya zo ya harari Dodanniya, yana yi mata kallon raini ya ce: “To, waxannan fa ‘ya’yanki ne kika yanka, ba ‘yan uwana ba.” Da ta lura da haka, sai ranta ya vaci ta yi wani qaraji, ta yi wuf ta kai masa bara za ta cafke shi, sai ya bauxe. Ta sake rarumo shi, amma sai ya xare bayan ragonsa. Rago kuwa kamar ya san zancen, sai ya kama sukuwa kamar walqiya, ya tsere mata fintinkau, ya bar ta sororo a cikin baqin ciki. Dodanniya ta xauko xan magurjinta na tsafi, ta bi ‘ya’yanta tana buga wa kowannensu a ka. Nan da nan namansu ya zama na tumakai, ta soye suka cinye ita da autarta. Daga nan ta yi alqawari sai ta rama qetar da Xankutungayya ya yi mata. Bayan ‘yan kwanaki, sai Dodanniya ta je bakin garin su Xankutungayya ta rikixe ta zama kanya kuma ta kwaza ‘ya’ya da yawa, har sun kusa nuna. Da yaran gari suka ga kanyar sai suka yi murna. Da ta nuna, sai wasu daga cikinsu suka dinga kaxo ‘ya’yan suna sha. Har dai wata rana yara da yawa suka hau kanta suna xiba. Da Dodanniya ta ga haka sai ta tashi sama da su, ba ta tsaya ba sai a gidanta. Nan da nan ta gaya wa autarta cewa nama ya samu. Sai ta umurce ta da ta wanke tukwane. Tana kuwa cikin wanke tukwane sai Xankutungayya ya ji labarin abin da ya faru, sai ya rikixa, ya zama xan maraqi, ya je gidan Dodanniya. Da zuwansa sai ya fara cin shuke-shuken da ke gidan, watau dai yana yi mata varna. Yana cikin wannan varna sai Dodanniya ta ce wa yaran da ta sato, su je su kori xan maraqin mai yi mata varna. Da ya ga sun doshe shi sai ya qi gudu, amma da suka zo dab da shi, sai ya xan gudu ya xan matsa gaba kaxan kuma ya ci gaba da varna. Yara kuma suka xan matsa kusa da shi, ya xan qara gaba kaxan. Haka dai ya dinga jan su, har sai da suka yi wa Dodanniya nisa. Sai ya rikixa ya zama mutum, ya ce da yaran nan su hanzarta su gudu. Ya jaddada musu cewa idan ba su gudu ba, Dodanniya za ta cinye su. Da suka ji haka, sai suka sheqa da gudu, suka koma garinsu, suka gaya wa iyayensu abin da ya faru. Shi kuwa Xankutungayya sai ya hau ragonsa, ya koma gidan Dodanniya. Da ya tabbatar ta gan shi, sai ya yi mata gwalo ya ce mata: “Na kuvutar da yara daga sharrinki, sun koma wurin iyayensu. Ni ne Xankutungayya na yi miki gayyar tawa, wadda ba za ki iya ramawa ba har abada.” Wannan abu da Xankutungayya ya yi wa Dodanniya da maganar da ya gaya mata, suka sa ta shiga tunani da qulla yadda za ta xauki fansa a kansa. Ana nan sai Dodanniya ta rikixa, ta zama mace kyakkyawar gaske, ta xauki wani adudu ta je cin kasuwa. Masoya suka yi ca a kanta, kowa yana so ya aure ta amma ta ce ba wanda za ta aura sai wanda ya buxe wannan adudun. Samari da yawa suka gwada amma duk suka kasa. Bayan ‘yan kwanaki, har samari sun fid da rai, sai xaya daga cikin yayyen Xankutungayya ya ji labari, ya bincika inda take a kasuwa ya je kuma ya gan ta, sai ya ji yana son ta. Ita kuma Dodanniya ta gane shi, saboda haka sai ta yi tsafi ta yadda idan ya gwada buxe adudun zai buxe. Da zuwansa kuma ya gwada sai adudun ya buxe, mutane suka yi ta mamaki, shi kuma ya yi murnar samun kyakkyawar mata. Aka xaura aure, ba ta jima ba ta tare a gidansa. Amma bayan ‘yan kwanaki sai ta qwaqwale wa mijin ido xaya, ta tafi da shi ta bar shi da jinya. Xankutungayya da jin wannan aika-aikar, ya tabbatar da cewa Dodanniya ce. Don haka ya quduri aniyar sai ya xauko fansar abin da ta yi wa yayansa. Sai ya rikixa ya zama Bafilatana, ya xauki nono, ya je gidanta talla. Da isar sa sai autar Dodanniya ta fito ta saya. Shi kuma ya yi mata araha. Kullum sai ya kai tallar nono, Dodanniya ba ta gane gogan ne ba. Da haka har Dodanniya ta saba da Bafilatana qwarai da gaske. Wata rana sai Bafilatana, watau Xankutungayya ya zo gidan Dodanniya a fusace. Dodanniya ta tambayi Bafilatana dalilin fushinta, sai ta ce: “Wani mutum wai shi Xankumale yake zuwa yana kashe mana shanu. Ga shi yanzu duk sun kusa qarewa.” Dodanniya ta ce: “Ke ba sunansa Xankumale ba, sunansa Xankutungayya. Mugun mutum ne. Ba shanunku kaxai ba, ku kanku ma ku yi hankali da shi. Ni ‘ya’yana goma sha xaya ya sa na kashe. Kwanan nan ma na kusa makantar da xan uwansa. Kin ga idon yayansa da na qwaqule.” Sai Bafilatana ta ce: “Tir da ganin idon lalatacce.” Sai Dodanniya ta ce: “Yau saura kwana uku ma in ba kyanwata idon mugun ta cinye.” Bafilatana ta ce: “Kash, da idon nan zai yi wa qanena daidai da kin ba ni shi. Shekaranjiya saniya ta harbi idonsa xaya ya fashe ya tsiyaye.” Cikin xoki da qeta Dodanniya ta ce: “Af, don wannan ai sai in ba ki.” Da jin haka sai Bafilatana ta yi farat ta ce: “Ai ko na gode.” Dodanniya ta qara yiwa Bafilatana gwaninta, sai ta gaya mata yadda za ta sa masa idon, ta ce: “A nemo qwayayen kifi guda bakwai da hantar baqin kare da kiyashi guda bakwai da kaucin marke; a shanya su bushe, sai a niqa, a rinqa sa masa a gurbin idon har kwana uku. A rana ta huxu sai a sa idon, zai zauna daram.” Bafilatana, watau Xankutungayya ta amshi ido, ta yi godiya. Da ta gusa kaxan sai ta tuve kayan Fulani, sai ga Xankutungayya ya bayyana. Sai ya yi wa Dodanniya gwalo ya ce: “Kin ga ni ne Xankutungayya.” Sai ya yi wani hatsabibanci ya vata, Dodanniya ta daina ganinsa. Bai tsaya a ko’ina ba sai gida. Da ya isa ya yi yadda Dodanniya ta kwatanta masa, idon yayansa kuma ya zauna daram, kamar ba a tava qwaqule shi ba. Rannan kuma sai Dodanniya ta rikixa ta zama kyanwa. Ta kama hanya ba ta tsaya ko’ina ba sai gidan su Xankutungayya. Da shigarta sai ta iske shi yana barci, sai ta lavava, har ta kai kusa da shimfixarsa. Sai ta yi wani karatu irin na tsafinta, ta tofa masa a fuska, sai ya zama vera, sai ta xauke shi ta kai gidanta, ta sa shi a quryar xaki. Daga nan ta yi masa wani tofin, ya koma mutum. Ita kuma ta rikixa ta zama mutum, sai ta harare shi, fuskarta murtuk, tana cike da fushi, ta ce: “Xankutungayya, yau fa ga ni ga ka, qaryarka ta qare.” Xankutungayya bai tsorata ba kuma bai ce mata komai ba. Can da Dodanniya ta xan huta sai ta sa autarta tsaron Xankutungayya; ita kuma ta kama hanyar kasuwa sayen kayan yaji wanda za ta dafa shi da shi. Tafiyarta ke da wuya sai Xankutungayya ya yi wa ‘yar auta dabara, ya karve kayan jikinta ya sa, ita kuma ya sanya mata nasa. Can sai ya ji motsin Dodanniya ta dawo, ya zabura, ya tarye ta yana kwaikwayon maganar ‘yar auta, yana yi mata maraba. Bayan wani xan lokaci kuma sai ga ‘yar a cikin kayan Xankutungayya tana yi mata maraba. Sai Xankutungayya ya dubi Dodanniya ya ce mata: “Ga munafukin nan Xankutungayya yana nunawa wai shi ne ni ‘yar autarki har da cewa, ‘Sannu da zuwa inna.’ Yau dai qaryarsa ta qare.” Sai Dodanniya ta ce: “Lallai kam, bar ni da lalatacce!” Nan take ta yi wuf ta shaqo ‘yarta, ta sa wuqa ta yanka. Tana gama yanka autarta sai Xankutungayya ya buga tsalle gefe, ya kwance zannuwan da ya xaura, ya dubi Dodanniyar nan ya ce: “‘Yar auta kika yanka, ni ko ni ne Xankutungayya gwanin gayya. Na yi miki gayyar tawa!” Yana gama faxa mata haka sai ya yi wal, ya vace. Dodanniya ta kama ‘yarta ta tuve kayan jikinta, sai ta ga lallai kuwa autarta ce ta yanka. Nan take sai ta haxiyi zuciya ta mutu. Qurunqus! Qarshen wannan tatsuniya ke nan, kuma tana xauke da darussa kamar haka: Qaunar juna da son ‘yan uwa kan qara wa juna danqon zumunci, kuma ya kuvutar da su daga duk wani sharrin maqetaci, kamar dai yadda Xankutungayya da ‘yan uwansa suka tsira daga Dodanniya. Haka kuma, tatsuniyar nan ta fassara mana karin maganar nan da ke cewa, mugunta fitsarin faqo ce, wanda ya yi ta take koma mawa.
Littafin Sandar Arziki (Da Wasu Labarai) A Mahangar NazariDaga Bashir Yahuza Malumfashi
Sunan Littafi: Sandar Arziki (Da Wasu Labarai)Marubuci: Bukar UsmanMawallafa: Gidan Dabino Publishers, KanoShekarar Wallafa: 2005Yawan Shafuka: 65Farashi: Ba a faxa ba
Littafin Sandar Arziki yana xauke ne da ingantattu kuma daxaxan tatsuniyoyi har guda tara, waxanda aka karkasa zuwa babi tara. Haka kuma, wannan littafi ya kasance xaya daga cikin jerin littattafai irinsa guda shida da ke qunshe a Taskar Tatsuniyoyi da Dokta Bukar Usman ya rubuta.Daga shafi na 5 zuwa na 65, littafin na qunshe da waxannan tatsuniyoyi: Tatsuniyar Sandar Arziki, tana xauke ne da labarin wani yaro mai ladabi da biyayya ga iyayensa, wanda haka ya sanya ya samu arziki da alherai masu yawa. Tatsuniyar na koya wa al’umma muhimmancin biyayya ga iyaye. Tatsuniya ta biyu ita ce ta Umbagila Da Dodo, inda wata yarinya ta kasance mai kunnen qashi, wacce ba ta jin maganar iyayenta, inda daga qarshe ta jawo wa kanta masifar auren dodo. Tatsuniyar na koya wa al’umma illar rashin bin maganar iyaye.Tatsuniya ta uku kuwa, ita ce ta Makauniya Da Xanta, inda ake ba da labarin wata makauniya da xanta guda xaya, wacce ta raine shi cikin kulawa sosai. Tatsuniyar na koya mana muhimmancin gaskiya da riqon amana a vangare xaya, sannan kuma take koya mana illolin da ke tattare da hassada da ganin qyashi. Tatsuniya ta huxu kuwa, ta Sarkin Maqera Da Dodo, tana xauke da abubuwan mamaki da kuma ban tsoro. Tana koya mana muhimmancin jaruntaka, haquri da juriya. Tatsuniya ta biyar, wacce ta kasance ‘Yar Mowa Da ‘Yar Bora; tana ba da labarin wasu ‘yan mata biyu ne ‘yan gida xaya, inda kishiyar xaya ta riqa matsanta wa xaya yarinyar da ba xiyarta ba, ta maida ta bora, amma daga qarshe ta samu arziki mai yawa. Daga qarshe dai xiyarta, wacce take gatantawa, ta mayar da ita bora, amma ta samo tsiya da talauci. Tatsuniyar na nuna mana muhimmancin yi wa yara tarbiyya ta qwarai, kamar kuma yadda take gargaxinmu da kada mu aikata mugunta a rayuwa.Tatsuniya ta shida mai suna Mai Haqar Vera, tana xauke ne da labarin wasu mafarauta, waxanda ke sana’ar farauta tare. Xaya daga cikinsu ya qi sauraren shawarar xaya, ya haqe wani rami, wanda ashe na kura ne, wacce daga qarshe ta halaka shi. Tatsuniyar na nuna mana illar taurin kai da rashin xaukar shawara da nasiha ta qwarai. Tatsuniyar Wata Mata Da Aljani ita ce ta bakwai a cikin wannan littafi. Tana ba da labarin wata mata ce da ta yi wa mijinta qarya, ta tsinto jariri a daji ta ce ita ta haife shi; inda daga qarshe suka gano ashe aljani ne ta tsinto kuma ya yi ta gallabarsu. Tatsuniyar na nuna mana illar qarya da ha’inci.Tatsuniya ta takwas ita ce, Musare Da Hodanego, wacce kuma ke nuna mana muhimmancin kyakkyawar tarbiyya da amfanin tausayi da jinqai tsakanin al’umma. Tatsuniya ta tara kuma ta qarshe da ke cikin littafin nan ita ce ta Marayu Biyu. Tana ba da labarin wasu marayu ne wa da qanwa, waxanda suka rasa iyayensu, amma suka ci gaba da zama cikin kulawar juna. Tana koya mana muhimmancin yin gaskiya da kuma bin gaskiya a kowane lokaci, kamar kuma yadda take gargaxi ga masu aikata munafunci.Babu shakka, littafin ya tsaru kuma marubucinsa ya zuba labarinsa cikin gwaninta da jan hankali; musamman kuma an qayata littafin da hotunan zane-zane masu qara armashi ga tatsuniyoyin.Ko me ya ja hankalin Dokta Bukar Usman har ya rubuta wannan littafi? Daga shafi na ix zuwa na xii, marubucin ya yi bayani dalla-dalla na dalilan da suka sanya ya yi wannan qoqari, inda yake cewa:“Nakan tuno a lokacin da nake qarami, a kullum da dare bayan ni da sauran yara mun ci abinci, mahaifiyata kan yi mana tatsuniya a cikin harshen Babur/Bura a can garinmu Biu, na qasar Borno.Idan da rani ne, mukan zauna a tsakar gida, wanda aka kewaye da zana. Wani lokacin kuma ga farin wata ya haske gari garau, kamar mutum ya tsinci allura a qasa; sararin sama kuma cike da taurari birjik, manya da qanana. Idan kuma da damina ne, sai mu zauna a cikin duhu a tsakar gidan, ko kuma a cikin xakin da aka hura wuta, musamman idan ana ruwa.Tatsuniyoyin masu qayatarwa ne qwarai, kuma na ji daxinsu a lokacin. Waxansu tatsuniyoyin na ban tsoro ne, wasu kuwa akwai ban mamaki. Sai dai dukkaninsu suna buxe mana idanu da qara mana ilimin zaman duniya da dabarun zama da mutane.Bayan haka, a lokacin da na fara karatun boko a wajen shekarar 1952, na karanta wasu littattafan Hausa kamar su Ka Koyi Karatu da Ruwan Bagaja da Magana Jari Ce da sauransu masu yawa, musamman waxanda shahararren marubucin nan, Alhaji Abubakar Imam ya rubuta. Kai bayan ma na yi murabus daga aikin Gwamnatin Tarayya a shekarar 1999, na ci gaba da karanta wasu littattafai da yawa da aka wallafa da Turanci, kamar na uwargidan Janar Domkat Bali, watau Esther Bali, wanda ya qunshi tatsuniyoyin mutanen Tarok da suke zaune a Jihar Filato da kuma waxanda wasu’yan Najeriya irinsu Shaihun malamin jami’a, Chinua Achebe da Cif Cyprian Ekwensi da Elechi Amadi suka rubuta. Bugu da qari, na karanta littattafai da yawa na shahararrun marubuta Turawa kamar su Chaucer da Shakespare da Jane Austin da Coleridge da Yeats. Duk waxannan littattafai sun sa na yi dogon tunani qwarai kan cewa ya kamata ni ma in rubuta littafin tatsuniyoyi da wasu labarai daga qasar Biu, watau mahaifata.A wannan zamani, mutane da yawa sun san wasu littattafai da Turawa suka wallafa domin yaransu, kamar Tom and Jerry da Chalk Zone da Jimmy Newton da Mew Mew Power, waxanda har yaranmu ma sukan karanta su a namu makarantun, ko kuma su riqa kallonsu a talabijin ko ta faya-fayen bidiyo. Wannan ya nuna cewa akwai wajibci da buqata ga ‘yan qasa su tashi tsaye su rubuta littattafai waxanda suka qunshi labarai irin namu, domin qara wa yaranmu ilimin da ya dace da qasarsu da yanayinta da xabi’un mutanenta, watau da misalan irin abubuwan da ke kewaye da mazauninsu.Wani abin lura shi ne, ko labaran na ‘yan Adam ne ko na aljanu ko na dabbobi, ko ma dai na wace irin halitta ne, suna nuni ne da halayya ta gari ko mummuna. Bugu da qari, akan ba da irin waxannan labarai ne domin a xebe kewa, kuma a koyar da darussan rayuwa masu amfani, kamar dai yadda na bayyana tun da farko. Don haka irin waxannan labarai suna da gindin zama a cikin adabi.A cikin ‘yan shekaru da suka shige ne na waiwayi waxannan tatsuniyoyi. Na je Biu musamman na yi bincike domin in samo mutanen da suka san irin waxannan tatsuniyoyi na da. Na yi haka ne domin ganin yadda yawancin yaran yanzu kan fara karatun boko tun suna ‘yan shekara uku a duniya, kuma idan sun koma gidajensu sai wasu su shiga kallon fina-finan bidiyo da talabijin, ko su sa waqoqin Makosa na mutanen qasar Kwango.To, ina fata waxannan tatsuniyoyi za su rage haka, domin tun tuni gajerun labarai da tatsuniyoyi kan hana yara fita yawon banza kuma su zaunar da dattijai a gida cikin iyali.A lokacin da nake bincike a kan tatsuniyoyin nan, na tuntuvi mutane da dama a qasar Biu, ciki har da wani da ya yi karatun boko har ya gama jami’a, amma ya ce bai tava jin ko xaya daga cikinsu ba. Wannan abu ya ba ni mamaki da qarfin gwiwar tattara tatsuniyoyin nan a cikin littafi, da fatan yara da manya za su amfana da su.Wani abin lura kuma shi ne, manyanmu, watau tsofaffi, waxanda suka iya ba da waxannan tatsuniyoyi ba su da yawa kamar da, kuma sai raguwa suke ta yi. Sai na lura idan ba an rubuta waxannan tatsuniyoyi na adabin baka ba, ba shakka za su vace nan da ‘yan shekaru kaxan masu zuwa. Allah Ya kiyaye faruwar haka, amin.Duk da cewa akasarin tatsuniyoyin waxanda na ji ne a qasar Biu, na kawo su ne a cikin harshen Hausa saboda mutane da yawa su sami damar karanta su, kuma su kwatanta su da waxanda suka sani. Kowa ya san cewa yanzu Hausa ta zama harshen mutane daban-daban a Najeriya, har ma a qasashen waje. Shi ya sa ma na fara kowace tatsuniya da: Ga ta nan, ga ta nanku maimakon in fara da: Suk suku, watau yadda ake fara tatsuniya da harshen Babur/Bura, inda masu saurare kan amsa da: Sunta, watau an gayyace ka ka ba da labarin, kamar dai Ta zo mu ji ta a cikin harshen Hausa.Ina fata jama’a za su samu qaruwa da wannan gudunmawa tawa.”Babu shakka wannan gudunmawa ta tabbata babban kavaki ga al’ummar yanzu da ma masu zuwa nan gaba. A yayin nazarin littafin nan, na ci karo da wasu ‘yan kura-kurai, waxanda ya kamata a bugu na gaba a yi qoqarin gyara su. Kaxan daga cikinsu sun haxa da: A shafi na iv, an rubuta bashi maimakon ba shi. A shafi na v, an rubuta Haqan maimakon Haqar. A shafi na vii, an rubuta dukan su maimakon dukkansu. Shafi na ix, an rubuta shaharraren maimakon shahararren. Shafi na x, an rubuta jihar Pilatu maimakon Jihar Filato, sai kuma aka rubuta fayafayan maimakon faya-fayen. A shafi na xi kuwa, an rubuta ‘yan adam maimakon ‘yan Adam, sai kuma aka rubuta darusan maimakon darussan, a gaba kuma aka rubuta finafinan maimakon fina-finan. A shafi na xii, an rubuta Nigeria maimakon Najeriya.Sauran kura-kuran sun haxa da: A shafi na xiv, an yi amfani da mawallafin maimakon marubucin. Shafi na xv an rubuta ko da yake maimakon kodayake, a gaba kuma aka rubuta gwamaya maimakon gwamutsa. Duk dai a wannan shafin, an rubuta maqwafin maimakon makwafin. Sai kuma shafi na xvii, inda aka rubuta yakamata maimakon ya kamata. A shafi na 6, an rubuta jifan maimakon jifar, sandana maimakon sandata. A shafi na 7, aka rubuta Yakan maimakon Takan. A shafi na 12, an rubuta xiban maimakon xibar. Shafi na 19, an rubuta bukatu maimakon buqatu. Haka kuma, a shafi na 39, an rubuta jimlar qwai da qwaiqwayemaimakon qwayaye. A shafi na 43, an rubuta kaiwa maimakon kai wa. Sai kuma shafi na 44, inda aka rubuta farautansa maimakon farautarsa. A shafi na 56 kuwa an rubuta hanunta maimakon hannunta. Sai kuma a shafi na 63 da aka rubuta tacinye maimakon ta cinye. Duk da cewa waxannan kura-kurai sun bayyana, amma ba su gurvata ma’anonin da ake nufi ba kuma ba su taka kara sun karya ba.Babu shakka littafin nan zai zama abokin hira ga yara da manya, kamar kuma yadda zai koyar da darussa masu yawa. Ina fata al’umma za su mallaki littafin nan, domin kuwa taska ce babba, abin adanawa. Haka kuma, ina kira ga makarantu da cibiyoyin ilimi da su tanadi littafin nan, domin kuwa zai fa’idantar.
Sharhi da nazari kan littafin Tsurondi (Da Wasu Labarai) Daga Bashir Yahuza Malumfashi
Sunan Littafi: Jarumin sarki (Da Wasu Labarai). Marubuci: Bukar Usman. Mawallafa: Gidan Dabino Publishers, Kano. Shekarar Wallafa: 2005. Yawan Shafuka: 61. Farashi: Ba a faxa ba. Babu ko shakka, al’ummar Hausawa na da daxaxxar al’adar nan ta koyar da ilimi da adana tarihi ta hanyar tatsuniya. Kamar yadda tarihi ya nuna, tun can zamanin zamunna, tsofaffi kan tara yara da dare, inda suke ba su gajerun labaru da sunan tatsuniya, inda ta wannan hanya suke ilimantarwa tare da nishaxantar da su. Haka kuma, duk dai ta hanyar tatsuniyar, al’umma kan bunqasa harshensu da tarihinsu. A wannan zamanin, lokacin da aka samu bayyanar hanyoyin ilimantarwa da shaqatarwa na zamani, kamar rediyo da talabijin, har ma da injinan bidiyo da sauransu, tuni al’umma suka yi watsi da tatsuniya a matsayin hanyar dogara, don samun irin wannan fa’ida. Sai dai barin tatsuniya da al’ummar Hausawa suka yi a matsayin muhimmiyar hanyar nishaxantarwa da ilimantarwa, ba qaramin sakaci ba ne, musamman saboda muhimmancinta. Domin dawo da martabar adabin Hausa, musamman ta fuskar tatsuniya, Malam Bukar Usman ya rubuta littattafai guda shida, inda ya kalato tsofaffin tatsuniyoyi, ya zuba su a ciki. Littafin Jarumin Sarki (Da Wasu Labara)i, wanda muke wa sharhi a wannan makon, xaya ne daga cikin jerin littattafan guda shida, waxanda ya sanya wa suna Taskar Tatsuniyoyi. Shi dai wannan littafi, an rubuta shi cikin harshe mai sauqi, an inganta shi da kyawawan zanannun hotuna masu fassara qunshiyar tatsuniyoyin da ke ciki. An yi xab’in littafin cikin inganci, wanda ya yi daidai da kowane littafi irinsa da za ka iya samu a duk faxin duniya. Marubucin littafin ya zavi kyawawan tatsuniyoyi guda goma, masu xauke da mabambantan darussa, sannan ya karkasa su zuwa babi-babi. A babi na xaya, wanda ya faro daga shafi na 5 kuma ya qare a shafi na 7, shi ke xauke da babbar tatsuniyar da aka sanya wa littafin suna, watau Jarumin Sarki. Sarkin dai ya kasance shahararren mayaqi, wanda ke auren mata huxu, ciki har da wacce duk jikinta kitse ne. A cikin wannan tatsuniya, an ba da labarin yadda sauran matansa suka haxa giri, suka sanya matarsa Takitse girki, wanda haka ya sanya zafin wuta ya narkar da ita. A babi na biyu kuwa, wanda ya faro daga shafi na 9 zuwa na 14, tatsuniyar kurege da kura (na xaya) ne. Irin yadda wannan abokantaka tsakanin waxannan mabambantan dabbobi ta kasance, ita aka warware cikin hikima da fasaha. Babu shakka akwai darasi mai kaifafa tunani a cikin wannan tatsuniya. Haka kuma, a babi na uku, irin wannan tatsuniya ce dai da ta shafi wata dangantakar kuma tsakanin kuregen da kuma kura. Sauran tatsuniyoyin da ke cikin littafin, daga babi na huxu zuwa na goma, watau daga shafi na 21 zuwa na 60 sun haxa da: Kishiyoyi Biyu, Cilakowa Da Kodokodo, Wata Mata Mai ‘Ya’ya Biyu, Qawancen Kyanwa Da Vera, Gizo Da Matarsa Qoqi, Zomo Da Damo da kuma tatsuniya ta qarshe, Cin Kasuwar Sama. Daga yadda aka rubuta tatsuniyoyin nan cikin tsanaki da kula, za su koya darussa masu yawa ga al’umma, musamman ma yaran makaranta. Yadda aka yi amfani da sunayen wasu dabbobi da tsuntsaye, babu shakka an adana kalmomin Hausa kuma an sanar da yara sunayen dabbobi da tsuntsayen da ba su sani ba, musamman ma yaran da suka tashi a birni, ba kasafai suke iya saninsu ba, amma ta hanyar wannan littafi, yara za su iya sanin kurege, kura, cilakowa, kodokodo, zomo da kuma damo. Kaxan daga darussan da za a iya koyo daga waxannan tatsuniyoyi sun haxa da illar karya alqawari, muhimmancin soyayya da illar gaba, illar wauta da abubuwan da take haifarwa. Haka kuma wasu daga tatsuniyoyin na nuna darussan illar kwaxayi da illar son zuciya da son kai. Sauran darussan sun haxa da mummunan sakamakon da munafuki kan fuskanta, illar hassada da kuma muhimmancin haquri da ribar da mai haquri kan samu a kowane lokaci. Duk da cewa an xauki lokaci wajen tsara wannan littafi cikin tsanaki, ta yadda aka kauce wa bayyanar kura-kurai da yawa, akwai kaxan daga wasu kura-kurai da suka bayyana a littafin, amma dai ba masu yawa ba ne, wasu ma tuntuven alqalami ne. Za mu kawo su nan ne kawai domin a samu damar gyarawa a bugu na gaba. Waxannan kura-kurai sun haxa da: A shafi na farko, an kira kamfanin wallafa na Gidan Dabino da Kamfanin Xab’i kuma a qasa aka ce Printed by Acadamy Press Plc, Lagos. A nan kamata ya yi a kira kamfanin a matsayin Kamfanin Wallafa (Publishers)ba na xab’i (Printers) ba. A shafi na iv, an rubuta kalmar kyaunmaimakon kyawun. A shafi na vii, an rubuta dukan su maimakon dukkansu. A dai wannan shafi, an rubuta wanda sukamaimakon waxanda suka. A shafi na x, an rubuta jihar Pilatumaimakon Jihar Filato. A dai kuma wannan shafi, an rubuta faya fayan maimakon faya-fayen. Sai kuma shafi na xi, inda aka rubuta darusan maimakon darussan. A dai wannan shafi, an rubuta finafinan maimakon fina-finan. A shafi na xii, an rubuta Nigeria maimakon Nijeriya. A shafi na xv kuwa, waxannan kura-kuran suka bayyana, inda aka rubuta ko da yake maimakon kodayake; sannan aka rubuta gwamaya maimakon gwamutsa. Haka ma a shafi na xvi, an rubuta yakamata maimakon ya kamata. A shafi na biyar, an rubuta amaryarsa kitse ne maimakon kitse ce. A shafi na 9, wajen rubuta jam’in riga sai aka ce rigaguna maimakon riguna. A shafi na 12, an kira kura da sunan durungu maimakon burungu. A shafi na 29, an rubuta fukafukai maimakon fuka-fukai. Sai shafi na 39, inda aka rubuta yaron ku wa maimakon yaron kuwa. A shafi na 44, an zana hoton magidanta biyu, mace da namiji a matsayin Gizo da Qoqi. Ya kamata a ce an zana su kamar yadda aka tava zana Gizo da siffar Gizo-gizo a littafin tatsiniyoyi na Ibrahim Yaro Yahaya. Wannan zai qara tabbatar da cewa Gizo ba mutum ba ne, duk kuwa da cewa yana wakiltar rayuwar mutane ne. A shafi na 46, an rubuta sunguminsa maimakon sangwaminsa, sansanya maimakon sassanya, ‘ya’yan shi maimakon ‘ya’yansa. A shafi na 47, an rubuta mutm-mutumin maimakon mutum-mutumin. Sai kuma shafi na 57, inda aka rubuta kuwamaimakon kuwwa. Idan muka yi la’akari da ingancin aikin littafin nan, da kuma muhimmancin abin da yake qunshe cikinsa da kuma yadda aka samu qarancin kura-kurai, babu shakka ya zama dole a yaba wa marubucinsa da kuma kamfanin da ya yi aikin wallafarsa. Littafin nan babbar taska ce, wacce ya kamata makarantu da cibiyoyin ilimi da iyayen yara su saya, domin amfanin al’umma gaba xaya. “Rubutun tatsuniya abu ne mai wuyar gaske, wataqila shi ya sa babu wadatattun littattafan tatsuniyoyi a cikin harshen Hausa. Amma idan ana samun masu yin hovvasa irin su Dokta Bukar Usman, za a cike wannan givi. Lallai wannan Taskar Tatsuniyoyi nasa, babban abin yabawa ne, wanda zai taimaka wa masu sha’awar karatun tatsuniyoyi.” Inji shugaban kamfanin wallafa na Gidan Dabino, Ado Ahmad. Dan Agwai Da Kura(Darussa 11 daga littafin)Tare da Bashir MalumfashiKamar yadda aka sani, tatsuniya na daya daga cikin hanyoyin koya ilimi, musaman ga yara a kasar Hausa. Wannan dalili ne ya sanya tastuniya ta zama wani jigo mai zaman kansa a cikin Adabin Hausawa, wanda a wannan zamani na ci gaba, aka samu adana tatsuniyoyin cikin littattafai.Littafin Dan Agwai Da Kura, daya ne daga cikin littattafai na Tatsuniyoyi da marubuci, Dokta Bukar Usman ya gudanar da nazari kuma ya rubuta. Kamfanin wallafa na Gidan Dabino, Kano ne ya wallafa littafin, wanda ke dauke da mabambantan tastuniyoyi guda goma sha daya cur.Wani abin ban sha’awa da burgewa kuma babban abin jan hankali shi ne, marubucin littafin nan ba yaro ba ne, ta fannin shekaru ko mukami, haka kuma shi ba Bahaushe ba ne, amma kamar yadda ya taba shaida wa wakilinmu, kishin harshen ne ya sanya ya maida hankali, ya yi nazari, ya tattara irin tastuniyoyin da ke akwai, ya rubuta wadannan littattafai. Ta fannin ilimi kuwa, marubucin ya mallaki shaidar karatu ta Digirgir (Phd), kamar kuma yadda ta fannin aiki ya kai mukamin Babban Sakatare a Gwamnatin Taraya, kafin ya ritaya.Kamar yadda bayani ya gabata, littafin Dan Agwai Da Kura na Dokta Bukar Usman, dan kabilar Babur daga Biu, na dauke da darussa masu yawa, da suka shafi zamantakewar al’umma. A yau, za mu zakulo kadan daga irin wadannan darusa, domin su kaifafa mana tunani, sannan kuma su taya mu hira.Darasi na daya, wanda za mu nazarta daga babi na daya na littafin, ya fito ne a tatsuniyar Dan Agwai Da Kura, watau daga shafi na biyar zuwa na tara na littafin. A tatsuniyar mun gane cewa lallai kwadayi ma budin wahala, musamman yadda kwadayin kura ya kai ta ga cin bakar wuya a hannun Dan Agwai. Haka kuma wannan na nuna mana cewa, duk yadda azzalumi ya kai da zaluncinsa, to wata rana zai gamu da wanda ya fi shi, watau kamar abin nan da ake cewa, abin da ka shuka shi zaka girba, ko kuma mu ce gaba da gabanta. Haka kuma, za mu iya gane cewa, dabara, a wasu lokata ta fi mai karfi tasiri. Gaskiyar wannan ta fito fili ne, idan muka duba yadda ta kwaranye tsakanin kura da Dan Agwai, domin kuwa kamar yadda ya nuna ya fi kura karfi nesa ba kusa ba, amma da ta nemi shawarar wani mai dabara, ta kuma aiwatar da dabarar, sai gashi ta samu galaba a kansa. Har kullum dai abin da ya kamata mutum ya lizimta shi ne, ya kasance mai gaskiya kuma ya guji kwadayi domin kuwa kwadayi, mabudin wahala ne.Darasi na gaba da za mu nazarta daga wannan littafi, ya fito ne a babi na biyu watau a tatsuniyar Dan Tsintuwa, daga shafi na goma sha daya zuwa na goma sha hudu. Babban darasin shi dai shi ne, zafin nema ba ya kawo samu. Yana nuna mana cewa duk matsayin da Allah Ya aje mutum, to ya hakura da shi kada ya ce zai wuce makadi da rawa wajen cimma wani buri nasa. Wannan darasi ya bayyana karara ga wata mata da Allah Ya jaraba da rashin haihuwa, amma ta yi ta fadi tashi don ganin ta mallaki yaro. Daga karshe ta tsinto wani hatsababin yaro, wanda ashe aljani ne shi ba mutum ba; wanda daga karshe ya yi ta wahalar da ita da mijinta. Wannan darasi zai iya amfani ga al’ummarmu musamman yadda a wannan zamanin mutane ke yin amfani da karkatattun hanyoyi don su mallaki dukiya, wanda daga karshe ta zama sanadiyyar halakar su, har ma su saka al’umma cikin bala’i. Ya kamata dai mu kasance masu hakuri da kaddarar da Allah Ya zaba mana.A babi na uku ne za mu nazarci darasi na gaba, a tatsuniyar Ya Tsinci Dami A Kala. Babban darasin kuwa shi ne, mu kasance masu aikata alheri komai kankantarsa, domin Hausawa sun ce danko ne, ba ya faduwa kasa banza. Kamar dai yadda wani yaro ya samu babban alheri a sakamakon wani alheri da ya aikata. Haka kuma a dai wannan tatsuniya, mun koyi darasin da ke nuna mana cewa mugunta fitsarin fako ce takan koma ga wanda ya shirya ta, musamman yadda wani sarki ya tashi halaka wannan yaro, amma daga karshe sai shi da iyalinsa suka halaka, ba yaron ba.A babi na hudu kuwa, a tatsuniyar Cin Amanar Dan uwa, mun karu da darasin da ke nuna illar cin amana. Mun haka a tatsuniyar, inda wani yaro ya ci amanar dan uwansa, amma bai kare lafiya ba. Hadama da handama dai ba su haddasa komai sai kaskanci da wulakanci.A babi na biyar kuwa, a tatsuniyar Dogarawa Uku, mun gane cewa kuskure ne ga shugaba ko alkali ya zartar da hukunci ba tare da ya gudanar da kwakkwaran bincike ba kamar dai yadda wani sarki ya zartar da hukunci ga Gidado, duk da cewa ba shi ya aikata laifin da aka tuhume shi da aikatawa ba. Mu rika kyautata zato ga kawunanmu, sannan mu rika yin bincike kafin zarta da hukunci.A babi na shida kuwa, a tatsuniyar Abotar Biri Da Kifi, mun koyi darasin da ke cewa, mu rike amanar da aka damka mana, domin cin amana bai haifar da abin kirki. Haka kuma hassada ba ta da kyau, domin idan aka yi wa mai rabo hassada, taki take zama.Darasi na bakwai, wanda za mu nazarta ya fito ne a babi na bakwai, a tatsuniyar Muwa Muwa. Darasin dai na nuna wa iyaye cewa, ba daidai ba ne kuma bai kamata su rika nuna bambanci ga `ya`yansu ba, domin ba a san wanda zai kasance nagari mai taimako ba. Lallai kam wannan babban darasi ne, musaman ga wasu iayayenmu na wannan zamani, da ke nuna kauna ga wasu `ya`yansu, alhali suna musguna wa sauran, kamar ba su suka haife su ba.Babi na takwas, wanda ke dauke da tatsuniyar Samarin Barayi Uku, na koya mana darasin illar cin amana, domin duk wanda ya ci amana, sai ta ci shi.A tatsuniyar Auta Da Dodanniya, a babi na tara, nan za mu gamu da darasin da ke koya mana muhimmancin yin alheri da kuma aikata abin da ya kamata. Yana nuna mana muhimmancin zaman tare na taimakekeniyar juna, kamar kuma yadda yake nuna mana cewa, komai ya yi tsanani, sauki zai biyo baya. Haka kuma yana nuna mana muhinmmancin karbar bako cikin mutunci da daraja, wanda haka kan haifar da alheri ga bakon da kuma mai masaukinsa.A babi na na goma ne za mu hadu da darasinmu na goma, a tatsuniyar Kuda Mai Kwadayi, inda wani kuda saboda bakin kwadayinsa ya bi kwaryar zuma, kansa ya karye ya mutu. Wannan na nuna mana illar kwadayi, wanda ke janyo wahala da halaka ga mai yinsa.Darasinmu na goma sha daya, wanda ya fito a babi na goma sha daya na littafin a tatsuniyar Barayin Albagadi na nuna mana muhimmnacin ladabi da biyyaya kamar kuma yadda yake nuna mana muhimmanci taimakon mabukata a rayuwa. Wadannan darusa sun fito fili ga attajiri mai suna Albagadadi, wanda ke taimakon al’umma da dukiyarsa, yadda barayin da suka shiga gidansa don yi masa sata suka halaka ba tare da sun samu nasarar taba dukiyarsa ba. Lallai kam, duk mai taimakon al’umma da dukiyarsa Allah zai kare shi daga asara da bala’i.Wadannan darusa guda goma sha daya da suka fito a littafin tatsuniya na Dan Agwai Da Kura, abin nazarta ne, kuma abin karanta ne ga yara da manya, musamman domin dibar darusa da kuma nishadi. Ya kamata gwamnatoci su tanadar da shi ga makarantunsu, don amfanin dalibai. Al’umma kuma, ya kamata su yi kokarin mallakarsa domin amfanin kansu.
Tatsuniyar Yarima Da Labbi A Sabon Littafi Daga Bashir Yahuza Malumfashi
Sunan Littafi: Yarima Da Labbi (Da Wasu Labarai).Marubuci: Bukar Usman.Mawallafa: Gidan Dabino Publishers, Kano.Shekarar Wallafa: 2005.Yawan Shafuka: 59.Farashi: Ba a faxa ba.A yayin da muke yin sharhi ga littafi na uku da ke cikin jerin littattafai guda shida na Taskar Tatsuniyoyi, wanda marubuci mai kishin ilimi, Dokta Bukar Usman ya rubuta, ba za mu gaji da nanata cewa, tatsuniya babbar taska ce ta ilimantarwa da nishaxantarwa ba; domin kuwa har zuwa yau xin nan, tana xaya daga cikin jigogin adana adabin Hausa a cikin al’umma.Kamar littafi na xaya da na biyu da muka nazarta a makonni biyu da suka gabata, shi ma wannan mai suna Yarima Da Labbi (Da Wasu Labarai), yana xauke ne da daxaxan tatsuniyoyi har guda goma, waxanda aka karkasa cikin babi goma. Haka kuma, an zayyana littafin tare da kyawawan hotunan zane-zane, wanda haka ya qara inganta tsarin littafin. An yi amfani da ingantattar Hausa kuma mai sauqin fahimta ga mai karatu, musamman ma qananan yara da su ne ke buqatar mafi yawa daga darussan tatsuniyoyin da ke ciki.Kamar yadda aka faxi cewa tatsuniyoyi goma ne ke cikin littafin nan, waxannan kuwa sun haxa da tatsuniyar Yarima Da Labi, Kura Da Kurege (Na Xaya), Gizo Da Sarki, Kurege Da Wayo da tatsuniyar Xan Auta Da ‘Yar Gwaggo. Sauran tatsuniyoyin su ne: Kura da Kurege (Na Biyu), ‘Yar Sarkin Da Ta Saci Xinya, Rimi Da ‘Yar Amana, Gizo Da Damon Sarki da kuma tatsuniya ta goma, TaliPaku Da Kurciya.Kaxan daga darussan da ke qunshe cikin wannan littafin sun haxa da muhimmanci da tasirin gaskiya da riqon amana, illolin qarya da cin amana, amfanin jaruntaka da rashin tsoro da dai sauransu. Haka kuma, wannan littafi zai taimaka sosai wajen adana adabin Hausa, kamar kuma yadda zai zama gayauna wajen koya kalmomin Hausa ga yara masu tasowa da ma waxanda suka taso amma ba su samu damar zama a karkara ba, wanda haka ya sanya ba su san wasu al’adun gargajiya na Hausa ba.Wani muhimmin ta’aliqi da Malam Salisu Saleh Na’inna ya rubuta wa littafin nan daga shafi na xiii zuwa na xvii, ya qara fito da muhimmanci da tasirin tatsuniya a cikin al’umma, kamar kuma yadda ya fayyace tarihinta da samuwarta a duniya baki xaya. Muhimmancin wannan ta’aliqi ya sanya muka ga ya dace mu tsakuro shi a nan kamar haka:“Akwai shaida mai qarfi da ke nuna cewa an jima da fara harhaxa tatsuniyoyi shigen waxanda wannan littafi ya qunsa a cikin harshen Hausa, domin amfanin masu karantawa da kuma tsare irin waxannan labarai na adabin baka daga vacewa.Tarihin tatsuniyoyi a duniya baki xaya, kamar yadda wani masanin tatsuniyoyi da gajerun labarai, Gerda Charles ya nuna a cikin littafi mai suna Great Short Stories of the World (London, 1976), tun da can mutanen qasar Masar sun yi nisa wajen tsara tatsuniyoyi. Masana sun amince cewa, mutanen Masar sun yi amfani da irin takardar rubutun nan da aka san su da ita, watau papyrus da duwatsu wajen yin zane-zane waxanda ke nuna qwarewarsu wajen tsara tatsuniyoyi game da halayen mutane a wancan zamani, tun kusan shekara 1,300 kafin bayyanar Annabi Isa (AS).Bayan Misirawa sai Girkawa suka qago littafin nan mai suna Aesop’s Fables, wanda ya qunshi labarun da suka yi kama qwarai da na mutanen Hindu. Daman dai su mutanen Hindu sun rubuta nasu tatsuniyoyin ne a cikin tsohon harshensu mai suna Sanskrit. Haka kuma tarihi ya nuna cewa mutanen Parisa ko Pasha sun yi dogon sharhi ko ‘yan qere-qere a kan tatsuniyoyin Hindu xin.Daga nan kuma sai Larabawa suka fassara waxancan tatsuniyoyi suka canja wasu abubuwa da ke cikinsu, kuma suka qara nasu a ciki. Yin hakan ya sa labarun sun koma kamar ma Larabawan ne suka qirqiro su tun da farko. Sun tara labarun ko tatsuniyoyin a cikin littafin nan mai suna Dare Dubu Da Xaya.Mutanen Ingila kuma sun tashi harhaxa tatsuniyoyi da ‘yan gajerun labaru a wajen qarshen qarni na 19. A lokacin ne mawallafin nan xan Ingila mai suna Charles Dickens ya buga littafinsa mai suna Pickwick Papers. Mutanen qasar Jamus ma sun taka muhimmiyar rawa wajen shirya qananan labarai masu qayatarwa. Mutanen Faransa da Italiya, watau Romawa da Jafanawa da mutanen qasar Rasha ma sun yi suna qwarai wajen tsara gajerun labaru da tatsuniyoyi a cikin harsunansu.A qasar Amurka kuma, wani Bature mai suna Charles Colcock Jones Jnrya fitar da wani littafin tatsuniyoyi mai suna Gullah Folkstales from the Georgia Coast a harshen Gullah, watau Turancin baqar fatar Amurka wanda ya yi kama qwarai da Broken English, a cikin shekarar 1888. A cikin sharhin da masaniya Susan Millar Williams ta yi wa littafin, ta ce tatsuniyoyin irin na baqar fata ‘yan asalin nahiyar Afrika da aka kai aikin bauta a yankunan bakin teku da ke Jihar Georgia da maqwaftanta a gabashin qasar Amurka ne. Ta ce duk alamu sun nuna cewa wannan littafi shi ne littafin tatsuniyoyi na farko da ta sani a Amurka. Tatsuniyoyin sun qunshi dodanni da dila da zomo da kurege da zaki da damisa da veraye da giwaye da dai sauran dabbobin da akan samu a nahiyar Amurka ko yankunan bakin tekun gabashin Amurka xin.”Kaxan ke nan daga tsokacin da Malam Salisu Na’inna ya yi a cikin wannan littafi, wanda haka ke nuna cewa ba qasar Hausa ce kaxai ke da tatsuniyoyi ba, kamar kuma yadda haka ke nuna mana cewa sauran nahiyoyi ma na adana nasu tatsuniyoyin, don haka me zai hana mu ma mu adana namu? Don haka nake kira ga al’umma da su mallaki littafin nan, sannan kuma gwamnatocin jihohi su tanadar da shi ga makarantunsu gaba xaya domin yaxa ilimi da adana adabin gargajiya.
Nazari Da Sharhin Littafin Jarumin Sarki Daga Bashir Yahuza Malumfashi Sunan Littafi: Jarumin sarki (Da Wasu Labarai). Marubuci: Bukar Usman. Mawallafa: Gidan Dabino Publishers, Kano. Shekarar Wallafa: 2005. Yawan Shafuka: 61. Farashi: Ba a faxa ba. Babu ko shakka, al’ummar Hausawa na da daxaxxar al’adar nan ta koyar da ilimi da adana tarihi ta hanyar tatsuniya. Kamar yadda tarihi ya nuna, tun can zamanin zamunna, tsofaffi kan tara yara da dare, inda suke ba su gajerun labaru da sunan tatsuniya, inda ta wannan hanya suke ilimantarwa tare da nishaxantar da su. Haka kuma, duk dai ta hanyar tatsuniyar, al’umma kan bunqasa harshensu da tarihinsu.A wannan zamanin, lokacin da aka samu bayyanar hanyoyin ilimantarwa da shaqatarwa na zamani, kamar rediyo da talabijin, har ma da injinan bidiyo da sauransu, tuni al’umma suka yi watsi da tatsuniya a matsayin hanyar dogara, don samun irin wannan fa’ida. Sai dai barin tatsuniya da al’ummar Hausawa suka yi a matsayin muhimmiyar hanyar nishaxantarwa da ilimantarwa, ba qaramin sakaci ba ne, musamman saboda muhimmancinta.Domin dawo da martabar adabin Hausa, musamman ta fuskar tatsuniya, Malam Bukar Usman ya rubuta littattafai guda shida, inda ya kalato tsofaffin tatsuniyoyi, ya zuba su a ciki. Littafin Jarumin Sarki (Da Wasu Labara)i, wanda muke wa sharhi a wannan makon, xaya ne daga cikin jerin littattafan guda shida, waxanda ya sanya wa suna Taskar Tatsuniyoyi.Shi dai wannan littafi, an rubuta shi cikin harshe mai sauqi, an inganta shi da kyawawan zanannun hotuna masu fassara qunshiyar tatsuniyoyin da ke ciki. An yi xab’in littafin cikin inganci, wanda ya yi daidai da kowane littafi irinsa da za ka iya samu a duk faxin duniya.Marubucin littafin ya zavi kyawawan tatsuniyoyi guda goma, masu xauke da mabambantan darussa, sannan ya karkasa su zuwa babi-babi. A babi na xaya, wanda ya faro daga shafi na 5 kuma ya qare a shafi na 7, shi ke xauke da babbar tatsuniyar da aka sanya wa littafin suna, watau Jarumin Sarki. Sarkin dai ya kasance shahararren mayaqi, wanda ke auren mata huxu, ciki har da wacce duk jikinta kitse ne. A cikin wannan tatsuniya, an ba da labarin yadda sauran matansa suka haxa giri, suka sanya matarsa Takitse girki, wanda haka ya sanya zafin wuta ya narkar da ita.A babi na biyu kuwa, wanda ya faro daga shafi na 9 zuwa na 14, tatsuniyar kurege da kura (na xaya) ne. Irin yadda wannan abokantaka tsakanin waxannan mabambantan dabbobi ta kasance, ita aka warware cikin hikima da fasaha. Babu shakka akwai darasi mai kaifafa tunani a cikin wannan tatsuniya. Haka kuma, a babi na uku, irin wannan tatsuniya ce dai da ta shafi wata dangantakar kuma tsakanin kuregen da kuma kura.Sauran tatsuniyoyin da ke cikin littafin, daga babi na huxu zuwa na goma, watau daga shafi na 21 zuwa na 60 sun haxa da: Kishiyoyi Biyu, Cilakowa Da Kodokodo, Wata Mata Mai ‘Ya’ya Biyu, Qawancen Kyanwa Da Vera, Gizo Da Matarsa Qoqi, Zomo Da Damo da kuma tatsuniya ta qarshe, Cin Kasuwar Sama.Daga yadda aka rubuta tatsuniyoyin nan cikin tsanaki da kula, za su koya darussa masu yawa ga al’umma, musamman ma yaran makaranta. Yadda aka yi amfani da sunayen wasu dabbobi da tsuntsaye, babu shakka an adana kalmomin Hausa kuma an sanar da yara sunayen dabbobi da tsuntsayen da ba su sani ba, musamman ma yaran da suka tashi a birni, ba kasafai suke iya saninsu ba, amma ta hanyar wannan littafi, yara za su iya sanin kurege, kura, cilakowa, kodokodo, zomo da kuma damo.Kaxan daga darussan da za a iya koyo daga waxannan tatsuniyoyi sun haxa da illar karya alqawari, muhimmancin soyayya da illar gaba, illar wauta da abubuwan da take haifarwa. Haka kuma wasu daga tatsuniyoyin na nuna darussan illar kwaxayi da illar son zuciya da son kai. Sauran darussan sun haxa da mummunan sakamakon da munafuki kan fuskanta, illar hassada da kuma muhimmancin haquri da ribar da mai haquri kan samu a kowane lokaci.Duk da cewa an xauki lokaci wajen tsara wannan littafi cikin tsanaki, ta yadda aka kauce wa bayyanar kura-kurai da yawa, akwai kaxan daga wasu kura-kurai da suka bayyana a littafin, amma dai ba masu yawa ba ne, wasu ma tuntuven alqalami ne. Za mu kawo su nan ne kawai domin a samu damar gyarawa a bugu na gaba.Waxannan kura-kurai sun haxa da: A shafi na farko, an kira kamfanin wallafa na Gidan Dabino da Kamfanin Xab’i kuma a qasa aka ce Printed by Acadamy Press Plc, Lagos. A nan kamata ya yi a kira kamfanin a matsayin Kamfanin Wallafa (Publishers)ba na xab’i (Printers) ba. A shafi na iv, an rubuta kalmar kyaunmaimakon kyawun. A shafi na vii, an rubuta dukan su maimakon dukkansu. A dai wannan shafi, an rubuta wanda sukamaimakon waxanda suka. A shafi na x, an rubuta jihar Pilatumaimakon Jihar Filato. A dai kuma wannan shafi, an rubuta faya fayan maimakon faya-fayen. Sai kuma shafi na xi, inda aka rubuta darusan maimakon darussan. A dai wannan shafi, an rubuta finafinan maimakon fina-finan. A shafi na xii, an rubuta Nigeria maimakon Nijeriya.A shafi na xv kuwa, waxannan kura-kuran suka bayyana, inda aka rubuta ko da yake maimakon kodayake; sannan aka rubuta gwamaya maimakon gwamutsa. Haka ma a shafi na xvi, an rubuta yakamata maimakon ya kamata. A shafi na biyar, an rubuta amaryarsa kitse ne maimakon kitse ce. A shafi na 9, wajen rubuta jam’in riga sai aka ce rigaguna maimakon riguna. A shafi na 12, an kira kura da sunan durungu maimakon burungu.A shafi na 29, an rubuta fukafukai maimakon fuka-fukai. Sai shafi na 39, inda aka rubuta yaron ku wa maimakon yaron kuwa. A shafi na 44, an zana hoton magidanta biyu, mace da namiji a matsayin Gizo da Qoqi. Ya kamata a ce an zana su kamar yadda aka tava zana Gizo da siffar Gizo-gizo a littafin tatsiniyoyi na Ibrahim Yaro Yahaya. Wannan zai qara tabbatar da cewa Gizo ba mutum ba ne, duk kuwa da cewa yana wakiltar rayuwar mutane ne.A shafi na 46, anrubuta sunguminsa maimakon sangwaminsa, sansanya maimakon sassanya, ‘ya’yan shi maimakon ‘ya’yansa. A shafi na 47, an rubuta mutm-mutumin maimakon mutum-mutumin. Sai kuma shafi na 57, inda aka rubuta kuwamaimakon kuwwa.Idan muka yi la’akari da ingancin aikin littafin nan, da kuma muhimmancin abin da yake qunshe cikinsa da kuma yadda aka samu qarancin kura-kurai, babu shakka ya zama dole a yaba wa marubucinsa da kuma kamfanin da ya yi aikin wallafarsa. Littafin nan babbar taska ce, wacce ya kamata makarantu da cibiyoyin ilimi da iyayen yara su saya, domin amfanin al’umma gaba xaya.“Rubutun tatsuniya abu ne mai wuyar gaske, wataqila shi ya sa babu wadatattun littattafan tatsuniyoyi a cikin harshen Hausa. Amma idan ana samun masu yin hovvasa irin su Dokta Bukar Usman, za a cike wannan givi. Lallai wannan Taskar Tatsuniyoyi nasa, babban abin yabawa ne, wanda zai taimaka wa masu sha’awar karatun tatsuniyoyi.” Inji shugaban kamfanin wallafa na Gidan Dabino, Ado Ahmad.
Gwaidayara (Darusa 9 daga littafin tatsuniyar) AMINIYA, Juma’a 23 ga Oktoba, 2009, Fasaha 37 Littafi Gwaidayara (Da wasu Labarai) na daya daga jerin littattafai goma sha hudu da ke cikin tsarin Taskar Tatsuniyoyi da marubuci Dokta Bukar Usman ya rubuta, kamfanin Gidan Dabino Publishers ya wallafa. Littafi ne da aka yi wa aikin dab’i mai inganci da ban sha’awa a ido, wanda kuma yake dauke da zane-zanen hotutna masu kyau. Littafin na dauke da babi-babi guda tara cur, kamar kuma yadda yake kunshe da ingantattun tatsuniyoyi har guda tara, kuma yana da shafuka 68 daidai.Kamar yadda kamfanin wallafa na Gidan Dabino ya ce: “Rubutun tatsuniya abu ne mai wuyar gaske. Watakila shi ya sa babu wadatattun littattafan tatsuniyoyi a cikin harshen Hausa. Amma idan ana samun masu yin hobbasa, irin su Dokta Bukar Usman, za a cike wannan gibi. Lallai wannan Taskar Tatsuniyoyi nasa, babban abin yabawa ne, wanda zai taimaka wa masu sha’awar karatun tatsuniyoyi.”Bisa gaskiyar wannan batu na sama, shi ya sanya za mu nazarci wannan littafi a yau, sannan mu zakulo wasu muhimman darussa daga littafin, domin amfanin al’umma gaba daya.Idan muka duba tatsuniya ta farko, watau Gwaidayara, wacce ta fito cikin littafin a babi na daya, za mu iya tsintar wadannan darussa; illar nuna bambanci tsakanin ‘ya’yan da mutum ya haifa, kamar dai yadda ta faru ga Gwaidayara, wacce mahaifinta ya nuna mata bambanci tsakanin ‘yan uwanta, ta yadda ya zaba musu sunaye masu kyau, amma ita ya sanya mata sunan Gwaidayara, amma da yake Allah ne ke badawa, sai gashi ita da aka wulakanta, ita ce ta samu daukaka, ta samu auren dan sarki, ta kasance tauraruwa a gidansu; ta sanadiyyar arzikin iyayen ta da ‘yan uwanta. Kada mu sake mu bambanta tsakanin ‘ya’yanmu, kowa da baiwar da Allah Ya hore masa.Darasi na biyu kuwa, za mu dauko shi ne a cikin tatsuniya ta biyu, watau tatsuniyar ‘Yar’auta Da Kogin Rantsuwa, Wannan kuwa shi ne, muhimmancin hukunta duk wanda ya yi ba daidai ba, wanda a sakamakon yin hukunci ne ake daidaita da saita halayen mutum da ya karkace daga hanya.Darasi na uku ya fito ne daga tatsuniyar Kurege Da Biri, watau a babi na uku na littafin. A nan ne muka fahimta da darasin da ke nuna mana cewa zamba da cin amana ba abin kwarai ne ba, domin kuwa duk mai yin su ba zai kai ga nasara ba, kan, yadda ta kasance da Kurege, wanda Biri ya yi ta zalunta da yaudara.Darasi na hudu mun tsinto shi ne ababi na hudu a tatsuniyar Kogi Mai Cinye Makaryata, inda muka koyi cewa, yin cikakken bincike yayin da za a yanke hukunci kan wani al’amari yana da tsananin muhimmanci, kuma yana haifar da ingantaccen sakamako.Darasi na biyar kuwa shi ne, duk wanda yake nuna tausayi da jinkai ga halittar Ubangiji, zai samu nasarar alamuransa ga rayuwa. Wannan darasi kuwa ya fito ne a babi na biyar, watau a tatsuniyar Sarki Gizo Da Kwarkwata.Darasinmu na shida ya fito ne a babi na shida, a tatsuniyar Talume, inda muka fahimci gaskiyar maganar nan da ke cewa, wanda bai ji bari ba ya ji hoho, watau dai mai kunnen kashi zai gamu da gamonsa a rayuwa.Sai kuma darasi na bakwai, wanda muka koya daga tatsuniyar Ladi Da Dodo, a babi na bakwai; wanda ke nuna mana cewa rashin bin maganar magabata na jefa mutum cikin hadari, kamar kuma yadda yake nuna mana muhimmancin zaman lafiya cikin jama’a, wanda haka ke haddasa taimako ga mutum da al’umma gaba daya.A babi na takwas kuwa, a tatsuniyar Darajar Neman Sani, mun gane cewa lallai ilimi shi ne gishirin zaman duniya, shi ne kuma tushen duk wani cigaban al’umma, wanda ke haddasa alherai daban-daban.Darasinmu na tara kuma na karshe a wannan littafi, wanda ya fito a babi na tara, a tatsuniyar Dan Buwaila Da Bangorinsa, yana nuna mana illar hassada da muhimmancin hakuri a rayuwa, kamar kuma yadda yake nuna mana muhimmancin tashi tsaye domin gwagwarmaya da neman nasarar rayuwa.Nazarin littafin nan da amfani da darussan da yake kunshe da su lallai zai taimaka wa al’umma. Za a iya amfani da littafin nan wajen koya wa yara darussan zaman rayuwa. Don haka, akwai bukatar makarantu da cibiyoyin ilimi su tanadar da shi ga dalibai a makarantu da dakunan karatu.
Littafin Marainiya Da Wasu Labarai A Mahangar Sharhi Daga Bashir Yahuza Malumfashi
Sunan Littafi: Marainiya Da Wasu Labarai.Marubuci: Bukar Usman.Mawallafa: Gidan Dabino Publishers, Kano.Shekarar Wallafa: 2005.Yawan Shafuka: 62.Farashi: Ba a faxa ba.Kowa ya san ma’anar tatsuniya, watau labari ne xauke da wasu halaye nagari da hanyoyin warware wasu matsaloli na rayuwa da kuma yin ishara game da wasu abubuwa da sukan faru ga masu aikata munanan halaye kamar mugunta da kwaxayi da wulaqanci ko zalunci ko kishi ko sata da cuta da sakarci da qarya; ko kuma ga masu aikata kyawawan halaye kamar aikata alheri da nuna mutunci da soyayya da ladabi da biyayya da riqe amana da sada zumunci da nuna tausayi da girmama na gaba da sauransu.”Wannan bayani na sama, shi ne xanxanon da aka lasa wa al’umma a bangon littafin da muke wa sharhi a yau. Kamar yadda sunan littafin ya nuna, an gina shi ne bisa gajerun labaru da a qasar Hausa muka fi sani da sunan tatsuniya. Duka-duka, littafin yana xauke ne da daxaxan tatsuniyoyi guda goma, waxanda suka bambanta da juna, kuma suke xauke da darussa daban-daban.Daga kallon litttafin nan, mutum zai san cewa da gaske aka yi wajen tsara shi, domin kuwa an yi masa xab’i mai inganci. Bangon littafin dai mai inganci ne ne, wanda aka xanxashe shi da zanen hoto mai xaukar hankali kuma mai kala. Takardar da aka yi amfani da ita a ciki kuwa, fara ce tas mai inganci, sannan kuma an qayata shafukan cikinsa da zanen hotuna masu kyau da qara bayyana qunshiyar tatsuniyoyin. Haka kuma, an yi amfani da haruffa masu girma, wanda haka ya sanya mai karatu zai samu sauqin karanta labarun dalla-dalla.Kamar yadda masu iya magana suka ce, hannu xaya ba ya xaukar jinka, marubucin littafin nan ya nuna haka, inda ya bayyana sunayen wasu muhimman mutane da suka kama masa har ya samu kammala wannan littafi, wanda ya ta’allaqa bisa zuzzurfan bincike. Waxannan mutane kuwa sun haxa har da mai martaba Sarkin Biu, Mai Umar Musxafa da Farfesa Xandatti Abdulqadir da Farfesa Bello Sa’id da Farfesa Xangambo Abdulqadir da Farfesa Sa’idu Ahmad Vavura da Editan jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo, Malam Tukur Abdulrahman da sauransu. Shi kuwa Malam Salisu Na’inna Xambatta, ta’aliqi ya rubuta a shafi na xiii zuwa xvii na littafin, inda ya yi nazari, ya bayyana tarihin tatsuniya da muhimmancinta ga al’umma.Kamar yadda aka bayyana cewa tatsuniyoyi guda goma ne a cikin wannan littafi, waxanda marubucin ya karkasa su cikin babi-babi, bari mu xauke su xaya bayan xaya, domin mu ga abubuwan da suka qunsa da kuma kaxan daga darussan da suke koyarwa ga al’umma.Babi na xaya na xauke ne da wata tatsuniya mai taken Marainiya. Tatsuniyar na ba da labarin wata yarinya ce da iyayenta suka rasu, suka bar ta cikin ‘yan uba maza da mata da kuma kishiyar uwa, waxanda suka taru suka riqa musguna mata. Da yake Allah shi ke da ikon azurta wanda Ya so, sai wannan yarinya ta samu xan sarkin garin yana son ta sosai, wanda daga qarshe dai ya aure ta kuma suka zauna cikin jin daxi da qaunar juna. Marainiya ta wahala qwarai kamin ta samu auren xan sarki.Babban darasin da ke cikin wannan tatsuniya shi ne, rabonka idan ya rantse, komai runtsi da matsatsai sai ka same shi, komai rauninka da rashin gatanka kuwa, kamar dai yadda Marainiya ta kasance.Babi na biyu kuwa na xauke da wata tatsuniya da ke ba da labarin wani sarki da matansa da ba su haihuwa, sai daga bisani ya auri mai haihuwa, wacce kishiyoyin suka yi ta yi wa qulle-qulle amma daga qarshe dai gaskiya ta bayyana, sarki ya gane. Babban darasin da ke cikin tatsuniyar shi ne, mugun hali da mugun nufi ba su da kyau, domin mafi yawan lokaci, qaiqayi kan koma kan masheqiya.Labarin kura da zomanya kuwa na cikin babi na uku ne, inda zomanya kan ci amanar kura, inda daga qarshe asirinta yake tonuwa, kuma ta shiga cikin kunya da qasqanci. Babban darasin labarin shi ne, cin amana dai ba kyau, domin qarshen maci amana dai jin kunya, kamar yadda wannan tatsuniya ta nuna.Babi na huxu kuwa na xauke da labarin kurege da kura, sai kuma babi na biyar da ke xauke da labarin wata budurwa marar rabo; a yayin da kuma babi na shida ke xauke da labarin wata yarinya kyakkyawa da wanta. Dukkan waxannan tatsuniyoyi, suna xauke da al’ajabi da tausayi da ban dariya a wasu wuraren. Kaxan daga cikin darussan da ke cikinsu sun haxa da illar ruwan ido da illar kwaxayi, wanda aka ce shi ne mabuxin wahala.Babi na bakwai na xauke da labarin wata mace mai ciki, kuma babban jigon tatsuniyar shi ne, muhimmancin cika alqawari idan har an qulla shi. Sai babi na takwas da ke xauke da tasuniyar wani dagaci da malaminsa. Babi na tara kuwa, wani labari ne ke cikinsa, na wata budurwa mai neman ganyen miya. Akwai tausayi da al’ajabi ckin wannan labari, wanda ke xauke da darussa kamar haka: Illar rowa, wacce ke haifar da tsiya, sannan kuma aka nuna muhimmancin kyauta ko alheri, wanda aka ce danqo ne, ba ya faxuwa qasa banza.A babi na goma kuwa, labarin wasu ‘yan mata ne masu kamun kifi, inda xaya daga cikinsu ke samun baiwa da xaukaka, sanadiyyar alheri da jinqai da ta nuna ga wata tsohuwa, wacce daga bisani ta gane cewa ashe aljana ce. Muhmmancin alheri da kuma illolin qarya duk sun bayyana a cikin wannan tatsuniya ta ‘yan mata masu kamun kifi.Babu shakka, littafin nan ya tsaru sosai kamar yadda aka yi bayani a baya. Wannan ne ma ya sanya mutum zai ga cewa an yi amfani da ingantattar kuma amsassar Hausa wajen tsara labarun, wanda haka ya sanya aka kauce wa samun kura-kurai da yawa a ciki. Sai dai duk da haka, akwai kaxan da aka samu na wasu ‘yan kura-kurai, waxanda kuma ba su taka kara suka karya ba, musamman ganin cewa ba lallai ne ma mai karatu ya gano lungun da suka vuya ba.Misali, a shafi na xi, an rubuta finafinai maimakon fina-finai. A shafi na xii, an rubuta Nigeria maimakon Najeriya. A shafi na xv, an rubuta ko da yake maimakon kodayake. A shafi na 6, an rubuta la’asar maimakon La’asar. Sai shafi na 7, inda aka rubuta gurunta maimakon wurinta. Haka kuma, a shafi na 29, an rubuta rawan ido maimakon ruwan ido. A shafi na 44, an rubuta koreta maimakon kore ta. Sai a shafi na 54, inda aka rubuta bata maimakon ba ta, kamar kuma yadda a shafi na 56 aka rubuta aureta maimakon aure ta.Idan aka yi la’akari da qarancin kura-kuran da suka bayyana a littafin, ya zama dole a yaba wa marubucinsa da kuma kamfanin da ya yi wallafarsa, musamman ta yadda suka tsara shi. Muna ba da shawarar da a yi qoqarin gyara kura-kuran a bugu na gaba, yadda littafin zai qara inganci sosai.“Duk wanda ya yi sa’ar samun wannan littafi na Taskar Tatsuniyoyi, ba shakka ya sami abokin hira, kuma rumbun hikima da basira, da zai zama mai amfani wajen xebe kewa ga yara da manya.” Inji Malam Salisu Na’inna Xambatta, a qarshen ta’aliqinsa. |
||